Editor

9513 Posts
Yan siyasar Amurka na cikin damuwa saboda rashin ɓarkewar yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine

Yan siyasar Amurka na cikin damuwa saboda rashin ɓarkewar yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine

Daga CRI HAUSA A ranar 12 ga watan Fabrairu, Shugaban Ƙasar Amurka, Joe Biden, ya sake yin iƙirari a yayin zantawarsa ta wayar tarho da Shugaban Ƙasar Rasha, Vladimir Putin cewa, idan har Rasha ta kai wa Ukraine hari, Amurka da ƙawayenta za su yi wa Rashar taron dangi har sai sun tabbatar da ta ɗanɗani kuɗarta. Game da wannan batu, Putin ya jaddada cewa, Rasha ta kasa gane dalilin da ya sa Amurka take fitowa ɓaro-ɓaro tana bayyanawa kafafen yaɗa labarai kalaman ƙarya cewa, Rasha tana shirin yi wa Ukraine mamaya. Duk da kasancewar Amurkar tana ci gaba da…
Read More
Gwamnatin Amurka ta yi rashin dattaku na ƙwace kuɗaɗen ceton rayuka a Afganistan

Gwamnatin Amurka ta yi rashin dattaku na ƙwace kuɗaɗen ceton rayuka a Afganistan

Daga CRI HAUSA A ranar 11 ga wata, shugaban ƙasar Amurka Joe biden, ya sa hannu kan wani umurni game da kuɗin babban bankin ƙasar Afganistan dake Amurka da aka hana amfani da su, inda aka bayyana cewa, Amurka za ta raba kuɗin da yawansa ya kai dala kusan biliyan 7 kasu biyu, wato za a yi amfani da rabinsa domin biyan kuɗin diyya ga waɗanda suka rasa rayuka ko suka ji rauni yayin haɗarin jirgin saman da ya faru a ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001, saura rabi kuma, gwamnatin Amurka za ta yi amfani da kuɗin domin…
Read More
Yawan Amurkawan da ke kallon gasar Olympic ta lokacin sanyi da ke gudana a Beijing ya zarce miliyan 100

Yawan Amurkawan da ke kallon gasar Olympic ta lokacin sanyi da ke gudana a Beijing ya zarce miliyan 100

Daga CRI HAUSA Jiya Asabar, an yi taron manema labarai karo na 8 a cibiyar watsa labarai ta gasar Olympic ta lokacin hunturu dake birnin Beijing. Kakakin kwamiti mai kula da harkokin Olympic Mark Adams, ya bayyana cewa, yawan mutanen da ke kallon gasar ya kai sabon matsayi. Kakakin ya ce, yawan Sinawa kusan miliyan 515 sun kalli gasar ta CMG kafin ranar 10 ga wata, adadin Amurkawan da suka kalli gasar ya haura miliyan 100 ta tashar NBC. Jami’an IOC da kwamitin shirya gasar na Beijing sun amsa tambayoyin da ‘yan jarida suka yi musu game da ba da…
Read More
Gidauniyar Fasaudat ta tallafa wa ‘yan gudun hijra a Sakkwato

Gidauniyar Fasaudat ta tallafa wa ‘yan gudun hijra a Sakkwato

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato 'Yan gudun hijira dake zaune a Ramen Kura a jihar Sakkwato sun samu tallafin abinci da tufafin sawa daga Gidauniyar tallafa wa marasa ƙarfi daga gidauniyar ta Fasaudat. Baya ga kayan abinci haka ma gidauniyar ta tallafa wa yaran 'yan gudun hijirar da tufafin sawa. Da take ƙaddamar da tallafin shugabar gidauniyar Hajiya Fatima Ahmed Maigari ta yi kira ga matan 'yan gudun hijira da su kula da karatu da kuma tarbiyyar 'ya'yansu. "Ina mai kira a gareku da kada ku dubi halin da kuke cike, ku yi amfani da damar ku wajen sauke nauyin…
Read More
Bunƙasa lantarki: Nijeriya za ta karɓi rancen Dala miliyan 200 daga Japan

Bunƙasa lantarki: Nijeriya za ta karɓi rancen Dala miliyan 200 daga Japan

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnati Tarayyar Nijeriya ta bayyana ƙudurinta na amso rancen Dalar Amurka Miliyan 200 daga hukumar haɗakar kamfanoni  na ƙasar Japan (JICA). Gwamnatin ta bayyana cewa, ba wani abu za ta yi da kuɗaɗen ba illa ta ƙara ƙarfin wutar lantarki a wasu zaɓaɓɓun ɓangarori a cikin jihohin Ogun da Legas. Alhaji Abubakar Aliyu, Ministan Makamashin Nijeriya, shi ya bayyana haka, a yayin da yake amsar baƙuncin wasu wakilai daga hukumar ta JICA a ofishinsa dake birnin tarayyar Abuja, inda ministan ya ƙara da cewa, wannan yunƙuri an yi shi ne domin a ƙara inganta sashen samar da…
Read More
Kwamishinan Zamfara ya ɗauki nauyin auren ’yan mata marayu 20

