30
Dec
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta fitar jaddawalin ƴan takarar gwamnan Jihar Ekiti da mataimakansu yayin shirye-shiryen zaɓen, wanda za a gudanar a ranar 20 ga watan Yuni, 2026, inda aka ga babu suna babbar jam'iyyar adama (PDP) a ciki. An ga cewa babu sunan ɗan takarar PDP, Dakta Wole Oluyede, da mataimakinsa, inda ta wallafa jerin sunayen ƴan takarar daga jam’iyyu 12 da za su fafata a kujerar gwamnan jihar a ofishinta da ke titin New Iyin Road, Ado-Ekiti, ranar Litinin. Jerin sunayen ya nuna cewa jam’iyyar APC na sake tsayar da gwamna…
