15
Feb
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Ɗaliban Nijeriya wato NANS, ta yi Allah wadai da sabon yajin aikin da Ƙungiyar Malaman Jami’a ASUU suka sake tafiya. A ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu 2022 ne shugaban ƙungiyar NANS na ƙasa, Asefon Sunday ya fitar da jawabi ga manema labarai, yana kokawa a kan wannan yajin aikin. Asefon Sunday ya haɗa da Gwamnatin Tarayya da shugabannin ASUU, ya yi masu ta-tas a kan yadda suka gaza shawo kan batun ba tare da rufe jami’o’i ba. “Mun samu labarin matakin da ƙungiyar ASUU ta ɗauka na shiga yajin aikin jan-kunne na…
