Babaji

5684 Posts

Tinubu ya sake ƙara wa’adin Shugaban Kwastom Adeniyi da wata shida

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya amince da ƙarin watanni shida a karo na ƙarshe ga wa'adin Kwantirola-Janar na Hukumar Kwastom NCS, Adewale Adeniyi, lamarin da ya ba shi damar cigaba da jagorantar hukumar har zuwa watan Fabarairun 2027. Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ne ya sanar da haka a wata sanarwa, ranar Juma'a. A cewar sanarwar, wa'adin Adeniyi na farko da zai ƙare ne a ranar 1 ga watan Agustan 2026, amma a yanzu Tinubu ya amince da masa ƙarin watanni shida domin samun damar kammala wasu muhimman sauye-sauye a hukumar.. Onanuga ya ce, an…
Read More

Tubabbun ‘yan bindiga sun kashe direba da sace mutane a yankin Birnin Gwari

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu da ake zargin tubabbun 'yan bindiga ne a Jihar Kaduna, sun halaka wani direban motar kasuwa tare da yin awon-gaba da wasu mutane tara a hare-hare biyu da suka ƙaddamar akan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari. Al'amarin ya wakana ne a wani ƙauye da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari a ranar Juma'a. Haka kuma, an ruwaito cewa direban mai suna Mallam Ibrahim Adamu, jika ne ga ɗaya daga cikin hakiman Masarautar Birnin Gwari. A cewar wani ɗan gidan su marigayin da ya zanta da ShaharaReporters, an halaka Ibrahim ne a Kwanan Giginya akan…
Read More

Tinubu ya umarci a tsaurara tsaro a makarantar NIPSS dake Kuru a Jos

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta tsaurara matakan tsaro a Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun Ƙasa (NIPSS) da ke Kuru a Jihar Filato. Shugaba Tinubu ya bada umarnim ne sakamakon wani harin da wasu 'yan bindiga suka kai wa makarantar a kwanan nan. Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya bayyana haka yayin wakiltar Shugaban, inda ya kuma yi alƙawarin cewa Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa iyalan sojoji biyu da ɗan sanda guda da suka rasa rayukansu a harin. Haka kuma, ya umarci mahukuntan NIPSS da su gabatar da cikakken rahoton…
Read More

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta musanta rufe mashigar Hormuz

Ma'aikatar Harkokin Wajen ƙasar Iran ta bayyana cewa babu wani sahihin tushe da ke tabbatar da rahotannin da ke cewa an sake rufe Mashigin Hormuz, daya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar mai da kayayyaki a duniya. Mai magana da yawun ma'aikatar, Esmail Baghaei, ya ce rahotannin da ke yawo kan batun ba su da inganci. Wannan na zuwa ne bayan wasu kafafen yada labarai sun rawaito cewa rundunar IRGC ta sanar da rufe mashigin saboda takaddama da Isra'ila. A cewar yarjejeniyar fahimtar juna da Amurka da Iran suka rattaba wa hannu a wannan mako, an amince a c gaba da…
Read More

Tsohon Shugaban INEC, Farfesa Yakubu ya kama aikin jakadanci a Ƙatar

Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya fara aiki a matsayin jakadan Nijeriya a ƙasar Ƙatar, inda ya samu gagarumar tarba daga jakadun ƙasashen Afrika 13 da manyan jami'ai a birnin Doha. Farfesa Yakubu ya isa Doha a ranar Laraba, inda Daraktan Sashen Ladabi na Ma'aikatar Harkokin Wajen Ƙatar, Jakada Ibrahim Yousif Abdullah Fakhro, ya tarbe shi a filin jirgin sama cikin girmamawa. Haka kuma, jakadun ƙasashen Afrikan, tare da Babban Sakataren Gas Exporting Countries Forum, Dakta Philip Mshelbila, da shugabannin al'ummar 'yan Nijeriya mazauna Ƙatar sun yi masa maraba. Sabon jakadan ya zo da gogewa…
Read More

