Babaji

5684 Posts

ADC ta naɗa tsofaffin gwamnoni a matsayin jagororin zaɓen fidda gwanin takarar shugaban ƙasa

Jam’iyyar adawa ta ADC ta naɗa tsohon Gwamnan Jihar Cross River, Sanata Liyel Imoke, da tsohon Gwamnan Jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, domin jagorantar kwamitocin zaɓen fidda gwani gabanin zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa da jam’iyyar za ta gudanar nan gaba. Yayin da Sanata Imoke zai kasance Shugaban Kwamitin Tantance ’Yan Takarar Shugaban Ƙasa, Abdulfatah Ahmed zai jagoranci Kwamitin Zaɓen Shugaban Ƙasa, kamar yadda Sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Bolaji Abdullahi ya bayyana. Sauran mambobin Kwamitin Tantance ’Yan Takarar Shugaban Ƙasa sun haɗa da Hon. C.I.D. Maduabum a matsayin Sakatare, Alhaji Lawal Batagarawa, Farfesa Bode Ayorinde, Hon. Nnena Elendu-Ukeje, Farfesa David…
Read More

Ɗan uwan Gwamna Zulum ya ci zaɓen fidda gwanin APC a Borno

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakta Kaumi Zulum, wanda ɗan uwan Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ne, ya lashe zaɓen fidda gwani a jam'iyyar APC na mazaɓar tarayya ta Dikwa/Konduga/Mafa a Majalisar Wakilai. Baturen zaɓen yankin, Jones Erue a wani taron manema labarai a Maiduguri, ya ce Zulum ne wanda ya lashe zaɓen ba tare da abokin karawa ba. Haka kuma, Mista Erue ya sanar da Fati Alƙali a matsayin 'yar takara kujerar Majalisar Wakilai ta mazaɓar tarayya ta Mobbar, Guzama, Abadam da Kukawa. Sannan, ya sanar da Usman Zana a matsayin ɗan takarar APC na Magumeri/Kaga/Gubio.…
Read More

Zaɓen fidda gwanin APC: An kada ɗan tsohon Shugaban Jam’iyya da Kakakin Majalisar Nasarawa

Kakakin Majalisar Dokokin jihar Nasarawa, Rt. Hon. Danladi Jatau, ya rasa damar tsaya wa takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Keffi/Karu/Kokona bayan shan kaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC. Rt. Hon. Danladi Jatau ya samu ƙuri’u 5,873 ne kacal, yayin da abokin takararsa, Hon. Daniel Ogazi, ya lashe zaɓen da kuri'a 13,083. Jaridar Punch ta ce haka kuma wasu ‘yan majalisar wakilai biyu masu ci sun rasa tikitin komawa takara bayan kammala zabukan fitar da gwani a cikin lumana a mazabunsu daban-daban. Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan majalisar da abin ya shafa sun hada da Mohammed Abdulmumini…
Read More

Babban Sakataren Bauchi ya rasu yayin aikin Hajji a Makkah

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Sakataren Sashen Ayyuka na Musamman na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Shehu Yahaya Jalam, ya rasu a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya yayin da yake gudanar da aikin Hajji. Jalam, wanda kuma shi ne Turakin Dawakin Misau, ya rasu ne a safiyar Lahadi bayan rashin lafiya yayin aikin Hajji a lokacin da yake tare da tawagar mahajjatan Jihar Bauchi, kamar wata sanarwa ta bayyana. Tuni dai gwamnatin Jihar Bauchi ta bayyana alhini da jimami akan rashin babban jami'in, tana mai cewa rasuwarsa babban rashi ne ga ma’aikatar gwamnati da kuma ofishin da yake…
Read More

Kano: Hukumar tace finafinai ta dakatar da Adamu Garba da Amina Rani kan bidiyon baɗala

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta dakatar da taurarin fim guda biyu, wato Amina Uba da aka fi sani da Amina Rani da kuma Adam Garba da aka sani da Raba Gardama, bisa zargin su da fitar da bidiyon baɗala acikin al'umma. A cewar Babban Sakataren hukumar, Abba El-Mustapha, an dakatar da taurarin biyu ne na tsawon shekara guda daga shiga dukkan harkokin fim a Jihar Kano bisa saɓa wa dokokin hukumar. A wata sanarwa da Kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a ranar Lahadi, an yi gargaɗin cewa matuƙar aka saɓa…
Read More

