16
Feb
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Kudu kuma Gwamnan Jihar Ondo, Mista Oluwarotimi Akeredolu, a ranar Talata, ya yi gargaɗin cewa, duk jam’iyyar da ta kuskura ta sanya ɗan Arewa a matsayin ɗan takarar Shugaban Ƙasa a shekarar 2023, to za ta faɗi ƙasa warwas. Gwamna Akeredolu ya bayyana cewar gwamnoni a yankin Arewa na ƙasar dake ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Gwamnonin Kudu a shirye take domin tabbatar da cewa shugaban ƙasa ya fito daga yankin Kudu. Gwamnan ya bayyana haka a ofishin sa a lokacin da 'ya'yan jam’iyyar suka kawo masa ziyara masu rajin maida mulki a…
