Babaji

5690 Posts

Zamfara: ‘Yan sanda sun daƙile harin ƴan bindiga a Ƙaramar Hukumar Maru

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar ƴan sanda a Jihar Zamfara ta ce jami'anta sun yi nasarar daƙile wani mummunan farmakin ƴan bindiga a Garin Maru da ke Ƙaramar Hukumar Marun Jihar Zamfara a safiyar ranar Lahadi. Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar a wata sanarwa, ya bayyana cewa haɗakar jami'an hukumomin tsaro ne suka gaggauta yin gaba-da-gaba da maharan, lamarin da ya tilasta musu ja da baya bayan samun munanan raunuka na harbin bindigu. Ya ce, babu wani daga cikin jami'an da ya samu rauni ko yin awon-gaba da wasu daga maharan a yayin fafatawar kasancewar an ƙarfafa jami'ai…
Read More

Kano: ‘Yan bindiga tara da ɗan bijilante sun rasu yayin arangama da sojoji a Shanono

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani ba-takashi da aka yi tsakanin ƴan bindiga da sojoji a Bakaji da Unguwar Garma na Goron Dutsen Ƙaramar Hukumar Shanono ya yi sanadiyyar halaka ƴan ta'adda guda tara da ɗan bijilante ɗaya yayin da kuma wani guda ya samu rauni. Tun da misalin ƙarfe 12 na daren ranar Lahadi ne ƴan bindigar cikin adadi mai yawa ɗauke da muggan makamai suka kai farmaki a yankin. An gano cewa sojojin sun daƙile shirin nasu ne a lokacin da suka yi arangama da su a wani yanki na shiga garin, inda suka ɗauki tsawon sa'o'i…
Read More

Yanzu-yanzu: Tinubu ya tafi Turai hutun ƙarshen shekara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Lahadi ne Shugaba Bola Tinubu ya bar Jihar Legas inda ya tafi Nahiyar Turai domin cigaba da hutunsa na ƙarshen shekara. A sanarwar da Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaban zai kuma kai ziyara a hukumance zuwa Abu Dhabi, babban birnin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE). Ya ce, Shugaban UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan ne ya gayyaci Tinubu domin halartar wani taro na mako ɗaya kan ɗorewar ci-gaba na 2026, wanda za a gudanar a farkon Janairun 2026. Onanuga ya kuma ce, taron na tsawon mako ɗaya,…
Read More

Nijeriya ta yi watsi da kafa Ƙasar Somaliland da Isra’ila ta amince

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Amurka ta fara ayyukan tattara bayanan sirri da na bincike ta sama a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya, inda take sanya ido kan ƴan ta'adda a dajin Sambisa, bayan hare-hare ta sama da ta kai a daren Alhamis akan mayaƙan ISIS a Jihar Sokoto. Brant Philip, wanda masanin tsaro ne kuma mai bibiyar ayyukan ta’addanci a yankin Sahel, ya bayyana hakan a ranar Asabar, inda ya wallafa bayanan bibiyar jiragen sama da ke nuna wani jirgin Amurka yana shawagi a sararin samaniyar Jihar Borno. Bayanan sun nuna cewa jirgin da aka yi amfani da…
Read More

Bayan harin Sokoto Amurka ta koma sintirin leƙen asiri ta jiragen sama a Sambisa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Nijeriya ta yi ƙi amincewa da ayyana ƙasar Somaliland a matsayin yanki mai cikakken ƴanci daga ƙasar Somaliya da Isra'ila ta yi a kwanan nan, inda Nijeriyar ta bayyana hakan a matsayin yunƙurin barazana ga ikon Somaliya da yiwuwar aukuwar rashin zaman lafiya a ƙasar. A wata takarda da Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Nijeriya, Kimiebi Ebienfa ya fitar a jiya Asabar, Gwamnatin Tarayya ta ce za a ta cigaba da ƙoƙarin kiyaye sharuɗɗan iko, iyakance guraben iko da kuma ƴancin siyasa kamar yadda sashen Majalisar Ɗinkin Duniya na 'Charter of the United Nations'…
Read More

