18
May
Tsohon gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello, ya samu amincewar kwamitin tantance ‘yan takarar jam’iyyar APC domin shiga zaɓen fidda gwani na kujerar Sanatan Kogi ta Tsakiya a zaɓen 2027. Rahotanni sun bayyana cewa sunan Yahaya Bello ya fito cikin jerin ‘yan takara 17 da APC ta tantance daga yankunan sanatoci uku na jihar domin fafatawa a zaɓen fidda gwani da za a gudanar ranar Litinin. A kwanakin baya dai an yi ta raɗe-raɗin cewa tsohon gwamnan na iya fuskantar cikas wajen samun damar shiga takarar, sai dai fitowar sunansa cikin jerin waɗanda aka tantance ya kawo ƙarshen jita-jitar. Yahaya Bello…
