Gwamna Buni ya bayar da umurnin raba wa tsangayoyi 475 kayan abinci da tufafi a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

A ƙoƙarin sa na inganta rayuwar al’ummar jihar, Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya bai wa hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, umurnin raba wa makarantun tsangaya 475, wanda ake sa ran alarammomi da almajiransu 8,000 za su ci gajiyar tallafin kayan abinci da na masarufi haɗi da dilolin tufafin sakawa, barguna, tabarmin leda, bokitan ruwa da sauran su a faɗin jihar Yobe.

Da take ƙaddamar da rabon tallafin a Tsangayar Slaramma Goni Yahaya dake unguwar Gwange a Damaturu, Sakataren Hukumar SEMA, Dr. Muhammad Goje, wanda Daraktan hukumar, Alhaji Hassan Bomai ya wakilta a wajen taron inda aka bayar da tattafin kayyayakin ga tsangayoyi 12, daga cikin adadin tsangayoyi 30 waɗanda za a bai wa tallafin da ke ciki da wajen birnin, da yammacin ranar Talata.

Ya ce: “Gwamnatin Jihar Yobe ta ɗauki wannan matakin tallafa wa makarantun da kayan abinci, kayan masarufi tare da tufafin sakawa, bisa la’akari da ta yi na buƙatar yin hakan, sannan da muhimmancin da suke da shi wajen koyar da ilimin addinin Musulunci. Sannan kuma ta lura da halin da suke ciki na buƙatar irin wannan tallafin a daidai wannan lokacin.”

Shugaban Hukumar SEMA ya ƙara da cewa, wannan shi ne karon farko wanda gwamnati ta aiwatar da makamancin wannan shiri domin makarantun tsangaya kaɗai a faɗin Jihar Yobe. Ya ce, “wannan ya nuna Gwamna Buni ya ɗauki karatun tsangayoyi da muhimmanci tare da ba su kulawa ta musamman domin kyautata wa mallamanmu na tsangaya bisa gudunmawar da suke bayarwa.”

Bugu da ƙari, kowace tsangaya ta samu tallafin buhunan shinkafa 2, buhunan masara 3, magi katan 1, bargo 10, bokiti 5, dillolin gwanjo 2, tabarmar leda 10, da makamantan su. Ya ƙara da cewa, ganin halin da ake ciki wanda aka fuskanci ibtila’in ambaliyar ruwan sama kana da matsalar tsaron da jihar ta sha fama da shi, ya sanya dole gwamnati ta ɗauki matakin inganta rayuwar al’umma.

Shugaban Hukumar ya roƙi waɗanda suka ci gajiyar tallafin da cewa su yi amfani da kayan kamar yadda aka buƙata, su guji sayar da su ko karkatar da su zuwa inda ba nan ne maƙasudin aiwatar da su ba.

Haka kuma ya roqi alarammomin da su ci gaba da yi wa Jihar Yobe da ma Nijeriya addu’o’i na musamman domin samun dawwamamen zaman lafiya tare da samun nasarar babban zaɓen da aka sa a gaba a 2023.

A nashi ɓangaren, Shugaban ƙungiyar makarantun tsangaya ta Jihar Yobe, Goni Ibrahim ya bayyana cewa, ba za su iya misalta jin daɗi da farin cikin wannan tallafin da Gwamna Mai Mala Buni ya bai wa makarantun tsangayoyi a jihar ba.

Ya ce, “duk wanda ya kalli fuskokin alarammomi, makaranta Alƙur’ani Maigirma a jihar Yobe ya ga alamomin canjin da walwala, al’amarin da ya fara tun bayan hawan Gwamna Buni a karagar mulkin jihar Yobe. Ya taimakemu da dukan abubuwan da suka dace mu samu. Sannan kuma gwamnatinsa ta ɗauki ilimin addinin Musulunci tare da mu malaman tsangayoyi da muhimmanci.

“Saboda haka, muna ƙara jaddada godiya da yaba wa gwamnatin jihar Yobe a ƙarƙashin Hon. Mai Mala Buni, ya yi mana abubuwan alheri tare da girmamawa da mutuntamu fiye da kowane lokaci. Muna yi masa fatan alheri kuma za mu ci gaba da gudanar da addu’o’i domin samun dawwamamen zaman lafiya a jiharmu da ƙasa baki ɗaya,” inji Goni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *