Editor

9513 Posts
Kotu ta tursasa wa kamfani cigaba da biyan albashi ga korarren ma’aikaci

Kotu ta tursasa wa kamfani cigaba da biyan albashi ga korarren ma’aikaci

Daga AMINA YUSUF ALI Wata kotun masana'antu reshen garin Fatakwal ta tursasa wa wasu kamfani mai suna, Hughes Limited da Baker Hughes Incorporated su cigaba da biyan ma'aikacinsu, Joshua Umoren albashi duk bayan sati biyu a tsahon shekaru domin biyan haƙƙoƙinsa.  Alƙalin kotun, Mai Shari'a Zainab ta yanke hukuncin a zaman kotun na ranar Juma'ar da ta gabata, bayan ta kammala sauraren shaidu daga ɓangarorin lauyoyin guda biyu. Wato na wanda ake ƙara, da na wanda yake ƙarar.  Alƙalin ta bayyana cewa, kamfanonin ba su karya doka ba don sun sallami Josua daga aiki ba. Amma sun karya dokar aiki…
Read More
Rashin tsaro ne ke kassara mu, inji matan FOMWAN a Bauchi

Rashin tsaro ne ke kassara mu, inji matan FOMWAN a Bauchi

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Ƙungiyar Mata Musulmi ta Nijeriya (FOMWAN) reshen jihar Bauchi ta bayyana damuwar ta dangane da matsalar rashin tsaro da yake addabar ɗaukacin mata a ƙasar nan, tana mai cewar, shekaru biyu da suka gabata, ƙalubalen ta kai ɗalibai mata bango a makarantun boko da na Islamiyya. Wannan ƙalubale, a cewar ƙungiyar, tana buƙatar gwamnatoci a dukkan matakan mulki, su bijiro da wasu tsare-tsare na ilmantar wa da zai bai wa miliyoyin yara damar samun ilimi ba tare da wani barazanar rashin tsaro ba. Shugabar ƙungiyar ta jihar Bauchi, Amirah A’ishatu Ibrahim Kilishi, ita ce…
Read More
Ilimi da aikin yi ne kadai za su kawar da matsalar tsaro -Yariman Bakura

Ilimi da aikin yi ne kadai za su kawar da matsalar tsaro -Yariman Bakura

Daga BASHIR ISAH Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ya bayyana cewar ingantaccen ilimi da samar da aikin yi ga matasan ƙasar nan ne kaɗai zai kawo ƙarshen matsalar tsaro da ake fama da ita. Sanata Yarima, ya bayyana haka ne a wajen taron goyon baya da Ƙungiyar Matasa Kiristoci ta Najeriya (YOWICAN), ta shirya a ranar Juma'a don mara masa baya kan ƙudurinsa na yin takarar shugaban kasa a 2023. "Dukkan matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar nan na da alaƙa da rashin samar da ingantaccen ilimi ga 'yan kasa. "Za mu samar da ilimi kyauta…
Read More
Ta’aziyya: Ina fatan za a yi wa Hanifa adalci, inji Aisha Buhari

Ta’aziyya: Ina fatan za a yi wa Hanifa adalci, inji Aisha Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai ɗakin shugaban Nijeriya, Aisha Buhari ta ziyarci Kano domin ta’aziyya ga iyalan Sheik Ahmad Bamba da kuma Hanifa Abubakar, yarinyar nan ‘yar shekara biyar da ake zargin mai makarantarsu ya kashe ta. A jawabin da ta gabatar a gidan gwamnatin jihar Kano ranar Laraba, Aisha Buhari ta ce ta je jihar ne a ziyarar ta kashin-kanta domin jajanta wa gwamnan Kano da matarsa, da Sarkin Kano da kuma al’ummar jihar a kan rasuwar Sheikh Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba da kuma Hanifa Abubakar. Game da kisan da aka yi wa Hanifa, matar shugaban ƙasar…
Read More
Jami’ar Bayero ta ƙaddamar da ƙamus ɗin Hausa zuwa Ingilishi a Kano

Jami’ar Bayero ta ƙaddamar da ƙamus ɗin Hausa zuwa Ingilishi a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  A ranar Asabar da ta gata an ƙaddamar da sabon qamus ɗin harshen Hausa zuwa Ingilishi da ya gudana a Jami’ar Bayero ta Kano. Littafin dai yana ɗauke da shafi 627, wanda Bature kuma masani a ɓangaren harsuna da ke Jihar Indiana ta Amurka, Paul Newman da mai ɗakinsa, Roxana Ma Newman suka wallafa, kuma maɗaba’ar Jami'ar Bayero ta buga shi. Newman dai ya tava zama a  Kano ne tun a  shekarar 1972, inda ya  zama Darakta na farko a Cibiyar Koyar da Harsunan Nijeriya a BUK, lokacin tana Kwalejin Abdullahi Bayero. Da ya ke…
Read More
‘Yan binga 20 sun baƙunci lahira bayan da suka yi yunƙurin shiga NDA

