Babaji

5689 Posts

Kano: Majalisar Dokoki ta goyi bayan komawar Gwamna Abba APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dokoki a Jihar Kano, ta bayyana goyon bayanta ga shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ficewa daga Jam'iyyar NNPP, tana mai kafa dalili da ƙamarin rikicin jagoranci da shari'o'i da ka iya shafar kujerun zaɓaɓɓun jami'ai. Da yake ganawa da manema labarai a Kano ranar Laraba, jagoran mafiya rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini, ya ce cigaba da zama acikin jam'iyyar ga gwamnan abu ne mai haɗari saboda rikice-rikicen da ba a warware su ba da shari'o'in da suke barazana ga halascin jam'iyyar. A cewarsa, rikicin cikin gida ya haifar da rashin tabbas ga…
Read More

APC a Ribas ta yi watsi da buƙatar tsige Gwamna Fubara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar APC reshen Jihar Ribas ta ƙi amince wa da shirin buƙatar tsigewa da Majalisar Dokokin jihar ta fara akan Gwamna Siminalayi Fubara da Mataimakiyarsa, Ngozi Odu, inda ta bayyana hakan a matsayin abin da ka iya "haddasa rikici kuma mara muhimmanci". A wata wasiƙa da Kakakinta, Darlington ya aike wa manema labarai a ranar Alhamis, APC ta ce tana sane da ikon da dokar ƙasa ta ba 'yan majalisa amma ba za ta goyi bayan abin da zai kai ga tsige gwamnan da ke ƙarƙashin inuwar APC ba. Jam'iyyar ta kuma ƙalubalanci mambobinta…
Read More

An gurfanar da soja bisa wadaƙar biliyan N22.8, kotu ta sake shi ba tare da hukunci ba, inji Femi Falana 

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Ƙwararren Lauya Mai Fafutukar neman 'yancin al'umma, Femi Falana a wata ƙasida, ya gabatar da misalin sakacin shara'a dangane da zargin cin hanci ko rashawa, inda aka zargi wani hafsan hafsoshi yayi ruf-da-ciki da kimanin  kuɗaɗe har Naira biliyan 22.8. Kamar yadda Falana ya zayyana, Babbar Kotun Tarayya Ta Sallame wannan hafsan bisa dalilin wai ba'a ma tuhume shi a  Kotun Soji ba, duk da cewar zargin yana da nasaba da zirga-zirga da maƙudan kuɗaɗe. Babbar Kotun ta sallami hafsan Soji bisa dalilin cewa ita ma Kotun dokar soji (martial court) bata tuhume shi kan…
Read More

Gwamnan Zamfara ya zargi Matawalle da amfani da ofishin Ribaɗu wajen garkuwa da jami’in gwamnati

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Zamfara ta koka game da zargin sace ɗaya daga cikin jami'anta a Abuja, inda ta zargi an yi amfani da jami'an tsaro na tarayya wajen cin mutunci da matsa wa 'yan ɓangaren adawa a jihar. Gwamnatin ta yi ikirarin jami'an tsaron birnin Abuja da ke aiki a ofishin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (ONSA) sun yi garkuwa da Salim Abubakar, wanda mataimakin harkokin gudanarwa ne na ofishin Gwamnan Zamfara, A wata takarda daga Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, gwamnatin ta ce al'amarin ya ƙara ƙarfafa damuwa akan yadda ake…
Read More

