Babaji

5684 Posts

Ministan Tsaron Birtaniya ya yi murabus

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Tsaron Birtaniya, John Healey ya yi murabus, bayan ya zargi Firaministan ƙasar, Keir Starmer da gazawa wajen cika alƙawuran inganta kuɗaɗen da ake kashewa a aikin soji. A wasiƙarsa ta Murabus, Mista Healey, ya ce Keir Starmer da ma'aikatar kuɗi ba su fitar da kuɗaɗen da ake buƙata wajen bada tsaron ƙasa, lamarin ya sa ya shiga damuwa akan ƙaruwar barazanar tsaro daga Rasha. A cewar wakilin BBC, ya ga wasiƙun murabus da dama a rayuwarsa amma bai taɓa ganin mafi ban mamaki kamar ta Healey ba. Shirin inganta tsaron ƙasa na Birtaniya…
Read More

Sojoji sun halaka jagoran ISWAP, Khalifa yayin da kwamandoji biyu suka miƙa wuya a Borno

Wasu manyan da ake zargi mambobin ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP guda biyu ciki har da wani ƙwararren mai ƙera boma-bomai da kuma wani kwamanda, sun miƙa wuya ga dakarun sojin Nijeriya a jihar Yobe. Rahotanni sun bayyana cewa mutanen biyu, da aka bayyana sunayensu da Abu Umar da Ismail Mohammed, sun mika kansu ga sojojin Bataliya ta 159 a garin Geidam ranar 8 ga watan Yuni kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito. Majiyoyin tsaro sun ce Abu Umar na daga cikin fitattun kwararrun ISWAP wajen kerawa da amfani da bama-baman da ake dasawa a cikin motoci domin kai hare-hare. Sun…
Read More

Ku miƙa wuya yanzu ko ku fuskanci uƙuba daga gwamnatin Nijeriya – Tinubu ga ‘yan ta’adda

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da su miƙa wuya ko kuma su fuskanci ƙarfin gwamnati akan miyagun laifukan da suka aikatawa wauen cutar da al'umma a sassan Nijeriya. Rahotanni sun bayyana cewa, Tinubu ya bayyana hakan ne acikin saƙonsa na Ranar Dimukraɗiyya ta 12 ga watan Yunin 2026. Ya ce, Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ta’addanci, inda ta lalata wani babban sansanin ISWAP a yankin Arege da ke Jihar Borno. Ya ƙara da cewa, yawan mutanen da ake kashewa sakamakon ta’addanci…
Read More

Jami’an tsaro sun halaka sanannun jagororin ‘yan bindiga biyu a Jihar Kogi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Alhamis Rundunar 'Yan sanda a Jihar Kogi, ta sanar da wata gagarumar nasara na mutuwar wani sanannen jagoran 'yan bindiga mai suna Ibrahim Baccujo bayan wani ba-takashi da jami'an tsaro a jihar. Al'amarin ya auku ne a lokacin jami'an suka yi yunƙurin daƙile garkuwa da wasu tarin ɗalibai da ke rubuta jarrabawar WAEC a makarantar sakandare ta Iluke da ke Ƙaramar Hukumar Kabba-Bunu a ranar 10 ga Yuni, 2026. A wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'ar rundunar, ASP Saliu Oyiza Afusat ya fitar, ya ce Baccujo na ɗaya daga cikin 'yan…
Read More

Ranar Dimukraɗiyya: Abiola, Yar’Adua, Sambo Dasuƙi, Jaafaru Isa da wasu sun shiga sahun waɗanda Tinubu ya karrama

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama wasu manyan mutane su 50 da kyautar ƙasa sakamakon rawar gani da suka taka wajen gwagwarmayar kafa dimukraɗiyya a Nijeriya. Daga cikin waɗanda aka karrama a Ranar Dimukraɗiyyar akwai 'yan jarida, jagororin fafutukar 'yancin al'umma da wasu manyan sojoji da suka yaƙi mulkin soji a ƙasar. Shugaba Tinubu ya sanar da haka ne a saƙonsa na ranar 12 ga Yuni a matsayin ɓangaren harkokin Ranar Dimukraɗiyya. A cewarsa, 'yan Nijeriya sun amfana da sadaukarwar 'yan fafutukar kafa mulkin dimukraɗiyya wajen ba shi kariya da ƙarfafa cibiyoyin harkokinsa. Ya…
Read More

