Sana’a: Babbar hanyar samun ingantacciyar rayuwa

Manhaja logo

A wannan makon, Blueprint Manhaja za za ta jawo hankalin matasanmu maza da mata ne game da muhimmancin yin sana’a kowace iri ce, in dai ba ta sava wa doka ba, ko ta saɓa ƙa’idojin da gwamnati ta kafa.

Mun taɓa yin bayani makamancin wannan a watannin baya, saboda muhimmancinsa ne ya sa muka ga ya kamata mu ɗan sake waiwayarsa.

Sana’a ga duk magidanci, ko wani mai neman ya zama yana neman na kansa, ta zama wajibi bisa la’akari da halin da ake ciki a duniyarmu ta yau. Domin ba za a iya cewa gwamnati za ta iya sama wa kowane matashi aikin yi ba, ko da kuwa ya yi karatu zuwa na Digiri ne ko gaba da Digiri, ballantana kuma matashin da bai samu halartar makaranta ba.

Ita sana’a tana da muhimmanci ko da kuwa a ce mutum ya yi karatun boko ne, domin zai iya zama bai samu aiki ba, ko kuma ya samu aikin, amma saboda halin da yau ciki, albashin da yake ɗauka ba ya iya biya masa buƙatunsa na yau da kullum. Domin za ka taras da wani matashin yana da aure, wasu kuma su ke ɗaukar nauyin iyayensu, sannan kuma ga hidindimun dangi da sauran al’ummar da ke tare a ciki.

Sau da yawa akan yi bayanin matasa, matasa, matasa. Wannan ya zama wajibi ne bisa la’akari da cewa su matasan ne ginshiƙin duk wata rayuwa mai ɗorewa ta al’umma. Don haka idan Allah ya sa matasa suka gyaru, to dukkan al’umma ta gyaru.

Saboda haka kuma babu wata hanya ta gyaruwar matashi kamar samun sana’ar dogaro da kai, ta hanyar dogaro da kai ne ake samun matashi natsattse wanda babu ruwansa da shiga duk wani tashin hankali ko aikin da bai dace ba.

Idan matashi yana sana’a, babu yadda za a yi a same shi wajen wasu ayyukan da ba su kamata ba, kamar dai yadda yake a fili cewa duk wani matsahin da aka samu a duk wata hayaniya, to idan aka bincika ba shi da wata takamaimiyar sana’ar da yake cin abinci a ciki, wanda hakan ne ma ke ingiza shi don gudanar da waɗannan munanan ayyuka.

Wani lokaci takaici ya kan kamani idan na ga matashi yana zaune babu wani aikin yi, babu zuwa makaranta, babu zuwa koyon sana’a, babu tavuka komai don samun abin ɗaukar nauyin kansa, ballantana na sauran mabuƙatan da ke tare da shi. Sai ka ga matashi ba ya aikata komai domin kula da rayuwarsa, yana zaune yana sa ido a harkokin mutane.

Irin waɗannan matasa da ba su da sana’ar yi sai dai sa ido, wanda Bahaushe ke cewa ‘sa ido sana’ar banza,’ to irinsu ne waɗanda aka fi saurin amfanai da su wajen aika duk wani nau’i na munanan ayyuka, musamman a wannan lokaci na siyasa, wanda wasu ’yan siyasa ke amfani da su, waɗanda suka gwammace ma buƙatun kansu fiye da na al’umma.

Muna faɗin haka ne bisa la’akari da cewa babu wani matashin da zai iya rufe wurin sana’arsa da yake samun riba, ya tafi ya aikata wani abin da ya san zai iya shafar wannan wurin da yake gidanar da wannan sana’ar, ko kuma aikata wani abin da ya san zai hana shi zama lafiya ko al’ummarsa.

Amma idan ya zama ba shi da sana’ar fa, zai zama ɗan a fasa kowa ya rasa.

A irin wannan ne kuma ake samun irin matasan nan masu fatan Allah kawo tashin hankali, ba don komai ba, sai don kawai su samu yanayin tare mutanen da ba addininsu ɗaya ba, su kashe su sace masu kuɗaɗe da sauran kaya masu amfani da ke jikinsu.

Za ka taras da waɗannan matasa suna da matuƙar buƙatuwa ga abubuwa na rayuwa, manyan wayoyin hannu, sutura mai tsada, neman mata, a wasu ma za ka taras har da shaye-shaye. To idan babu kuɗaɗen da za a yi waɗannan abubuwa, babu tunanin da matashi zai yi illa shiga duk hanyar da zai shiga don samun kuɗaɗen da zai biya wa kansa buƙata, ga shi kuma ya ƙi kama sana’a.

Sai dai duk da waɗannan abubuwa da muke faɗa, ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, akwai matasan da suka duƙufa wajen neman na kansu, waɗanda suke gudanar da sana’o’insu, wasu ma har suna koya ma wasu. Su ke ɗaukar nauyin kansu, na iyalansu da ma na iyayensu.

Haka kuma ko a gwamnatoci ma, akan tarar da wasu gwamnatocin sun duƙufa wajen koyar da sana’o’in hannu ga matasa ta yadda za a su samu abin dogaro da kai, musamman ganin irin rawar da suke takawa a duk wata harka ta tsaro ko ci gaban al’umma ko akasin haka.

Haka kuma baya ga gwamnati, wasu ’yan siyasar ma sukan gudanar da irin waɗannan abubuwa, ta yadda za ka tarar da wani ɗan siyasa, ɗan majalisar dokoki ko na tarayya ko wani mashawarci na Gwamna ko Shugaba ƙasa ya ware ɗan wani abu daga cikin abin da yake samu, yana ɗaukar nauyin wasu matasa wajen koya masu sana’o’i. wannan abin a yaba ne, ina ma a ce kowane ɗan siyasa yana yi haka!

Da wannan ne Blueprint Manhaja ke kira ga matasanmu su dage wajen ganin sun sami wata sana’ar da za su rinƙa yi suna samun abin da za su rinƙa ɗaukar nauyin harkokinsu na yau da kullum. Su rungumi harkar sana’a komi ƙanƙancinta, domin ta haka ne za su zama manyan gobe managarta, waɗanda sun fi ƙarfin wani mara kishin su ya yi amfani da su wajen aikata munanan ayyuka.

Ya zama kowa yana da sana’arsa, ta yadda matashi ko da yana karatun Jami’a ne, to ya zama idan ya samu hutu akwai inda zai je ya yi sana’a, ballantana kuma a ce ba ya zuwa makaranta. Domin ita harka ta makaranta ba kowa ba ne ke da dama ko halin samun zuwa ba, amma sana’a fa? Kowa yana da hali da daman zuwa, matuƙar Allah ya ba shi lafiya.

Sannan kuma, kamar yadda na muka faɗa a sama, yana da kyau gwamnatocin tarayya, jihohi da Ƙananan Hukumomi da saura ’yan siyasa su fito da hanyoyin da za su rinƙa koya wa matasa sana’o’in hannu ta yadda za su samu abin dogaro da kansu. Domin matasa ne ginshiƙin kowace al’umma.