Babaji

5684 Posts

Shettima ya ƙaddamar da muhimman ayyukan raya ƙasa a Ekiti a madadin Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Talata Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar da manyan ayyuka tattali da ababen more rayuwa a garin Ado-Ekiti, Babban Birnin Ekiti, a wata ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar. Daga cikin ababen da aka ƙaddamar akwai sabon ofishin reshe na Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) akan hanyar Old Iyin a Ado-Ekiti da kuma kilomita 1.2 na babbar gada da aka yi wa laƙabi da Okeyinmi, a matsayin gagarumar nasara a fagen ababen more rayuwa da za fa sauƙaƙe lamuran zirga-zirga a birnin. Kakakin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha…
Read More

Ministan Labarai zai jagoranci babban taron NUJ kan tsaro a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar 'Yan jarida ta Ƙasa (NUJ) ta sanar da cewa Ministan Labarai da Wayar da kan Al'umma, Mohammed Idris ne zai jagoranci babban taronta na kwana biyu akan tsaro da za a gudanar a Abuja. Shugabar kwamitin shirya taron, Abimbola Oyetunde a wata sanarwa a Abuja ta bayyana haka, idna ya ce taron tsaron zai ƙunshi haɗin-gwiwa tsakanin 'yan jarida da hukumomin tsaro domin masalaha ɗorewa al'amuran ci-gaban ƙasa. Ta ce, an tsara gudanar da zaman ne a ranar 18 ga Yuni, 2026 mai taken "Media and Security Agencies as Partners in Nation Building".…
Read More

UTME ta 2026: JAMB ta buƙaci waɗanda aka shirya wa sabuwar jarrabawa su fitar da takardun shaida

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), ta yi kira ga ɗaliban da aka sake shirya wa jarrabawar UTME ta 2026 da su fitar da takardar shaidarsu gabanin ranar rubuta ta, wato 13 ga Yuni. A wata sanarwa da JAMB ta fitar a ranar Litinin ta bakin Kakakinta, Fabian Benjamin, ta ce a yanzu waɗanda suka cancanta suna da damar fitar da takardar bayan ta buɗe sahihin shafinta. Benjamin ya ce, takardar ta ƙunshi bayanai kamar cibiyar da ɗalibi zai rubuta, rana, lokaci da wasu dokoki da suka shafi jarrabawar. Ya kuma ce, an…
Read More

Sanannen basaraken Nijeriya ya rasu a Misra

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Masarautar Ngazargamu ta sanar da rasuwar sarkinta Mai Martaba Mai Ngazargamu Alhaji Tijjani ibn Saleh Geidam. Marigayin ya rasu ne a ranar Talata, 9 ga watan Yuni, 2026 a Misra bayan tsawon lokaci yana jinyar rashin lafiya, kamar yadda wata sanarwa daga masarautar ta bayyana. Za a kawo gawar marigayin zuwa Nijeriya domin yi masa jana’iza a Damaturu, inda masarautar ta ce za a sanar da rana lokaci daga bisani. Alhaji Muhammad Alamai Baba Kankare, wanda ya sanya wa sanarwar hannu kuma Wazirin masarautar, ya roƙi jama'ar Musulmi da su sanya marigayin a addu'o'insu…
Read More

Jagoran ‘yan bindiga, Kachalla ya bada sharuɗɗan sako Janar Rabe da iyalinsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanannen jagoran 'yan bindiga a Jihar Katsina, Muhammad Kachalla ya bayar da sharaɗi na musamman akan sako Manjo-Janar Abubakar Rabe (mai ritaya) da matarsa, Hajiya Amina Abubakar. A cewar Kachalla, ya tattauna da iyalan mutanen biyu bayan garkuwa da su. Manjo-Janar Rabe, wanda shi ne tsohon Daraktan hulɗa da jama’a na hedikwatar tsaro, an sace shi ne da iyalin nasa da kuma direbansa, Abdullahi Sa’idu a lokacin da suke kan hanyar koma wa Katsina daga Kaduna, lokacin da 'yan bindigar suka yi wa motarsu ƙawanya a yankin Kafin-Soli da ke Ƙaramar Hukumar Matazu a…
Read More

