Editor

9513 Posts
Rasuwar Garba Aliyu Zariya ta girgiza duniyar ’yan jarida

Rasuwar Garba Aliyu Zariya ta girgiza duniyar ’yan jarida

Daga DAUDA USMAN a Legas A ranar Asabar ɗin ƙarshen makon jiya ne, Allah ya karɓi rayuwar fitaccen ɗan jarida, Alhaji Garba Aliyu Zariya.  Wannan bawan Allah ya rasu ne da da misalin ƙarfe 12:00 na dare a gidansa da ke unguwar Agege ta Jihar Legas.  Tuni dai aka rigaya aka yi jana'izarsa, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, tare da fatan Allah ya jiƙan sa, ya kuma gafarta masa da rahama. Shi dai Marigayi Alhaji Garba Aliyu Zariya an haife shi a ranar 8 ga Janairu, 1969, wato shekaru 63 kenan da suka gabata. Garba Zariya ya rasu ya…
Read More
Abinda ya sa Shoprite ya rufe reshensa na Legas

Abinda ya sa Shoprite ya rufe reshensa na Legas

Daga AMINA YUSUF ALI Kamfanin rukunin shagunan sayayya na Shoprite ya rufe reshensa na unguwar Maryland da yake a jihar Legas.  Haka kuma rahotanni sun sake bayyana cewa, kamfanin ya sanar da cewa, nan ba da daɗewa ba zai buɗe sababbin rassansa a garuruwan Kaduna, Fatakwal, Binin, da kuma Jos a ƙoƙarinsa na ganin ya bunƙasa kasuwancinsa. Shi dai kamfanin 'The Retail Supermarket Nigeria Limited (RSNL)' wanda shi ne mamallakin rukunin shaguna na Shoprite, ya ba da sanarwar rufe reshen nasa na Maryland a Ikejan jihar Legas  a ranar 31 ga watan Janairun shekarar 2022 da muke ciki.  Ciyaman ɗin…
Read More
Matuƙin adaidaita ya halaka ɗan yuniyal kan Naira 20 a Keffi

Matuƙin adaidaita ya halaka ɗan yuniyal kan Naira 20 a Keffi

Daga BASHIR ISAH A ranar Juma'a ta makon jiya wani matuƙin adaidaita-sahu ya yi ajalin wani jami’in yuniyal na NURTW mai suna Abba da ke aiki a tashar motar da ke kusa da NTA, hanyar Abuja a Keffi, jihar Nasarawa. Matuƙin keken ya halaka Abba ne ta hanyar daɓa masa wuƙa har sau biyu biyo bayan jayayyar da ta shiga tsakaninsu a kan rashin biyan kuɗin sallamar da ‘yan yuniyal suka saba karɓa daga hannun duk wani mai abin hawan da suka ba shi fasinja a tasharsu. Da yake yi wa wakilinmu ƙarin haske kan yadda lamarin ya auku, Aƙilu…
Read More
Allah ya jiƙan Rayan Awram

Allah ya jiƙan Rayan Awram

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA A yayin da har yanzu ake cigaba da juyayin rasa yarinya ’yar shekara 5 da haihuwa da malamin makarantarsu, Abdulmalik Tanko ya yi wa kisan gilla a Kano, sai ga wani juyayin na rasa yaro Rayan Awram mai shekaru 5 shi ma a Maroko. Abin da ya bambanta rashin yaran biyu shi ne, yayin da na Hanifa cin amanar da malmanin makaranta ya yi ne bayan sacewa da neman kuɗin fansa ya kuma kashe ’yar yarinya wai don kar asirinsa ya tonu; mutuwar Rayan kuma sanadiyyar hatsarin da ya rutsa da shi ne lokacin da ya…
Read More
Mun ɗauki ’yan sanda 40,000 aiki cikin shekaru huɗu – Gwamnatin Tarayya

Mun ɗauki ’yan sanda 40,000 aiki cikin shekaru huɗu – Gwamnatin Tarayya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, ta ɗauki ’yan sanda sama da 40,000 aiki a cikin shekaru huɗu da suka gabata domin magance matsalar rashin tsaro a ƙasar. Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ta bakin ministan harkokin ’yan sanda, Dokta Maigari Dingyadi, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a garin Uyo na jihar Akwa Ibom, a wani taro da aka yi wa manyan jami’an ’yan sanda mai taken ‘Sabon hangen ’yan sanda, hanyar gyara tsaron ƙasa’. Shugaban ya sanar da cewa, a ƙoƙarinsa na ƙara kwarin gwiwar jami’ai da kuma samar da ingantacciyar hidima ga…
Read More
Rikicin Bagudu da Aliero: Zaɓen ƙananan hukumomin Kebbi ya zamo ’yar manuniya