Zacch Adedeji: Tinubu ya jinjina wa shugaban NRS a ranar zagayowar haihuwarsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya taya Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta ƙasa NRS da aka fi sani da FIRS, Dakta Zacch Adedeji murna bisa zagayowar ranar haihuwarsa. Tinubu ya kuma jinjina wa ƙoƙarinsa na jagorancin hukumar, wadda tun tsawon shekaru 83 da suka gabata aka kafa ta, inda ya gabatar da sababbin shawarwari, bin salon da ake amfani da su a mataki na duniya cikin ayyukan hukumar, inganta tsare-tsarenta da inganta ma'aikatan domin amfanin ƙasa. A cewar shugaban ƙasar, shugaban na NRS ya cimma nasarar tara buƙatar kasafin ƙasa a zango na uku na 2025…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Dokokin Ribas na shirin tsige Gwamna Fubara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'amuran siyasa a Jihar Ribas da ke kudancin ƙasar nan na shirin ɗaukar wani salo, yayin da Majalisar Dokokin jihar ta fara shirye-shiryen tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Oduh. A yayin zaman na yau Alhamis ƙarƙashin jagorancin Kakakinta, Martins Amaewhule, majalisar ta bakin jagoran mafiya rinjaye, Major Jack, ta karanta wani saƙon gargaɗi da ke zargin gwamnan da saɓa wa ƙa'idojin aiki. Tuni 'yan majalisar guda 26 suka goyi bayan saƙon, inda suka yi ikirarin gwamnan ya aikata wasu laifuka da suka saɓa wa dokokin Nijeriya. Hon. Amaewhule ya bayyana cewa za…
Read More

Kotu ta umarci a ƙwace kadarori 57 da aka danganta da Malami na wucin-gadi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja ta umarci a karɓe kadarori guda 57 da aka yi zargin suna da alaƙa da tsohon Antoni-Janar kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami da 'ya'yansa biyu, wato Abdulaziz da Abiru-Rahman tare da damƙa wa Gwamnatin Tarayya. Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Laraba, inda ta ce tana kuma zargin an mallake su ne waɗanda suka haɗa da gidaje da filaye ta haramtattun hanyoyi. Mai shari'a Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin bayan lauyan hukumar EFCC, Ekele Iheanacho ya buƙaci hakan. A wata sanarwa da EFCC ta…
Read More

2027: Ministan Labarai ya dakatar da mai taimaka masa bayan musanta fitowa takarar gwamna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ministan Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Mohammed Idris, ya dakatar da ɗaya daga cikin mataimakansa mai suna Sa'idu Enagi bisa tsokacinsa na cewa akwai yiwuwar ministan ya tsaya takarar gwamna a Jihar Neja yayin zaɓen 2027. Mai taimaka wa ministan akan harkokin yaɗa labarai Rabi'u Ibrahim ne ya bayyana haka a wata takarda, inda ya kuma yi kira ga al'umma da su yi watsi batun, wanda a cewarsa, ba daga ministan ba ne. Mohammed Idris ya ce, a yanzu ya mayar da hankalinsa ne wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na…
Read More

Gwamnatin Tarayya ba ta watsar da ɗaliban Nijeriya a Moroko ba – Minista

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Tarayya ta ƙaryata rahotannin da ke yawo a wasu kafafen labarai game da ɗaliban da suka samu damar karatu kyauta a ƙasar Moroko, tana mai bayyana ikirarin a matsayin ƙarya mara tushe da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama'a. A wata sanarwa ta ranar Laraba daga Daraktar hulɗa da jama'ar Ma'aikatar Ilimi, Boriowo Folasade, Minista Dakta Tunji Alausa ya bayyana cewa, babu wani ɗalibin Nijeriya da ke ƙarƙashin halastaccen shirin karatu kyauta da aka yi watsi da shi. Ya ce, dukkan ɗaliban da ke cikin tsarin karatun da aka tantance su a…
Read More

An daƙile yunƙurin juyin mulki da kisan Shugaba Traoré a Burkina Faso

Hukumomin tsaro na ƙasar Burkina Faso sun ce ce sun gano tare da daƙile wani shirin juyin mulki da aka tsara don kashe shugaban sojin ƙasar, Kyaftin Ibrahim Traoré, da kawo rashin kwanciyar hankali a kasar a ƙarshen makon da ya gabata. Ministan tsaro ƙasar, Mahamadou Sana, ya bayyana hakan a cikin wani jawabi da ya yi a daren ranar Talata, inda ya nuna wani bidiyo da ke nuna yadda aka shirya kai hari ga shugaban kasar ko dai ta hanyar harbin shi kai tsaye ko kuma ta hanyar sanya bam a gidansa a daren 3 ga watan Janairu, kafin…
Read More