Babaji

5689 Posts

Badaƙalar kuɗaɗe: Kotu ta saka ranar sauraron neman belin Malami, ɗansa da matarsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Juma'a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage shari'ar neman bada belin tsohon Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari'a Abubakar Malami, ɗansa da kuma matarsa, wato Bashir Asabe. Alƙalin da ke hukunci akan ƙarar, Mai Shari'a Emeka Nwite ya ayyana ranar 7 ga watan Junairu, 2026 a matsayin lokacin hukuncin akan buƙatar belin mutane ukun. Alƙali Nwite ya sanya ranar ne bayan lauyoyin ɓangarorin biyu na masu ƙara da kuma na Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, sun gabatar da hujjoji da takardunsu a gaban kotu. EFCC na…
Read More

Bichi: Sarkin Kano ya nemi sabon Dagacin Hagawa ya kiyaye adalci

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na II ya ja hankalin Sabon Dagacin garin Hagawa, Malam Mansur Abdur-Rahman na Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano, akan ya zamo mai adalci da riƙon amana a wajen jagorantar al'ummarsa. Sarkin ya bayyana haka ne a anar Talata jim-kaɗan bayan da aka nada sabon dagacin a Fadar sarkin. Mai Maraba Sanusi na II ya gargaɗe shi game da haɗa kai da azzaluman mutane masu cutar da al'uma ta kowace siga. Ya tabbatar masa da cewa wannan nauyi ne da Allah (SWT) ya dora masa. Ya kuma shawarce shi da bude zauren…
Read More

Peter Obi ya koma ADC a hukumance

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar LP tare da komawa jam’iyyar ADC. Obi ya bayyana hakan ne yayin wani taron siyasa, inda ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na sabon tsari da hangen nesa na ceto da gyara siyasar Najeriya, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen shekarar 2027. A cewarsa, ya ɗauki matakin ne bayan dogon nazari, yana mai jaddada cewa burinsa shi ne gina adalci, shugabanci nagari da tsarin siyasa mai amfani ga talakawan Nijeriya. Wannan ci-gaba ya haddasa cece-kuce a faɗin ƙasar nan, inda magoya bayansa ke…
Read More

Borno: Sojoji sun kama ɗan ƙunar baƙin-wake, sun ƙwato sinadaran bom

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun atisayen HAƊIN KAI na rundunar sojin Nijeriya a Jihar Borno, sun yi nasarar cafke wani da ake zargin ɗan ƙunar baƙin-wake ne mai suna Abubakar Mustapha da wasu ababen haɗa boma-bomai. Kakakin jami'an haɗaka na JTF na rukunin a Arewa ta Gabas, Laftanal Sani Uba ya bayyana haka a wata takarda, ranar Talata. A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne tun a ranar Litinin a ƙarƙashin jagorancin atisayen runduna ta 152 ta Bataliyar Task Force da haɗin-gwiwar sauran jami'an hukumomin tsaro a Ƙaramar Hukumar Bama da ke arewacin jihar. Ya bayyana cewa,…
Read More

Jita-jitar sauya sheƙar wasu mambobinmu ba gaskiya ba ne – NNPP

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar NNPP a Kano, ta yi watsi da ikirarin cewa wasu daga cikin mambobinta na shirin ficewa daga jam'iyyar da nufin sauya sheƙa zuwa APC mai mulki, tana mai cewa babu goyon baya akan haka a matakin jihar ko jagorancinta na ƙasa. Shugaban NNPP na jihar, Hashim Sulaiman Dungurawa yayin ganawa da manema labarai ranar Litinin a Kano, ya ce kan ƴaƴan jam'iyyar har yanzu a haɗe yake wajen cimma manufofinsu na siyasa a jihar da ma Nijeriya baki ɗaya. Ya bayyana cewa, jam'iyyar ta mayar da hankali wajen shugabancin damawa da jama'a musamman…
Read More

