10
Feb
*Alƙawarin ɗan siyasa*Kira ga masu neman takarar shugabancin Nijeriya a 2023 Assalamu alaikum. Wata babbar cutar da ke damun matasanmu ita ce rashin sanin yakamata, da kuma jahilci. An mayar da zauren sada zumunta na intanet wani fagen barkwanci, wani lokacin kuma fagen fama inda ake buɗe wuta da kalamai, musamman matasa masu son wasa iyayien gidajensu a siyasance, ta yadda a yawaita yabo ko zagi kamar zogale. Wannan annamimancin na faruwa tsakanin ’yan adawa, ‘yan jam’iyya ɗaya ko ma ’yan uwa ‘yan gida ɗaya. Duk da mun san cewa talauci da jahilci suna taka rawar gani a wajen aiwatar…