Rikicin Bagudu da Aliero: Zaɓen ƙananan hukumomin Kebbi ya zamo ’yar manuniya

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Ranar Asabar 5 ga watan Fabrairun 2022 da ta gabata ne aka gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Kebbi, sai dai zaɓen ya zama kamar ma'auni ne na farin jinin jam'iyyar APC mai mulki ko kuma na ɓangaren gwamnan jihar Sanata Atiku Bagudu. Sai dai zaɓen ya bar baya da qura bayan bayyanar wata takarda mai ɗauke da sa hannun shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kebbi Honarabul Aliyu Muhammed Mera, inda ta ke bayanin cewa an yi wa jam'iyyu goma sha takwas rajistar shiga zaɓen amma dai sha bakwai ne suka…
Read More
Sana’a: Babbar hanyar samun ingantacciyar rayuwa

Sana’a: Babbar hanyar samun ingantacciyar rayuwa

A wannan makon, Blueprint Manhaja za za ta jawo hankalin matasanmu maza da mata ne game da muhimmancin yin sana’a kowace iri ce, in dai ba ta sava wa doka ba, ko ta saɓa ƙa’idojin da gwamnati ta kafa. Mun taɓa yin bayani makamancin wannan a watannin baya, saboda muhimmancinsa ne ya sa muka ga ya kamata mu ɗan sake waiwayarsa. Sana’a ga duk magidanci, ko wani mai neman ya zama yana neman na kansa, ta zama wajibi bisa la’akari da halin da ake ciki a duniyarmu ta yau. Domin ba za a iya cewa gwamnati za ta iya sama…
Read More
Sin na adawa da ra’ayin Ministan Harkokin Wajen Lithuania game da ƙasar Sin

Sin na adawa da ra’ayin Ministan Harkokin Wajen Lithuania game da ƙasar Sin

Daga CRI HAUSA Rahotanni na cewa, yayin da ministan harkokin wajen ƙasar Lithuania ke ziyara a ƙasar Australia, ya yi kira ga dukkan duniya da su yi adawa da ayyukan keta haƙƙin ɗan Adam da Sin da Rasha suke aikatawa. Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya yi nuni a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, ya kamata ƙasar Lithuania ta rungumi gaskiya, ta gyara kuskurenta, ta komawa manufar “ƙasar Sin ɗaya tak a duniya”, kuma ta dakatar da matakai marasa dacewa, da haɗa kan sauran ƙasashe, wajen adawa da ƙasar…
Read More
Gasar Olympic ta lokacin sanyi: Dandali mai kyau na fahimtar Ƙasar Sin

Gasar Olympic ta lokacin sanyi: Dandali mai kyau na fahimtar Ƙasar Sin

Daga AMINA XU ”Mai kuzari, mai ban sha’awa, mai ƙwazo, mai hikima, abokiya mai muhimmanci ta fuskar ciniki..” Yadda babban editan shafin yanar gizo na kafar yaɗa labarai ta T-Online ta ƙasar Jamus Florian Harms, ya bayyana Sin da jama’arta a bayaninsa ke nan. A bayanin da ya rubuta, ba ma kawai ya jinjina wa gasar Olympic ta lokacin sanyi da ake yi a birnin Beijing ba, har ma ya yi kira ga jama’ar ƙasar Jamus da su ƙara fahimtar ƙasar Sin ta hanyar da ta dace. Lalle Florian Harms ya gano hanyar da ta dace don fahimtar ƙasar Sin.…
Read More
Da ruwan ciki akan ja na rijiya

Da ruwan ciki akan ja na rijiya

Daga SAMINU ALHASSAN Sanin kowa ne cewa, duk wani ci gaba da duk wata ƙasa za ta samu, yana yin tasiri ne idan ƙasar ta iya cimma nasarar wanzar da rayuwar alummun ta, musamman ta fannin samar da abinci da tsaro, kafin duk wani mataki na inganta rayuwar alumma. A baya-bayan nan, ɗaya daga muhimman batutuwa dake jan hankulan masharhanta, shi ne yadda yankin kahon Afirka ke fuskantar kamfar abinci, sakamakon fari mai tsanani dake addabar yankin wanda ya haifar da ƙarancin yabanya a gonaki, da kuma farin ɗango da suka addabi yankin a wasu lokuta. A cewar shirin samar…
Read More