11
Jun
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai Martaba Sarkin Ilorin kuma Shugaban Majalisar Sarakunan gargajiya na Jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya naɗa Sheikh Muhammad Bashir Dasuki Imam Fulani a matsayin Babban Limanin Masarautar Ilorin. Kakakin sarkin, Dakta Abdulazeez Arowona ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Ya ce, an yi naɗin ne bayan dogon nazari da zaɓe akan al'amarin, inda Imam Fulani ya yi nasarar zama wanda aka zaɓa don riƙe muƙamin daga cikin sauran malaman. Ya gaji Alhaji Muhammad Bashir Imam OON, wanda ya rasu a ranar 19 ga watan Junairu, 2026.…
