Editor

9513 Posts
Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Sufeto Janar na ‘Yansanda, Usman Alƙali Baba

Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga Sufeto Janar na ‘Yansanda, Usman Alƙali Baba

Daga NAFI'U SALISU Kamar yadda yake a dokar ƙasa, dukkan wani jami’in tsaro aikinsa shi ne kare rayuka da dukiyar al’ummar ƙasa. Don haka ne ma kowanne ma’aikacin Ɗansanda sai ya yi rantsuwa da littafin addininsa a yayin kama aikinsa na bada tsaro, cewar ya rantse da kundin tsarin mulkin ƙasarsa zai yi aiki a bisa doka da oda, wajen ƙare rayuka da dukiyar al’umma. Babu wata al’umma da za ta rayu cikin aminci face sai da hukuma a cikinta, kasancewar hukuma a cikin al’umma kuma shi ne ginshiƙin tafiyar da rayuwa cikin tsari, ta hanyar bin doka da oda.…
Read More
Ƙasar Sin ta amsa sunanta na aminiya ta ƙwarai ga ƙasashen Afrika

Ƙasar Sin ta amsa sunanta na aminiya ta ƙwarai ga ƙasashen Afrika

Daga CMG HAUSA Har kullum kulawar kasar Sin ga aminanta na Afrika, ya kasance abun burgewa, da ya kamata manyan kasashe irinta su yi koyi da shi. Yadda ake maganar an bar kasashen Afrika a baya idan ana tattauna a dandamalin duniya, kamata ya yi a rika ganin tallafin wadannan manyan kasashe a nahiyar ta Afrika idan har da gaske suke. Ban da kasar Sin, ba ka jin wata kasa dake abubuwan na tallafi masu kwari na a zo a gani, wadanda kuma suka shafi jama’a kai tsaye. Hausawa kan ce ruwan da ya dake ka, shi ne ruwa. Tabbas…
Read More
Ƙasar Sin ta gudanar da bikin tunawa da Wadanda aka halaka a Birnin Nanjing

Ƙasar Sin ta gudanar da bikin tunawa da Wadanda aka halaka a Birnin Nanjing

Daga CMG HAUSA Al'ummar birnin Nanjing sun yi shiru na minti daya, an kuma karar jiniya a ko'ina cikin birnin, yayin da kasar Sin ke ci gaba da gudanar da bikin tunawa na kasa karo na 9 a yau Talata, domin nuna alhini ga mutane dubu 300 da aka kashe a kisan kiyashin Nanjing. Kisan kiyashin na Nanjing, ya faru ne a lokacin da sojojin Japan suka kwace iko da birnin a ranar 13 ga watan Disamban shekarar 1937. A cikin makonni shida, maharan na Japan sun kashe Sinawa fararen hula da sojoji dubu 300, da ba sa dauke da…
Read More
Manyan jami’an Sin da Amurka sun yi shawarwari a Lardin Hebei a ƙasar Sin

Manyan jami’an Sin da Amurka sun yi shawarwari a Lardin Hebei a ƙasar Sin

Daga CMG HAUSA Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana jiya Litinin cewa, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Xie Feng, ya yi shawarwari da mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin gabashin Asiya da tekun Pasifik Daniel Kritenbrink, da babbar darekta mai kula da harkokin kasar Sin a majalisar tsaron Amurka Laura Rosenberger, ranar 11 da 12 ga watan Disamba a lardin Hebei dake arewacin kasar Sin. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labarai na yau da kullum cewa, bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi,…
Read More
An kai wa jarumi Akeem Adeyemi hari a wurin ɗaukar fim

An kai wa jarumi Akeem Adeyemi hari a wurin ɗaukar fim

Daga AISHA ASAS Fitacciyar jaruma a masana’antar finafinai ta Kudu Wumi Toriola, ta bayyana labarin tsautsayin da ya afkawa abokin aikinta Akeem Adeyemi, a wani faifan bidiyo da ta fitar a shafinta na Istagram, wanda ke ɗauke da labarin yadda abin ya faru cikin murya da hotuna. An hasko jarumi Akeem, yana darzar kuka a faifan bidiyon, bayan da wasu tsageru suka kai masa hari a lokeshon, inda ya je da zumar ɗaukar wani shirin fim. Kamar yadda jarumar ta bayyana a a ƙarƙashin bidiyon, tsagerun sun hargitsa wurin ta hanyar mayar da muhallin mai cike da kwanciyar hankali da…
Read More
Kannywood da SAKA sun yi gangamin ranar cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV

Kannywood da SAKA sun yi gangamin ranar cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gidauniyar Kannywood da haxin gwiwa da hadaɗiyyar Ƙungiyar masu Shirya Finafinai ta Ƙasa, MOPPAN da hukumar da ke kula da cuta mai karya garjuwar jiki, wato SAKA, ta shirya gangami a kan ranar tunawa da cuta mai karya garkuwa ta HIV a ranar 1-12-2022. Gangami wanda ya fara da tattaki daga Ƙofar Nasarawa zuwa gidan Makama, inda daga nan aka garzaya ɗakin taro na Kannywood TV da ke unguwar Tudun Yola, Tun da farko a jawabinsa Dr. Ahmad Muhamad Sarari, wanda shi ne Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Shirya Finafinai ta ƙasa, ya bayyana cewa, sun shiga…
Read More
Me ke kawo taƙaddama tsakanin surukai a ƙasar Hausa?

Me ke kawo taƙaddama tsakanin surukai a ƙasar Hausa?

Daga AMINA YUSUF ALI Masu karatu sannu da jimirin karatun jaridarku mai farin jini, Blueprint Manhaja. A wannan mako muna tafe da bayanai a kan yadda alaqar tsakanin surukai take ƙara lalacewa a ƙasar Hausa har take zama ma kamar kishi ne tsakaninsu ba wai surukuta ba. Wannan abu ne mai matuar ban mamaki musamman idan muka yi la'akari da yadda alaƙar surukai take jiya a ƙasar Hausa. A zamanin da, ba komai sai kunya da tsakanin surukai a ƙasar Hausa. Kuma mafi yawan lokuta ma a gida guda suke zaune. Amma hakan bai sa ko da wasa suruka ta…
Read More
Halin da sakatariyar Kebbi ke ciki bayan shekaru 10 da fara aikinta kan biliyoyin Naira

Halin da sakatariyar Kebbi ke ciki bayan shekaru 10 da fara aikinta kan biliyoyin Naira

Daga AMINU AMANAWA a Kebbi “Na kan kashe kusan dukkanin albashina wajen tafiya aiki da samarwa kaina muhalli da abinci, saboda nisan wajen da nake aiki. Ka ga Ina ƙarƙashin Ma'aikatar Kasafi tana nan cikin Birnin Kebbi, amma sashen da nake na Bagudu tafiyar kilomita 160 zuwa 200, wanda ba zai yiwu na je aiki kullun na dawo ba, abinda ya sa albashin da nake karva ba ya isa ta ɗawainiyar tafiya kawai, da abinci da wurin zama dole sai  na ɗan haɗa da ɗan buge-buge, saboda ba muhalli, kuma maganar gaskiya indai mahalli ne ko manyan sakatarori ba su…
Read More
Ina da burin kawo canji a siyasar Filato ta Arewa – Hon. Sahlan

Ina da burin kawo canji a siyasar Filato ta Arewa – Hon. Sahlan

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU a Jos Shiyyar Filato ta Arewa daga Jihar Filato yanki ne da ya daɗe yana shan gwagwarmaya da rikita-rikitar siyasa, saboda kasancewar sa yanki mafi yawan jama'a da tarin albarkatun ƙasa, ƙabilu nabambanta, wanda kuma ya sha fuskantar hare-hare da rikice-rikice masu nasaba da siyasa, ƙabilanci da addini. Har wa yau kuma shi ne yanki mafi kusa da gwamnatin tsakiya mai hedikwata a Jos, Babban Birnin Jihar Filato.  Hon. Muhammad Shafi'u Yakubu Sahlan na daga cikin matasan 'yan siyasar da suka fito zawarcin kujerar Sanata da zai wakilci Shiyyar a Majalisar Ƙasa.  A zantawarsa da wakilin…
Read More
Bai kamata a siyasar da gasar fifa ta Qatar ta fakewa da batun kare hakkin bil Adama ba

Bai kamata a siyasar da gasar fifa ta Qatar ta fakewa da batun kare hakkin bil Adama ba

DAGA CMG HAUSA A wannan makon da muke ciki, za a gudanar da wasannin kusa da na karshe, na gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya dake gudana a Qatar. Da fatan kafofin yada labarai za su mai da hankali kan gasar ita kanta kadai. Qatar ita ce kasa ta farko cikin kasashen Larabawa da ta karbi bakuncin wannan kasaitacciyar gasa a duniya. Amma tun lokacin da ta fara neman iznin daukar bakuncin gasar, kasashen yamma suka rika takalar ta, suna cewa wai wasu ma’aikatan ginin filayen gasar fiye da dubu 10 sun mutu, da nufin zuga wutar da za…
Read More