Gasar Olympic ta lokacin sanyi: Dandali mai kyau na fahimtar Ƙasar Sin

Daga AMINA XU

”Mai kuzari, mai ban sha’awa, mai ƙwazo, mai hikima, abokiya mai muhimmanci ta fuskar ciniki..” Yadda babban editan shafin yanar gizo na kafar yaɗa labarai ta T-Online ta ƙasar Jamus Florian Harms, ya bayyana Sin da jama’arta a bayaninsa ke nan.

A bayanin da ya rubuta, ba ma kawai ya jinjina wa gasar Olympic ta lokacin sanyi da ake yi a birnin Beijing ba, har ma ya yi kira ga jama’ar ƙasar Jamus da su ƙara fahimtar ƙasar Sin ta hanyar da ta dace.

Lalle Florian Harms ya gano hanyar da ta dace don fahimtar ƙasar Sin. Haƙiƙa, za a iya fahimtar matsayin da Sin take ɗauka kan abubuwan duniya ta hanyar aikin shirya da gudanar da wannan gaggarumar gasar da ra’ayin da masu halartar gasar suke bayyanawa ta shafukan sada zumunta.

Domin cika alƙawarin da take yi, Sin ta yi amfani da ƙarfinta wajen shirya wannan gasa, inda ta yi amfani da kimiyya da fasaha wajen gina ɗakunan wasanni ba tare da gurɓata muhalli ba, da watsa shirye-shiryen wasanni ta amfani da fasahar sadarwa ta 5G, da ba da hidima masu kyau ga mahalarta gasar. Ban da wannan kuma, Sin ta haɗa gasar Olympic da al’adun Sin tare don samar da wani biki mai ƙayatarwa. Kazalika, taken gasar a wannan karo shi ne “Haɗa kai tare don amfanin gaba”, matakin da ya bayyana aniyar ƙasar Sin na haɗin kan ƙasa da ƙasa don samun makoma mai kyau baki ɗaya.

Kamar yadda Florian Harms ya bayyana, gasar ta zama wani mafari ne ga duniya wajen fahimtar ƙasar Sin, yawancin al’ummar ƙasashen yamma ba su samu cikakkiyar fahimta game da Sin ba. Abin farin ciki shi ne, wasu kafofin yaxa labarai da ‘yan ƙasashen yamma sun ɓullo da hanyar da ta dace wajen fahimtar ƙasar Sin ta hanyar gasar Olympic ta lokacin hunturu da ake yi a birnin Beijing.