19
May
A bisa nagartar kishi da ƙwazon gina al’umma da Alhaji Abubakar Kabir Abubakar ya sa a gaba, ya sake zama halastaccen ɗantakar Majalisar Tarayya mai Wakiltar Karamar Hukumar Bichi, a yayin gudanar da zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar Majalisar Wakilai ta Tarayyar ƙasar nan, wanda Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranci gudanarwa a Asabar ɗin nan a garin Bichi. A lokacin kaddamar da ɗantakarar, Gwamna Abba Kabir Yusuf yana tare da wakilin Gwamnatin Tarayya kuma mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara a kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari da kuma wasu daga cikin ‘yan Majalisar Wakilan…