Gaboara ce ta tashi a Babban Asibitin Kebbi ba Bom ba, inji gwamnati

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Kebbi ta yi bayanin haƙiƙanin abin da ya faru a Babban Asibitin Bagudo a safiyar yau Talata. A wata sanarwa daga mai ba Gwamna Nasir Idris Shawara akan Harkar Labarai, Yahaya Sarki, gwamnatin ta ce fashewar ta faru ne sakamakon gobara ba fashewar bom ba kamar yadda aka yi tunani da fari. Ya bayyana cewa, Sakataren Gwamnatin (SSG), Yakubu Balance Tafida ne ya faɗi haka a yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce binciken farko da rahotanni daga hukumomin tsaro sun nuna cewa fashewar mai ƙarfi ta samo asali ne daga…
Read More

MOPPAN ta jinjina wa Kabir Jammaje bisa samar wa mambobinta fagen karatu kyauta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta ƙasa (MOPPAN) da ɗaukacin ƴan masana'antar Kannywood, sun yaba wa Malam Kabir Musa Jammaje bisa samar da shirin bada ilimin kararun darasin Turanci a kyauta ga mambobinsu. MOPPAN ta ce, ƙoƙarinsa na inganta jaruman harkar fim, daraktoci, jami'an shirya fim da sauransu a masana'antar, abu ne da zai taimaka wajen bunƙasa harkokinsu. A wata takarda da Kakakin ƙungiyar, Ibrahim Amarawa ya fitar, MOPPAN ta bayyana cewa a wannan zamani na ci-gaba, ƙwarewa a yaren Turanci ba iya nagarta ba ce, abu ne da zai buɗe ƙofar wasu damarmakin wajen…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta tasa ƙeyar Malami da ɗansa zuwa kurkukun Kuje

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja, ta umarci a tsare Abubakar Malami, wato tsohon Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari'a a gidan yarin Kuje har zuwa lokacin da za ta sake sauraron ƙarar da aka shigar akansa da neman bada belinsa. Alƙali Emeka Nwite yayin hukuncin, ya kuma umarci a tsare ɗan Malami, Abdulaziz da, kuma matarsa Bashir Asabe har zuwa lokacin da za a bada belinsu. An gurfanar da mutane ukun ne bisa zargin su da hannu a laifuka guda 16 masu alaƙa da badaƙalar kuɗaɗe a yau Talata. Baki…
Read More

FRSC ta bayyana musabbabin hatsarin da ya rutsa da Anthony Joshua

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta ce gudu sama da kima da kuskuren kere ne suka yi sanadiyyar hatsarin da ya rutsa da zakara damben duniya, Anthony Joshua. A jiya Litinin Joshua ya haɗu da iftila'in a kusa da Shagamu, Jihar Ogun, inda abokanansa biyu da suka zo daga Ingila suka rasa rayukansu. An ga wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta da ke nuna yadda Joshua ya jikkata bayan faruwar al'amarin. A sanarwar da babban jami'in hulɗa da jama'a da wayar da kai na FRSC, Olusegun Ogungbemide ya fitar, ya…
Read More

INEC ta soke PDP a jaddawalin ƴan takarar gwamnan Ekiti kan shari’o’i

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta fitar jaddawalin ƴan takarar gwamnan Jihar Ekiti da mataimakansu yayin shirye-shiryen zaɓen, wanda za a gudanar a ranar 20 ga watan Yuni, 2026, inda aka ga babu suna babbar jam'iyyar adama (PDP) a ciki. An ga cewa babu sunan ɗan takarar PDP, Dakta Wole Oluyede, da mataimakinsa, inda ta wallafa jerin sunayen ƴan takarar daga jam’iyyu 12 da za su fafata a kujerar gwamnan jihar a ofishinta da ke titin New Iyin Road, Ado-Ekiti, ranar Litinin. Jerin sunayen ya nuna cewa jam’iyyar APC na sake tsayar da gwamna…
Read More