15
Jun
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shahararren tsohon ɗan wasan ƙungiyar Arsenal, Thierry Henry ya yi ƙarin haske game da kalamansa akan Nijeriya yayin gasar Kofin Duniya na 2026 da ke gudana, yana mai cewa ba a fahimci tsokacinsa ba ne kuma ba da nufin cin fuska ya yi su ba akan ƙasar. Tsohon ɗan wasan na Faransa ya bayyana haka ne yayin hira a shirin iShowSpeed gabanin wasan Amurka da Paraguay na rukunin D, wanda Amurkawa suka yi nasara da ci 4 da 1. Henry ya yi barƙwancin ne a lokacin da aka ga 'yan wasan Amurka sun shiga…
