26
Dec
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da haɗin-gwiwar tsaro da leƙen asiri tsakanin Nijeriya da Amurka biyo bayan harin maɓoyar ƴan ta'adda a yankin Arewa maso yammacin Nijeriya da Amurka ta kai a yankin jihar Sakkwato a daren Juma'a. A cewar Ma’aikatar Harkokin Waje wannan mataki ya haifar da samun ƙarin nasarori a yunkurin kai hare-haren jiragen sama da suka yi a wasu sansanonin ƴan ta’adda a yankin. A wata sanarwa da Kakakin Ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya fitar a yau Juma'a, an bayyana cewa haɗin-gwiwar tsaron ya ƙunshi musayar bayanan sirri, dabarun tsaro, da sauran…
