13
Feb
Daga BASHIR ISAH Da alama dai wutar rikicin jam’iyyar APC a Kano na ci gaba da ruruwa musamman ma ganin yadda tsagin tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau, suka dake kan buƙatun da suka gabatar wa shugabancin jami’iyyar na ƙasa. A ranar 8 ga Fabrairu ne tsagin Sanata Ibrahim Shekarau ya rubuta wa babban ofishin APC na ƙasa wasiƙa yana mai nuna rashin jin daɗinsa kan cewa an ƙi sauraron buƙatun da ya gabatar wa ofishin. Haka nan, cikin wata wasiƙar da tsagin na Shekarau ya sake aike wa babban ofishin APC, mai ɗauke da kwanan wata 9 ga Fabrairu,…