NDC ta yi ganawar sirri da ‘yan Kwankwasiyya kan rikicin cikin gida

Jagororin ƙasa na tafiyar Kwankwasiyya sun gudanar da wata ganawa ta musamman da jagoran jam’iyyar NDC na ƙasa, Henry Seriake Dickson, tare da sauran shugabannin jam’iyyar domin tattauna matsalolin da suka kunno kai tsakanin tafiyar Kwankwasiyya da wasu tsoffin shugabannin NDC a Jihar Kano. A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam’iyyar, Barrista Osa Director, ya fitar, an bayyana cewa an gudanar da taron ne a cikin sirri, inda shugabannin NDC suka yi sasanci da nufin samar da haɗin kai da tabbatar da bai wa kowane ɗan jam’iyya damar shiga cikin harkokin jam’iyyar. Sanarwar ta ce…
Read More

Amurka ta soke tikitin Kofin Duniya da aka ware wa Iran kwanaki kaɗan gabanin gasar

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta kasar Iran ta ce ƙasar Amurka ta soke kaso mai yawa na tikitin da aka ware wa magoya bayanta, domin kallon wasannin rukuni na gasar Kofin Duniya, tana mai zargin ɗaya daga cikin ƙasashen da ke karɓar baƙuncin gasar Amurka da hana magoya bayan nata damar halartar wasannin. Ana ganin hakan a matsayin matakin da aka ɗauka saboda tsamin dangantakar difulomasiyya da ke tsakanin ƙasashen biyu. A cewar hukumar, Amurka ta sanya wasu matsalolin gudanarwa da na takardu da suka shafi shiga ƙasar ga tawagar Iran a babbar gasar ta Duniya, ciki har da ƙin ba…
Read More

‎Majalisar Wakilai ta gayyaci jagororin tsaro da Ribaɗu kan taɓarɓarewar tsaro

Majalisar Wakilai ta gayyaci manyan hafsoshin tsaro da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Akan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu, domin su bayyana a gabanta kan cigaba da taɓarɓarewar al'amuran tsaro a sassan ƙasar.‎‎Matakin ya biyo bayan amincewa da wani ƙudirin gaggawa da ɗan majalisar mai wakiltar mazaɓar Gummi/Bukkuyum ta Jihar Zamfara, Hon. Sulaiman Abubakar Gumi, ya gabatar a zaman majalisar na ranar Talata.‎‎Ɗan majalisar ya bayyana damuwarsa kan yadda hare-haren 'yan bindiga, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da kashe-kashen fararen hula ke ci gaba da ƙaruwa a jihohi da dama, lamarin da ya ce yana barazana ga…
Read More

Majalisar Dattawa za ta hanzarta kammala aikin dokar ‘yan sandan jihohi kan taɓarɓarewar tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dattawa za ta fara aikin tabbatar da dokar kafa 'yan sandan jihohi yayin da ta fara zamanta na yau Talata, kamar yadda Sanata Opeyimi Bamidele ya sanar a ranar Litinin. Ya ce, jagorancin Majalisar Dokokin Ƙasa ya yanke shawarar ware dokar kafa 'yan sanda da ainihin hanyoyin nazari akan kundin dokar ƙasa. A cewarsa, suna haka ne don la'akari da halin da 'yan Nijeriya ce ciki na rashin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, lamarin da ya sa suka sanya dukkan masu ruwa da tsaki aciki tun daga kan shugaban ƙasa har zuwa…
Read More

Gocewar jirgin ƙasa na Warri zuwa Itakpe ya yi ajalin fasinjoji uku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An tabbatar da rasuwar fasinjoji guda uku bayan wata gocewa da jirgin ƙasa na Warri zuwa Itakpe ya yi. Rahotanni sun bayyana cewa al'amarin ya auku ne a ranar Litinin, wanda ya sa hukumomi suka gaggauta kai agaji da kuma fargabar rashin aminci a fannin sufurin jiragen ƙasa na Nijeriya. Da take tabbatar da faruwar al'amarin, Hukumar Kula da Tashoshin jiragen ƙasa ta Ƙasa (NRC), ta ce tawagar bayar da agajin gaggawa sun je wajen da abin ya faru domin agaza wa waɗanda al'amarin ya shafa. NRC ta kuma ce, tana kula da ci-gaban…
Read More