Kwamishinan Zamfara ya ɗauki nauyin auren ’yan mata marayu 20

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Kwamishinan ma'aikatar raya otal-otal da yawon buɗe ido na jihar Zamfara Hon. Abubakar Abdullahi ya ɗauki nauyin auren yara mata marayu su 20 a ƙaramar hukumarsa Tsafe. Da yake jawabi yayin bikin ɗaurin auren da aka gudanar a fadar mai martaba Sarkin Tsafe ranar Lahadin da ta gabata, mai martaba Sarkin Tsafe Alhaji Muhammad Bawa ya yaba wa kwamishinan bisa jajircewarsa na inganta tarbiyya da rayuwar marasa galihu a yankin. Sarkin ya yi kira ga masu arzikin yankin da su yi koyi da shi wajen inganta rayuwar marasa galihu a masarautarsa. "Ina so in yi…
Read More
Ghana ta ci tarar wani kamfani Dala miliyan shida don silar mutuwar mutane 13

Ghana ta ci tarar wani kamfani Dala miliyan shida don silar mutuwar mutane 13

Gwamnatin Ghana ta ci tarar wani kamfanin haƙar ma’adinai tarar Dala miliyan shida, saboda haɗarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13 a watan Janairu sakamakon fashewar motar da ke ɗauke da nakiya. Fashewar nakiyar ta haifar da ƙaton rami da kuma rushewar gidaje da dama kusa da birnin Bogoso da ke da nisan kilomita 300 daga birnin Accra. Hukumar agajin gaggawa a ƙasar ta ce, bayan mutuwar mutane 13, haɗarin ya raba mutane sama da 700 da muhallinsu. Ministan ma’adinai Samuel Jinapor, ya sanar da cewar, kamfanin Maxam Ghana da ke sarrafa nakiyoyin, ya saɓa wa dokokin hakar ma’adinai…
Read More
Bacci a jikin ɗan adam (2)

Bacci a jikin ɗan adam (2)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI ’Yan uwa masu karatu, Assalamu alaikum. Barkan mu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi da ke kawo mu ku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Idan kun shirya, bismillah! A makon da ya gabata,  na fara bayani ne a kan yadda bacci ya ke a jikin ɗan adam. Inda na fara somin tavin manyan al'amura da sula shafi bacci. Na faɗa cewa bacci maudu'i ne mai faɗin gaske, wanda ya ke da alaƙa da rayuwar ɗan adam ta fuskoki da dama irinsu: nutusuwa,…
Read More
An cafke ɗan shekara 14 mai garkuwa da yin fyaɗe a Zamfara

An cafke ɗan shekara 14 mai garkuwa da yin fyaɗe a Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jami'an hukumar tsaro na Civil Defence sun yi nasarar cafke wani yaro mai suna Sani Suleiman ɗan kimanin shekara 14 da ake zargi da laifin sata da yin garkuwa da mutane a Jihar Zamfara.  Labarin hakan ya fito ne daga bakin babban kwamandan rundar jami'an tsaron farin kaya ta jihar, A.A Spark a lokacin da yake gabatar da mai laifin ga manema labarai ranar Laraba.  A cewarsa, an cafke Suleiman ne a ƙauyen Kadage da ke yankin Masarautar Moriki a Ƙaramar Hukumar Zurmi  Kamar yadda rahoton ya nuna, ƙaramin yaron ya samu horo ne…
Read More
NNPC ya bayyana gidajen man da suka shigo da gurɓataccen mai daga Belgium

NNPC ya bayyana gidajen man da suka shigo da gurɓataccen mai daga Belgium

*Lamarin ya rutsa da Oando, MRS, AY Maikifi da Duke Oil Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Babban Manajin Darakta Kamfanin Man Fetur (NNPC), Malam Mele Kyari, ya bayyana yadda aka shigo da gurɓataccen man fetur mai sinadarin ‘Methanol’ fiye da kima daga Ƙasar Belgium ba tare da an gano shi ba da kuma kamfanonin man da suka shigo da shi. Wannan na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan Ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya nuna cewa, gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin gudanar da wani gagarumin bincike domin bankaɗo al’amuran da suka shafi shigo da kayayyaki da kuma…
Read More