28
Jun
Wasu daga cikin sababbin matasan da aka ɗiba aikin soja sun yi hatsari yayin da suka taho daga Jihar Imo domin fara karɓar horo a sansanin horar da Sojojin Nijeriya da ke Zariya, Jihar Kaduna, a safiyar Asabar. A cewar wasu majiyoyin soji, masu neman aikin na kan hanyarsu ta zuwa cibiyar horaswa domin fara horon soja lokacin da hatsarin ya faru. An ce tafiyar tana ƙarƙashin kulawar Laftanar Kanal P.D. Ngal. Majiyar ta ce sun tashi daga Jihar Imo zuwa Zariya kafin wannan mummunan hatsari ya afku. Bidiyoyin da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna wasu daga…