IPOB ta dakatar da Nnamdi Kanu daga shugabancin Rediyon Biafara har illa ma sha Allah

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Fafutukar kafa Ƙasar Biafara (IPOB), ta ce ta dakatar da Shugabanta, Nnamdi Kanu tare da tsige shi daga muƙamin daraktan Rediyo Biafara a matsayin wani ɓangare na sauya tsare-tsaren jagoranci da ayyukanta. Shugaban kula da harkokin ƙungiyar, Chikadibia Edoziem ya sanar da haka a wata takarda, ranar Alhamis, bisa umarnin tawagar shugabancin ƙungiyar. Edoziem ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne bayan wani taro da aka gudanar a ranar 17 ga Yuni, inda aka yi nazari kan wani rahoton sirri da ya shafi ganawar Kanu da jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) da…
Read More

Kwanan nan ‘yan jarida za su fara raka sojoji fagen fama, inji Ministan Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya na duba yiwuwar gabatar da wani sabon shiri da zai ba 'yan jarida damar raka jami'an tsaro yayin ƙaddamar da wasu atisaye a matsayin wani ɓangare na inganta lamuran tsaro a Nijeriya. Za a yi haka ne da nufin bunƙasa fahimtar yanayin ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta ga 'yan ƙasa da kuma tabbatar da tsare gaskiya da adalci akan harkokin sojoji. Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa ya bayyana a a ranar Alhamis yayin babban taron tsaron ƙasa da Ƙungiyar 'Yan jaridar ta Ƙasa (NUJ) ta shirya a Abuja. Ministan, wanda mai…
Read More

Ku daina ba ‘yan ta’adda satar amsa – Ministan Labarai ga gidajen jaridun Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Al'umma, Mohammed Idris ya yi kira ga gidajen jaridun Nijeriya da su daina buɗe sirri ga 'yan ta'adda da wasu ɓarayi, yana mai cewa cigaba da yawaita yaɗa ayyukansu dama ce ga masu son watsa fargaba da rashin zaman lafiya acikin al'umma. Mohammed Idris ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin babban taro akan tsaro da Ƙungiyar 'Yan jarida ta Ƙasa (NUJ) ta shirya da haɗin-gwiwar Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS), inda ya ce wajibi ne 'yan jarida su samar da daidaito akan 'yancin yaɗa…
Read More

Ana sa ran farashin fetur ya faɗi yayin da ɗanyen mai ya koma ƙasa da Dala 75

Farashin ɗanyen mai ya ragu ƙasa da Dala 75 a ranar Alhamis, karo na farko tun watan Maris, 2026, wato mafi ƙanƙantarsa tun lokacin da aka fara yaƙin Iran, bayan yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Amurka da Iran ta ƙara hasashen samun wadataccen mai a kasuwannin duniya. Farashin man Brent ya sauka da dala 1.59, wato kashi 2%, zuwa dala 77.96 kan kowace ganga, yayin da man West Texas Intermediate (WTI) na Amurka ya ragu da dala 1.83, wato kashi 2.38%, zuwa dala 74.96 kan kowace ganga. Faduwar farashin ya biyo bayan yarjejeniyar mai matakai 14 da Amurka da Iran…
Read More

‘Yan sanda sun kama mai yi wa ‘yan bindiga safarar kayan shayi a Kwara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar 'Yan sanda a Jihar Kwara, ta kam wani da zargi da yi wa 'yan bindiga safara kayan aiki a Ilorin, inda ta ƙwato wasu ababe da ake zargin yana kai wa ƙungiyoyin ta'addanci da ke ayyukasu a dazuka da wasu yankuna a jihar. An yi nasarar haka ne bayan yaɗa wata jita-jitar kai harin 'yan bindiga, lamarin da ya tilasta wa ɗaruruwan iyaye zuwa ɗauko 'ya'yansu a makarantu. A wata sanarwa da Kakakin rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ya fitar a ranar Alhamis, ya ce sashen yaƙi da miyagun laifuka (VCRU) ne ya yi…
Read More