Gwamnatin Zamfara ta ƙaddamar da taswirar faɗaɗa Gusau da wasu birane

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Zamfara ta ƙaddamar da fayyacacciyar taswirar faɗaɗa Gusau, Babban Birninta da wasu birane a faɗin jihar. Taswirar za ta bayar da damar faɗaɗa jihar na tsawon shekaru 20. Shirin ya ƙunshi samar da titina, ayyukan ci-gaban yawan al'umma, asibitoci, makarantu, ofisoshin gwamnati da cibiyoyin tsaro. Kwamishinan Raya Gidaje da Birane na jihar, Ibrahim Nasiru Zurmi ne ya bayyana a haka a Gusau yayin hira da gidan rediyo Nijeriya. Ya ce, tsarin aikin zai faɗaɗa daga Gusau zuwa Bunguɗu saboda kusancin iyakoki da kuma Ƙaramar Hukumar Tsafe. Alhaji Ibrahim Zurmi ya bayyana cewa,…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta ayyana 12 ga Yuni a matsayin hutu don karrama Ranar Dimukraɗiyya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Juma’a, 12 ga watan Yuni, 2026, a matsayin ranar hutu domin bikin Ranar Dimukraɗiyya ta ƙasa. Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya ce ranar 12 ga Yuni tana da muhimmanci a tarihin Nijeriya, domin tana tuna wa al’umma sadaukarwa, jajircewa da gwagwarmayar da ‘yan ƙasar suka yi wajen tabbatar da mulkin dimukraɗiyya. Gwamnatin ta kuma jaddada aniyarta ta cigaba da kare dimukraɗiyya, tabbatar da bin doka, gaskiya, riƙon amana da shugabanci mai haɗa kan kowa. A shekarar 2018 ne marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya ayyana…
Read More

Majalisar Dattawa ta soke izinin kama Kyari, ta nesanta kanta daga kalaman Oshiomhole na adawa da NNPC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Alhamis Majalisar Dattawa ta sanar da nesanta kanta daga sammacin kama tsohon Shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, wanda Kwamitin Majalisar kan kuɗaɗen al'umma ya bayar. Haka kuma, Majalisar ta bakin jagoran masu rinjaye, Sanata Bamidele Opeyemi, ta bayyana cewa kalaman da aka danganta ga Sanata Adams Oshiomhole, mai wakiltar Edo ta Arewa ba su wakiltar matsayar shugabancinta. An ce Oshiomhole ya bayyana NNPC a matsayin “gungu na masu laifi da ɓarayi” yayin zaman kwamitin a ranar Laraba, amma Majalisar Dattawa ta yi watsi da danganta waɗannan kalamai da…
Read More

‘Yan Nijeriyar da aka kwaso daga Afirka ta Kudu kan ɓangaranci sun isa Legas

Gwamnatin Tarayya ta ce kaso na farko na ’yan Nijeriya da aka kwaso daga Afirka ta Kudu sakamakon hare-haren ɓangaranci da ƙyamar baƙi ya isa Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas da safiyar yau Alhamis. Kakakin Ma'aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, inda ya ce ana sa ran jirgin zai sauka da misalin ƙarfe 5:00 na safe. Sanarwar ta ce jirgin kamfanin sufurin jiragen sama na Air Peace zai tashi daga Filin Jirgin Sama na Oliver Tambo da ke Johannesburg a daren ranar Laraba. Ebienfa ya…
Read More

WAEC: ‘Yan bindiga sun sace ɗalibai suna tsaka da jarrabawa, sun halaka mataimakin shugaban makaranta da wasu biyu a Kogi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba 'yan bindiga suka kutsa makarantar sakandare ta Iluke Bunu a Ƙaramar Hukumar Kabba-Bunu ta Jihar Kogi, inda suka halaka mutum uku ciki har da mataimakin shugaban makaranta tare da yin awon-gaba da wasu ɗalibai a yayin da ake rubuta jarrabawar kammala sakandare (WASSCE). Rahotanni sun bayyana cewa al'amarin ya auku ne da misalin ƙarfe 9:45 kuma an hari ɗalibai masu rubuta jarrabawar ne kai tsaye. Wata majiya daga yankin ta ce maharan sun hari makaranta UBE ne a garin, inda ɗalibai daga ƙauyuka uku suek taruwa don rubuta jarrabawar WAEC. Majiyar…
Read More