Babaji

5689 Posts

An fitar da abin da tattaunawar Jonathan da jagororin PDP ta ƙunsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan, ya bayyana gamsuwa da cewa babbar jam'iyyar adawa (PDP) tana nan da kwarjini da ƙarfinta saɓanin jita-jitar wasu gidajen jaridu, yana ma cewa har yanzu ita ce ginshiƙin dimukraɗiyyar Nijeriya, wadda ta rage daga jam'iyyun da aka kafa a 1998. Jonathan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin mambobin kwamitin gudanarwar (NWC) jam'iyyar na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Dakta Kabiru Tanimu Turaki a ofishinsa da ke Abuja a yammacin Talata. A yayin ganawar, an mayar da hankali ne wajen hanyoyin da suka dace a bi don…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta bada belin Malami, matarsa da ɗansa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotun Tarayya da ke abin, ta bada belin Naira biliyan 1.5 akan tsohon Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, matarsa, Asabe Bashir da ɗansa, Abdulaziz Malami. A shari'ar da ta yi a yau Laraba ƙarƙashin jagorancin Alƙali Emeka Nwite, kotun ta bada belin kowane ɗaya daga cikinsu ne akan Naira miliyan 5 bayan Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) ta shigar da su ƙara na zargin su da hannu a sauya akalar Naira miliyan 8.7. Mai Shari'ar ya kuma sanya musu sharaɗin samar da mutane biyu-biyu a…
Read More

Kotu ta soke rushe jagororin NNPP a Kano, ta jaddada halascin ‘yan ɓangaren Gwamna Abba

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotu a Kano ta soke hukuncin rushe majalisun zartarwar NNPP a matakin jiha, ƙananan hukumomi da gundumomi daga ɓangaren kwamitin ayyukan na ƙasa (NWC) na jam'iyyar. A wani hukunci da Mai Shari'a Nasiru Saminu ya yi a ranar Talata, kotun ta kuma haramta wa kwamitin ɗaukar wani mataki akan tsarin shugabancin jam'iyyar a Kano har sai an gudanar da shari'ar ƙarar da aka shigar akan al'amarin. Wani mai suna Abdullahi Zubairu Imam da wasu mutane biyar ne suka shigar da ƙarar a madadin kwamitin zartarwar NNPP na ƙananan hukumomi 44 na jihar…
Read More

Tinubu ya naɗa mace ta farko a shugabancin Makarantar Lauyoyi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Dakta Olugbemisola Titilayo Odusote a matsayin darakta-janar ta Makarantar Horar da Lauyoyi ta ƙasa. Naɗin nata zai fara aiki ne daga ranar 10 ga watan Junairu, 2026, inda za ta shafe tsawon shekaru huɗu a muƙamin. Dakta Titilayo Odusote mai shekaru 57, ita ce mataimakiyar shugaban makarantar, wadda kuma za ta maye gurbin Farfesa Isa Hayatu Chiroma da zai kammala wa'adinsa a ranar 9 ga Janairu. Haka kuma, ita ce mace ta farko da za ta jagoranci makarantar tun bayan buɗe ta a shekarar 1962. Ta kammala…
Read More

Neja: Al’umma sun shiga firgici bayan gano kan makami mai linzami na Amurka a wani ƙauye

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mazauna yankin Zugurma a Ƙaramar Hukumar Mashegu ta Jihar Neja sun shigar firgici a yau Litinin bayan gano wani abu mai kama da kan makami mai linzami a wani juji da ke kusa da su, lamarin da ya sa jami'an tsaro suka gaggauta kai ɗauki. A cewar majiyoyi daga yankin, 'yan ƙauyen ne suka ga baƙon abin a lokacin da suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum. Ganin haka ya sa suka hanzarta sanar da jami'an tsaro domin ɗaukar matakin gaggawa. Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewa ana zargin abin…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Chelsea ta naɗa sabon koci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta naɗa Liam Rosenior a matsayin sabon mai horar da 'yan wasanta, inda ta ba shi kwantiragin shekaru shida. A sanarwar da ta fitar, Chelsea ta ce za ta cigaba da mayar da hankali akan inganta 'yan wasa, yayin da take fatan cimma manyan burikanta. A nasa ɓangaren, Rosenior ya bayyana alfaharinsa ga samun muƙamin wanda ya bayan a matsayin babban dama ga zangonsa na horarwa. Ya ce, zai yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ƙungiyar ta cimma nasarori a yayin zamansa a muƙamin. Tsohon ɗan wasan bayan ya…
Read More

Dakarun tsaro sun ceto tsohon soja daga hannun ‘yan bindiga a Filato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jami'an Rundunar Sojoji ƙarƙashin sashen 3 da Operation Enduring Peace, sun yi nasarar ceto wani kanal mai ritaya mai suna Ajanaku daga komar 'yan bindiga a Ƙaramar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato. A cewar masanin harkar tsaro, Zagazola Makama, an tsohon jami'in sojan ne a yankin Rafiki da ke ƙaramar hukumar, bayan bin diddigin 'yan bindigar a Wildlife Park, wajen da suke bi su tsere. Rundunar sojin ta tabbatar da cewa an samu nasarar ceton ne bayan haɗin-gwiwa da kuma gaggawar ɗaukar mataki daga jami’an tsaro, inda suka bi sawun masu aikata laifin…
Read More

Yahaya Bello ya cancanci a ba shi dama a kujerar sanatan Kogi ta Tsakiya, inji VeryDarkMan

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanannen tauraron Soshiyal Mediya, Martins Vincent Otse da aka fi sani da VeryDarkMan ya janyo ce-ce-ku-ce bayan ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga tsohon gwamnan Jihar Kogi na tsayawa takarar sanatan Kogi ta Tsakiya a zaɓen 2027 da ke tafe. A ranar 30 ga watan Disamba tsohon gwamnan ya bayyana muradinsa na tsayawa takarar kujerar sanata, a lokacin da ya ziyarci Fadar Ohinoyi na Masarautar Ebira. A nan ne ya gabatar da jawabi ga sarakunan gargajiya, jagororin addini da sauran masu ruwa da tsaki na mazaɓar sanatan, inda ya ce ya karɓi…
Read More

Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 32 bayan halaka biyu a Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Aƙalla mutane 32 ne 'yan bindiga suka yi awon-gaba da su ciki har da tsohuwa da ƙananan yara bayan sun halaka wasu guda biyu a Jihar Kaduna. A cewar SaharaReporters, an sace tsohuwar ne ƙasa da kwana biyu da halaka babban ɗanta da wani a Ƙauyen Arak da ke Ƙaramar Hukumar Sanga. Matar mai suna Misis Averik Arak, an sace ta ne tare da jikarta bayan halaka baban jikar mai suna Habila Averik a ranar Lahadi. An ruwaito cewa, dattijuwar ta shiga halin rashin lafiya sakamakon kashe ɗanta a kan idonta tare da mata…
Read More

‘A ci daɗi lafiya – Kwankwaso ya nemi Abba ya ajiye kujerar gwamna kafin koma wa APC

' Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya aike da saƙon gargaɗi ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ya nemi da ya sauka a kujerarsa matuƙar ya nufi ficewa daga jam'iyyar NNPP. Kwankwaso ya bayyana haka yayin jawabi a wani taron magoya bayansa da masu ruwa da tsaki na NNPP yayin ake tsaka da yaɗa jita-jitar gwamnatin NNPP da ke mulki a jihar na shirin haɗewa da jam'iyyar APC. Da yake jawabi cikin kakkausan murya, tsohon gwamnan ya ƙalubalen dalilin da ya sa ake neman ɗauke gwamnan daga…
Read More