09
Jun
Tsohuwar Ministar Harkokin Jin-ƙai da Ci-gaban Jama'a, Sadiya Umar Farouq, ta roki Babbar Kotun Abuja da ta soke sammacin kame da aka bayar a kanta. Farouq ta gabatar da bukatar ne bayan kotun ta bai wa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) izinin gurfanar da ita tare da tsohon Babban Sakataren ma'aikatar, Bashir Alkali, da Sani Mohammed a ranar 16 ga Afrilu. Rahotanni sun nuna cewa EFCC na zargin wadanda ake tuhumar da hannu a wasu batutuwan da suka shafi gudanar da kudaden gwamnati a lokacin da suke rike da mukaman gwamnati. Lauyoyin Farouq sun bukaci kotun da…