‘Yan binga 20 sun baƙunci lahira bayan da suka yi yunƙurin shiga NDA

Daga BASHIR ISAH Sama da 'yan bindiga ashirin ne suka baƙunci lahira sakamakon artabun da suka yi da sojojin saman Nijeriya na rundunar 'Thunder Strike' a daidai lokacin da suka doshi makarantar bai wa sojoji horo, NDA a taƙaice ke Kaduna. Sahihan majiyoyi sun shaida wa jaridar PRNigeria cewa, an ga 'yan bindigar a ranar Alhamis da ta gabata a kan babura sama da guda 50 inda suka doshi NDA da ke Kaduna. Idan za a iya tunawa, 'yan bindigar sun samu nasarar kai hari cikin NDA a watan Yunin bara tare da sace wani babban soja kana suka bindige…
Read More
Zhao Lijian: Taron sassa 4 wani yunƙuri ne na daƙile ƙasar Sin

Zhao Lijian: Taron sassa 4 wani yunƙuri ne na daƙile ƙasar Sin

Daga CRI HAUSA Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya ce taron da manyan jami’an ƙasashen Amurka da Japan, da Australia da Indiya suka shirya gudanarwa, wani salo ne na yunƙurin daƙile ƙasar Sin. Zhao wanda ya bayyana hakan a Juma’ar nan, yayin taron manema labarai da ya gudana, ya ce sassan 4 na da burin amfani da taron na su, domin tattauna abun da suka kira “ƙaruwar tasirin Sin”. Jami’in ya ƙara da cewa, wannan salo ne da Amurka ke bi domin wanzar da danniya, kuma hakan zai harzuƙa wasu sassa, tare da haifar da fito na…
Read More
CMG ya samar da kyamara mai saurin ɗaukar hotunan bidiyo domin gasar wasannin Olympics ta Beijing

CMG ya samar da kyamara mai saurin ɗaukar hotunan bidiyo domin gasar wasannin Olympics ta Beijing

Daga CRI HAUSA Babban gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin na CMG ya ƙera wata kyamara mai ƙarkon gaske, bisa fasahar “Ultra HD 4K” domin amfani da ita wajen ɗaukar hotunan bidiyo masu nagarta. Kyamarar dai na iya zarta gudun ‘yan wasan dake tsere a dandamalin ƙanƙara, yayin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing dake gudana yanzu haka. An kafa kyamarar a cikin zauren tseren ƙanƙara na babban filin wasan hunturu dake birnin Beijing, inda kyamarar da aka yi wa laƙabi da "Cheetah," kan yi gudun mitoci 25 ko wace daƙiƙa, wato kwatankwacin gudun kilomita 90 ko…
Read More
Gasar Amurka, gasa ce cikin lumana ko yunƙurin hana bunƙasuwar sauran ƙasashe?

Gasar Amurka, gasa ce cikin lumana ko yunƙurin hana bunƙasuwar sauran ƙasashe?

Daga CRI HAUSA Kwanan baya, majalisar dokokin ƙasar Amurka ta zartas da Dokar Gasa ta Amurka ta Shekarar 2022, domin tabbatar da matsayin ƙasar na kan gaba a fannonin masanaantu, ƙirƙire-ƙirƙire, da ƙarfin tattalin arziki. Amma, cikin wannan doka, ƙasar Amurka ta yi suka kan manufofin ƙasar Sin wajen neman ci gaba, da wasu harkokinta na cikin gida. Haƙiƙa dai, nufinta shi ne hana ci gaban ƙasar Sin bisa hujjar yin gasa. Shi ya sa, ake ganin cewa, wannan dokar da ƙasar Amurka ta fidda, doka ce ta hana ci gaban sauran ƙasashe. Ƙasar Amurka tana da yancin neman bunƙasuwa,…
Read More
Laifin Gwamnatin Tarayya ne idan muka sake tsunduma yajin aiki – ASUU

Laifin Gwamnatin Tarayya ne idan muka sake tsunduma yajin aiki – ASUU

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) Reshen Jihar Legas ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su tunkari Gwamnatin Tarayya gar-da-gar a kan matsalar da ke damun jami’o’in gwamnati, waɗanda su ke tilasta tafiya yajin aiki. ASUU ta ce, ƙungiyar ta na tafiya yajin aiki ne sai bayan ta yi iyakar dukkan ƙoƙarin sasantawa, amma abin ya faskara. Idan ba a manta ba, ASUU ta nemi mambobin ta su ware rana ɗaya domin wayar wa ‘yan Nijeriya kai cewa su na ja-in-ja da gwamnati ne domin su ceto jami’o’in ƙasar nan daga durƙushewa. ASUU ta ce…
Read More