12
Dec
DAGA MINA Abokai, gwamnatin kasar Sin ta taba gabatar da manufofin taimakawa al’ummar Xinjiang guda 9. Yau “duniya a zanen MINA” zai gabatar muku yadda Sin ta aiwatar da daya daga cikin wadannan manufofi, wato manufar taimakawa al’ummar Xinjiang wajen samun aikin yi, matakin da ya inganta zaman rayuwar al’ummar yankin. Matar dake cikin wannan zane sunanta Jimilanmu Makmuti, wadda ma’aikaciya ce a wata masana’antar samar da kayayyaki dake Xinjiang, ta ce: “na samu aiki mai kyau, zan samu zaman rayuwa mai kyau nan gaba”. A shekaru 4 da suka gabata, Jimilanmu Makmuti da iyalanta sun dogara ga dan albashin…
