Editor

9513 Posts
Taron manyan jami’ai huɗu da Amurka ta kira ya ƙara fallasa manufar Amurka ta tada hargitsi

Taron manyan jami’ai huɗu da Amurka ta kira ya ƙara fallasa manufar Amurka ta tada hargitsi

Daga CRI HAUSA A baya-bayan nan, ƙasar Amurka ta fitar da rahoton taron ganawar manyan jami’an ƙasashe 4 mai laƙabin "U.S. Indo-Pacific Strategy", rahoton da ya ƙara tabbatar da manufar Amurka, cikin shekarun baya-bayan nan, ta kambama zargin nan na kasancewar “Sin barazana”, da gayyatar ƙawayen ta domin haɗa wani gungu, da fatan yin haɗin gwiwar daƙile ƙasar Sin, ta yadda Amurka za ta cika burin ta na wanzar da danniya, da farfaɗo da tasirin ta a yankin tekun Asiya da Fasifik, da ma sauran sassan duniya. Don haka dai ta bayyana a fili, cewa taron manyan jami’an na Amurka,…
Read More
Kantinan sayar da abincin ƙasar Sin sun bunƙasa fiye da gabanin ɓarkewar annobar COVID-19

Kantinan sayar da abincin ƙasar Sin sun bunƙasa fiye da gabanin ɓarkewar annobar COVID-19

Daga AHMAD FAGAM Masu hikamar magana na cewa, “sai da ruwan ciki ake jan na rijiya.” Haƙiƙa abinci shine ginshiƙin rayuwar duk wata halitatta a doron ƙasa, kuma rayuwa ba ta yiwuwa ba tare da abinci da kuma abin sha ba. A ƙasar Sin fannin abinci wani babban jigo ne da shugabanni da mabiya ke ɗora muhimmanci kansa. Alal misali, ko da a ƙarshen wannan mako, wani rahoto ya bayyana cewa, kamfanonin dake mallakar kantinan sayar da abinci sun samu gagarumar bunƙasuwar da ta kai matsayin koli wacce har ma ta zarce makamancin lokacin gabanin ɓarkewar annobar COVID-19. Rahoton kan…
Read More
MOPPAN ta kama hanyar magance rikicin Kannywood

MOPPAN ta kama hanyar magance rikicin Kannywood

Daga BASHIR ISAH A yayin da ake ci gaba da tafka zazzafar muhawara, Ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta MOPPAN ta bayyana cewa, ta miƙe domin ɗaukar matakin daƙile rikicin da ya kunno kai a masana'antar Kannywood tun bayan da jaruma Ladin Cima ta bayyana cewa abin da ake biyan ta a masana'antar bai taka kara ya karya ba yayin wata tattaunawa da BBC Hausa ta yi da ita. A bayyane yake cewa har ila yau, zancen na ci gaba da jan hankalin al'umma, musamman mabiya lamurran fina-finan Hausa, inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa dangane da batun. Lamarin da ya…
Read More
ASUU ta soma yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya

ASUU ta soma yajin aikin gargaɗi na wata ɗaya

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta soma yajin aiki don neman cimma buƙatunta a wajen Gwamnatin Tarayya. ASUU ta bayyana soma yajin aikin nata ne ga manema labarai a wannan Litinin. Da yake yi wa manema labarai bayani kan matakin da suka ɗauka bayan kammala tattaunawar yini biyu da shugabbanin ƙungiyar suka yi, shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce yajin aikin nasu na tsawon wata guda ne a matsayin gargaɗi ga gwamnatin ƙasa. Ya ce tun a ranar Asabar da ta gabata shugabannin ASUU na ƙasa suka soma zaman tattaunawa a Jami’ar Legas kan batun.…
Read More
Asarar Dala biliyan 27.8 ta ruguzo da Zuckerberg daga sahun attajirai 10 na Duniya

Asarar Dala biliyan 27.8 ta ruguzo da Zuckerberg daga sahun attajirai 10 na Duniya

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu dai mawallafin dandalin Fesbuk, wanda yanzu ya koma Meta, Mista Mark Zuckerberg, ya ruguzo daga sahun attajirai 10 mafiya kuɗi a duniya, inda ya ruguzo i zuwa mataki na 12.  Wannan ragin matsayi na Zukerberg ya faru ne a sanadiyyar asarar da kamfanin nasa na Fesbuk ya yi har ta Dalar Amurka Biliyan 27.8 a tsakanin kwana biyu kacal.  Rahotanni sun bayyana cewa,  asarar ta biyo bayan tsame hannayensu da wasu masu hannun jari suka yi daga kamfanin. Al'amarin kuma ya faru bayan kwana biyu kacal da Zukerberg ɗin ya samu ɗarewa kan muƙamin matsayin…
Read More
Ƙungiyar ’yan fim ta Arewa ta zaɓi Sani Sule Katsina a matsayin sabon shugabanta

