21
Jun
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Sakwa a Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Hon. Mohammed Wanzam ya rasu a safiyar ranar Lahadi. Har zuwa lokacin rasuwarsa, Hon. Wanzam shi ne shugaban kwamitin kasafi na majalisar. Kakakin majalisar, Rt. Hon. Abubakar Y. Sulaiman ne ya sanar da rasuwar marigayin a wata sanarwa. Mai magana da yawun kakakin, Mukhtar Garba Kobi a sanarwar, ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen ma'aikatacin gwamnati da ya hidimta wa mazaɓarsa da jihar daidai gwargwado. An gudanar da jana'izar marigayin ne a Masallacin Juma'a na Gwallaga da ke garin Bauchi da misalin ƙarfe…