Ɗan Majalisar Wakilai, Yusuf Gagdi ya faɗi a zaɓen fidda gwanin APC a Filato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Pankshin/Kanke/Kanam, Yusuf Gagdi ya faɗi a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC da aka gudanar a Jihar Filato. An sanar da sakamakon zaɓen ne a Ƙaramar Hukumar Pankshin daga Baturen zaɓen yankin, Daspan Ishaya, wanda ya ayyana Dakta John Tongshinen a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan samun kuri’u 29,968. Gagdi, wanda ke neman koma wa kujerar a karo na biyu, ya samu ƙuri’a 5,849 yayin da wani takara mai suna John Pia, ya samu guda 51. Dalla-dallar bayanan sakamakon zaɓen ya nuna cewa Tingshinen shi…
Read More

Sarkin Malaman Gaya, Sheikh Munzil ya cika shekara biyu a sarauta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin, 17 ga watan Mayu, 2026 ne Sheikh Munzil ya cika shekara biyu cif a Sarautar Sarkin Malaman Gaya bayan gadar mahaifinsa a muƙamin. A wata takarda da ya fitar, Sheikh Munzil ya godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa ƙaddara masa samin damar da ya samu, yana mai addu'ar fatan samun rahama ga marigayin mahaifin nasa da ya bar muƙamin. Ya kuma yi godiya ga Mai Martaba Sarkin Gaya, Kirmau Mai Gabas, bisa amincewa da ya yi da shi waje naɗa shi ia matsayin. Haka kuma, ya miƙa godiya ga Gwamnan Jihar…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta bada belin El-Rufa’i akan miliyan N100

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayar da belin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i akan Naira miliyan 100 da gabatar da mutum ɗaya da zai tsaya masa. Alƙalin a yayin hukuncin a yau Litinin, ta ce wajibi ne wanda zai tsaya masan ya zama yana zama a unguwar Maitama ko gundumar Asokoro na birnin tarayya Abuja, kuma sai ya bayar da takardar mallakar fili ta asali ga ofishin rajistar kotun. Haka kuma, wajibi ne sai ya zama ma'aikacin gwamnati wanda bai yi ƙasa da muƙamin mai matsayi…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Sojojin Nijeriya da Amurka sun halaka mayaƙan ISWAP 20 kwanaki kaɗan da kisan kwamandan ISIS

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar Sojojin Nijeriya da ke aiki da haɗin-gwiwar Sashen Dakarun Tsaron Amurka a Afirka (AFRICOM), sun ƙaddamar da sabon hari akan 'yan ta'adda, inda suka yi nasarar halaka samar da mayaƙan ƙungiyar ISWAP guda 20 a Jihar Borno. Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ce harin ya auku ne a maɓoyar 'yan ta'adda da ke Metele a arewacin jihar, yankin da ke fama da hare-haren mayaƙan a 'yan shekarun baya-bayan nan. Manjo-Janar Samaila Uba, Daraktan yaɗa labaran hedikwatar, ya sanar da haka a wata takarda, ranar Litinin. A cewar hedikwatar, an ƙaddamar da harin ne bayan…
Read More

Ɗan Majalisar Wakilai mai ci na hannun daman Akume ya faɗi a zaɓen fidda gwanin APC a Benuwai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Lahadi Kwamitin Majalisar Dokoki ta Ƙasa akan shirya zaɓen fidda gwani a Jihar Benuwai, ya sanar da sakamakon zaɓen da aka gudanar a mazaɓun tarayya guda 11 na jihar. Acikin 10 na 'yan majalisa masu ci da suka shiga takarar, guda huɗu sun yi nasara a mazaɓunsu, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Waɗanda suka yi nasarar sun haɗa da Ojotu Ojeme na mazaɓar tarayya ta Apa/Agatu Cif Regina Akume ta Gboko/Tarka, Blessing Onuh ta Otukpo/Ohimini, da kuma Solomon Wombo na Katsina-Ala/Logo/Ukum. Ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Ado/Okpokwu/Ogbadibo, Philip Agbese, ya koma…
Read More