Auren Sakataren gwamnati Akume da tsohuwar matar Oonin ife Zaynab ya tada hazo

Auren Sakataren gwamnati Akume da tsohuwar matar Oonin ife Zaynab ya tada hazo Daga BELLO A. BABAJI aa Abuja Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume ya auri Zaynab Ngohemba, wadda ita ce tsohuwar matar Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, lamarin da ke nuna samun ƙaruwa ta musamman ga ɗaya daga cikin manyan jami'an gwamnati. Rahoto sun bayyana cewa an sanar da al'amarin ne a ranar Juma’a ta hannun ɗaya daga cikin mambobin iyalan Dajoh, Abraham Double-d Dajoh, ta shafin Facebook. Iyalan Dajoh sun tabbatar da auren tare da tarbar Sarauniya Zaynab a hukumance zuwa gidan iyali da…
Read More

Aiwatar da sabuwar dokar haraji a 1 ga Junairu na bisa tsari, inji Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa kuma Shugaban kwamitin Shugaban Ƙasa akan lamuran kasafi da gyare-gyaren haraji, Taiwo Oyedele ya ce ranar ɗaya da ga watan Junairun 2026 da aka ayyana aiwatar da sabuwar dokar haraji tana nan daram. Oyedele ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a Legas yayin ganawa da manema labarai bayan wata ganawa ta musamman da Shugaba Bola Tinubu. Ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya ba za ta ja da baya ko sassauta matsayinta ba wajen aiwatar da sabuwar dokar haraji da aka tsara fara aiki da ita a farkon watan Janairun…
Read More

Harin Amurka a Sakkwato bai da wani tasiri – Masanin tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sanannen masanin harkar tsaro, Zagazola Makama ya bayyana cewa tarin hare-haren da Amurka ta ƙaddamar a Jihar Sakkwato kuskure ne na abin da aka nufa. Makama ya faɗi hakan ne yayin da yake tsokaci akan harin da sojojin Amurka suka kai a daren Kirsimeti, inda aka ce an kai harin ne kan ƴan ta’adda, abin da ya jefa al’ummar jihar cikin fargaba da tashin hankali. A wani faifan bidiyo an ga yadda mazauna ƙauyen Jabo da ke Ƙaramar Hukumar Tambuwal suka shiga halin firgici bayan ɗaya daga cikin ababen hare-haren ya sauka a yankinsu…
Read More

Rashin tsaro: Sababbin dabaru za su samar da sakamakon da ake buƙata, inji Tinubu

Shugaba Bola Tinubu na ya tabbatar wa al'ummar Nijeriya cewa sababbin hanyoyin da ake ɗauka don magance matsalar tsaron ƙasar za su samar da nasara nan ba da jimawa ba. Shugaban ya bayyana haka ne yayin karɓar baƙuncin Ƙungiyar Kiristoci ta ƙasa (CAN), ƙarƙashin jagorancin Shugabanta Archbishop Daniel Okoh, a gidansa da ke Legas, ranar Juma'a. Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Oyanuga ne ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar. Tinubu ya bayyana cewa a shirye gwamnatinsa take wajen ƙirƙiro da ƴan sandan jihohi domin inganta tsarin tsaron ƙasar. Ya yi kira ga CAN da ta yi aiki da…
Read More

Bom ɗin jami’an tsaro ya tarwatsa wani gida bisa kure a Kwara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta ya nuna yadda wani gini a garin Offa na Jihar Kwara ya tarwatse sakamakon fashewar wani bom bisa kure. Hakan ya faru ne sa'o'i bayan Shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da cewa sojojinsu sun kai farmaki akan sansanonin ƴan ta'addar ISIS a Jihar Sakkwato. Mazauna sun tabbatar da cewa sun jiyo ƙararraki bayan wani bom da aka jefo ya faɗi a wani gida, kamar yadda suka shaida a bidiyon. Saidai a yayin haɗa wannan rahoton, hukumomi ba su tabbatar da ko hakan na…
Read More