Babaji

5684 Posts

NAHCON ta yi ƙarin haske kan dawowar alhazan Nijeriya gida

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A halin yanzu an shiga rana ta goma a aikin jigilar alhazan Nijeriya na koma wa jihohinsu bayan nasarar kammala aikin hajjin 2026, kamar yadda Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta bayyana. A yayin haɗa wannan rahoto, jimillar alhazai guda 17,347 ne aka mayar da su Nijeriya daga ƙasa mai tsarki, Saudiyya. A sakamakon haka wasu jihohi sun kammala karɓar nasu alhazan. A wata sanarwa da hukumar gudanarwar hukumar ta fitar a ranar Asabar, 13 ga Yuni, 2026, NAHCON ta ce jihohin da suka kammala karɓar mahajjatansu sun haɗa da Nasarawa, Gombe, Kogi, Oyo,…
Read More

Hajiya Fatima Ladi Binta, mahaifiyar Ministar Al’adu, Hannatu Musawa ta rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'ummar Musulmi sun shiga jimami a sakamakon rasuwar Hajiya Fatima Ladi Binta Musa Musawa, wato mahaifiyar Ministar Al'adu, Hannatu Musa Musawa. A cewar wata sanarwa da iyalanta suka fitar, za a yi mata sallar jana'iza bayan sallar azahar a yau Assabar a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja. Za a kuma a binne marigayiyar ne a maƙabartar yankin Gudu da ke babban birnin. Tuni dai dangi, abokai da sauran suka shiga yi wa Hajiya Binta addu'ar fatan samun rahamar Allah, yayin da aka buƙaci da su halarci jana'izarta. A ƙarshe, sanarwar ta yi fatan…
Read More

Manjo Janar Rabe ya rasu a hannun ‘yan bindiga

Daga UMAR GARBA a Katsina Tsohon kakakin rundunar sojin Nijeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya) ya rasa ransa a hannun 'yan bindiga. Kwamishinan tsaron jihar Katsina Dr. Nasuru Ma'azu Damnusa ne ya tabbatar da mutuwar ta sa, inda yanzu haka ana shirye shiryen xauko gawarsa daga dajin da ake tsare da shi. 'Yan bindiga masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa, sun sace tsohon Janar xin tare da matarsa a hanyar Matazu a yayin da suke cikin mota don halarta xaurin aure. Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa ya rasu ne yayin da yake hannun ‘yan bindiga duk…
Read More

Shettima ya je jana’izar Sarkin Ngazargamu, Tijjani Ibn-Saleh

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce rayuwar marigayi Sarkin Masarautar Ngazargamu, Alhaji Tijjani Ahmed Ibn Saleh abar koyi ce ga al'umma. Shettima ya bayyana haka ne a lokacin da ya je jana'iza da ta'aziyyar rasuwar sarkin, wanda ya rasu a ƙasar Misra bayan fama da rashin lafiya na tsawon lokaci, yana mai cewa wajibi ne 'yan ƙasa musamman matasa su cigaba da neman ilimi kamar yadda ya wa'azantar. Da yake ganawa da manema labarai a Damaturu, Jihar Yobe, jim-kaɗan bayan jana'izar marigayin, Shettima ya ce sarkin ginshiƙi ne na haɗin kai, zaman lafiya…
Read More

Elon Musk ya zama attajiri na farko a duniya da ya mallaki Dala tiriliyan

Wanda ya samar da kamfanin SpaceX kuma shugabansa, Elon Musk, ya zama mutum na farko a tarihin duniya da dukiyarsa ta haura dala tiriliyan ɗaya, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta CNN ta ruwaito. Wannan nasara ta samu ne sakamakon fara sayar da hannayen jarin kamfanin SpaceX a kasuwar hada-hadar hannayen jari, lamarin da ya jawo gagarumin ƙaruwa a darajar kamfanin. SpaceX ta fitar da hannayen jarinta kan farashin dala 135 kan kowane kaso, abin da ya sa an kiyasta dukiyar Musk ta haura dala tiriliyan ɗaya. Hannayen jarin kamfanin, da ake cinikinsu da alamar “SPCX” a kasuwar Nasdaq, sun…
Read More

