30
Jun
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta amince da aiwatar da manyan sauye-sauye a Hukumar kula da matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), da nufin inganta tsarin gudanar da shirye-shiryenta da kuma daidaita su da buƙatun zamani. Ministan Ci-gaban Matasa, Mista Ayodele Olawande ne ya bayyana haka ga manema labarai, jim-kaɗan bayan ganawa da Shugaba Bola Tinubu a zaman majalisar zartarwa a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ranar Litinin. Daga cikin sauye-sauyen da aka amince da su akwai maye gurbin tsarin jagorancin sojoji da na farar hula a hukumar, tare da sake fasalin kayan aikin masu…