Ƙungiyar ’yan fim ta Arewa ta zaɓi Sani Sule Katsina a matsayin sabon shugabanta

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Ƙungiyar masu shirya fim ta Arewa, wato Arewa Film Makers Association Of Nigeria, ta gudanar da sabon zaɓen shugabannin da za su tafiyar da shugabancin ta na gaba a taron da ta gudanar a ranar Lahadin makon jiya. Taron wanda aka gudanar da shi da yammacin ranar Lahadi, 23/1/2022 a wajen taro na Hazeen Event Center da ke cibiyar digan gona a cikin garin Kano, ya samu halarta dukkan wakilai daga jihohin arewacin ƙasar nan da sauran masu ruwa da tsaki a ƙungiyar. Tun da farko da yake bayanin yadda taron ya gudana, shugaban kwamitin…
Read More
’Yan bindiga sun kashe ladani a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ladani a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wasu gungun ‘yan bindiga sun kai hari a cikin wani masallaci a Larabar da ta gabata a cikin garin Magazu a Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, inda suka kashe ladani mai suna Abubakar Muhammad wanda aka fi sani da Abu Dogo ɗan shekara 25. Wani mazaunin garin na Magazu mai suna Malam Isma’il Magazu a wata hira ta wayar tarho da Blueprint Manhaja ya ce ‘yan ta’addan sun kai hari masallacin ne da misalin ƙarfe 5:40 na safiyar ranar ta Laraba. "Kamar yadda nake magana da kai yanzu, an yi jana'izar Marigayi Malam Abu…
Read More
Muhammadu Sanusi ya hango wa Nijeriya tarnaƙin ƙura gabanin zaɓen 2023

Muhammadu Sanusi ya hango wa Nijeriya tarnaƙin ƙura gabanin zaɓen 2023

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Sarkin Kano mai murabus, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya yi hasashen tarin ƙalubaloli da Nijeriya za ta fuskanta gabanin zaɓen shekara ta 2023, yana mai cewar, akwai buƙatar ‘yan takara su yi kyakkyawan shiri domin tunkarar su. Sanusi ya kuma fahimci cewar, ƙasar ta Nijeriya tana zaman bakin kogi ne da lokacin irin wannan zama ya ƙure. Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriyar dai yana jawabi ne a garin Abeokuta ta jihar Ogun, a wani taron liyafa na cika shekaru 80 da rayuwar wani babban basarake, Babanla Addini Mai Ƙasar Egba, Chief Tayo Sowunmi. Tsohon…
Read More
Tsohon ɗan Majalisar Tarayya ya zama hadimin Aisha Buhari

Tsohon ɗan Majalisar Tarayya ya zama hadimin Aisha Buhari

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Hon. Sani Zorro a matsayin Babban mai taimaka masa na musamman a kan Dabarun Hulɗa da Jama'a a ofishin Matar Shugaban Ƙasa. Sabon babban mai taimakawa na musamman a Ofishin matar shugaban ƙasa, Muhammad Sani Zorro dai ƙwararren ɗan jarida ne kuma jagora a aikin jarida a Nijeriya, Afirka, da ma duniya. Babban mai taimaka wa Shugaban Ƙasa a kan harkar yaɗa labarai, Garba Shehu ne ya tabbatar da naɗin a wata sanarwar da ya fitar a Asabar da ta gabata a Abuja. Shehu ya ce Zorro zai yi…
Read More
Sarkin waƙa Naziru ya bai wa Ladin Cima kyautar Miliyan biyu

Sarkin waƙa Naziru ya bai wa Ladin Cima kyautar Miliyan biyu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Naziru Ahmed Sarkin Waƙa ya gwangwaje Ladin Cima, wacce aka fi sani da Tambaya, da kyautar Naira miliyan 2 domin ta fara kasuwanci da magance wasu matsalolinta. Naziru Sarkin Waƙa ya bayyana hakan ne a sahihin shafinsa na Facebook. A makon da ya gabata ne dai Tambaya, wacce ta daɗe tana harkar fim a masana'antar Kannywood, ta tada ƙura, bayan da ta yi wata hira da BBC Hausa, inda ta ce ba a taɓa ba ta sama da Naira dubu 2 ko 3 idan ta yi fim ba, Wanda hirar ta haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin…
Read More