Birtaniya ta jinina wa Uba Sani kan cigaban Kaduna

Gwamnatin Ƙasar Birtaniya ta sake nuna amincewarta da salon mulkin Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, inda ta yaba da sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa tare da jaddada aniyar ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen raya jihar. Yabon ya fito ne daga Ministar Harkokin Raya Ƙasa da Afirka ta Birtaniya, Jenny Chapman, yayin wata ziyarar aiki da ta kai gidan gwamnatin jihar Kaduna domin duba tasirin ayyukan haɗin gwiwa da Birtaniya ke tallafawa a fannoni daban-daban. Ministar ta bayyana cewa gwamnatin Uba Sani ta nuna jajircewa wajen aiwatar da gyare-gyaren da suka ƙarfafa cibiyoyin gwamnati, inganta gaskiya da riƙon amana…
Read More

Ranar Dimukraɗiyya: Gwamnan Kaduna ya saki fursunoni 97, ya tallafa musu da jari

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya saki fursunoni 97 da ke Gidan gyaran hali na Kaduna, inda ya ba su ‘yanci tare da tanadar musu tallafin kuɗi da damar koyon sana’o’i domin fara sabuwar rayuwa. Da yake jawabi a wajen bikin da aka gudanar a gidan gyaran halin Kaduna, Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa ranar 12 ga Yuni wata rana ce mai muhimmanci a tarihin Nijeriya, wadda ke tunatar da al’umma irin sadaukarwar da jaruman dimokuraɗiyya suka yi wajen tabbatar da mulkin farar hula da ‘yancin jama’a. Gwamnan ya ce sakin fursunonin ya biyo bayan amfani da ikon…
Read More

Kwamitin zartarwar ƙungiyar shirya finafinan Arewa ya gudanar da taron ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) na Ƙungiyar Masu Shirya Finafinan Arewa ya gudanar da babban taro da ya haɗa mambobinsa daga sassa daban-daban. An gudanar da taron ne a ranar Talata, 9 ga watan Yuni, 2026, wanda aka yi da nufin sauya fasalin ƙungiya da kuma samar da hanyoyin ƙarfafa harkokin bisa tsari mai kyau. Shugaban ƙungiyar, Salisu Mohammed Officer, a wata takarda da Sakataren ƙungiyar Sani Sule Katsina ya fitar, ya jaddada muhimmancin haɗin kai akan lamuran buƙatun masana'antar shirya finafinai da kuma ɗaukacin al'umma, wanda ka iya haifar da gagarumar ci-gaba ga…
Read More

Trump ya janye sabon yunƙurin Amurka na kai wa Iran hari

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da soke hare-haren da aka shirya kai wa Iran bayan Tehran ta yi barazanar cewa za ta ƙara tsananta yaƙin idan aka cigaba da sabon yaƙin. Trump ya ce, an samu cigaba a tattaunawar da ake yi, saboda haka an dakatar da hare-haren da aka tsara, duk da cewa takunkumin ruwan teku kan Iran zai ci gaba da aiki. Sai dai jami'an Iran sun yi gargadin cewa duk wani sabon hari daga Amurka zai fuskanci martani mafi tsauri, kuma hakan na iya ƙara faɗaɗa rikicin a yankin.…
Read More

‘Yan sanda sun harbi ɗan gwagwarmaya, Sowore yayin zanga-zanga a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An garzaya da ɗan fafutukar 'yan ɗan-adam kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore zuwa asibiti bayan ya faɗi sakamakon arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga. Al'amarin ya faru ne a yankin Unity Foundation da ke Birnin Tarayya Abuja, ranar Juma'a. Masu zanga-zangar sun yi cincirindo ne don nuna adawarsu halin da rashin tsaro, matsin tattali da abin da ya suka kira da "shugabanci mara kyau" da al'ummar Nijeriya ke fuskanta. A cewar jaridar Vanguard, shaidu sun ce zanga-zangar, wadda ta haɗa 'yan gwagwarmaya da ƙungiyoyin al'umma, ta samu tsaiko ne a…
Read More