Babaji

5690 Posts

PDP ta sake shiga tsaka mai wuya bayan INEC ta ƙi karɓar sabbin shugabanninta kan hukuncin kotu

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ba za ta amince da Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar PDP da Kabiru Turaki ke jagoranta ba, saboda hukuncin kotuna da har yanzu suke aiki da kuma shari’o’in da ba a kammala ba. INEC ta ce ta karɓi buƙatu daga lauyoyin PDP na neman a amince da shugabannin ƙasa da aka ce an zaɓa a Babban Taron Jam’iyyar da aka gudanar a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, 2025, a Ibadan, Jihar Oyo. Sai dai bayan duba buƙatun, hukumar ta yanke shawarar ƙin amincewa da su bisa doka da hukuncin…
Read More

AFCON 2025: Super Eagles ta fara da ƙafar dama bayan doke Tanzaniya a rukunin C

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Super Eagles ta Nijeriya ta bi sawun sauran manyan ƙasashe wajen fara gasar AFCON da ƙafar dama sakamakon doke Tanzaniya a wasanta na farko da ci 2 da 1. 'Yan wasa Semi Ajayi da Ademola Lookman ne suka zura wa Super Eagles ƙwallayen da suka ba tawagar Nijeriyar nasara. Da fari, ɗan wasa Alex Iwobi ne ya yi bugun tazara daga gefen fili, wands hakan ya ba Semi Ajayi damar zura ƙwallon farko a wasan. Tanzaniya ta samu damar farkewa ne yayin da aka dawo hutun rabin lokaci da mintuna biyar ta hannun ɗan…
Read More

Za ku ɗanɗana kuɗarku idan kuka ci gaba da addabar mutane – Gwamnatin Tarayya ga ‘yan ta’adda

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ayyana masu garkuwa da mutane, ƙungiyoyin da ke ɗaukar makamai ba bisa ƙa’ida ba, da kuma masu tayar da hankalin al’umma a matsayin ƴan ta’adda, a wani muhimmin mataki na ƙarfafa yaƙi da matsalar tsaro da ke addabar ƙasar nan. Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ya bayyana haka a ranar Litinin yayin jawabin ƙarshen shekara ga manema labarai a Abuja. Wannan mataki na gwamnati na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da ƙarewa satar mutane, hare-haren ‘yan bindiga da kuma tayar da zaune tsaye a sassa daban-daban na ƙasar.…
Read More

Iliyasu Kwankwaso ya yaba wa Tinubu akan hana karkatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗaya daga cikin jiga-jigan ƴaƴan Jam'iyyar APC a Jihar Kano, Dakta Musa Iliyasu Kwankwaso, ya bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu akan dagewarsa kan lallai sai ƙananan hukumomin jihohi sun samu ƴancin karɓar kuɗaɗensu kai tsaye daga Gwamnatin Tarraya. Ya ce, hakan biyayya ce ga doka saɓanin zargin cimma burin siyasa. Musa Iliyasu Kwankwaso wanda a yanzu shine Babban Daraktan Kudi a Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama'are, ya jaddada cewa bai wa ƙananan hukumomi damar cin gashin kansu ginshiƙi ne na samar da ci-gaba daga ƙasa kuma zai samar da daidaito a…
Read More

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Tarayya ta fara ganowa da goge shafukan sada zumunta da ƴan ta’adda ke amfani da su

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ce hukumomin tsaron Nijeriya suna aiki da kamfanonin kafafen sada zumunta domin ganowa da kuma soke shafukan da ƴan ta'adda da ƙungiyoyinsu ke amfani da su wajen tallata ayyukansu da tara kuɗaɗe. Da yake jawabi yayin isar da saƙon ƙarshen shekara a Abuja ranar Talata, Darakta Janar na Cibiyar yaƙi da ayyukan ta'addanci, Manjo Janar Adamu Laka, ya ce kafofi irin su TikTok, Facebook, Instagram, Snapchat da X ƴan ta'adda suke amfani da su wajen yaɗa manufofinsu da ayyukansu gami hulɗa da masu taimaka musu. Ya ce, hukumomin tsaro sun yi…
Read More

Legas: DSS sun kama waɗanda ake zargi ƴan ISWAP ne a Apapa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumomin tsaro sun yi nasarar cafke waɗansu mutane biyu da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne a Jihar Legas, lamarin da ya sake tayar da hankula kan yiwuwar faɗaɗar ayyukan ta’addanci zuwa kudancin Najeriya daga Arewa maso Gabas. Rahotanni sun bayyana cewa, jami'an Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS) ne suka kama wani mai suna Modu Gana da Ibrahim Dugge a safiyar ranar Lahadi a garin Apapa, inda kuma tuni suka garzaya da su ofishinsu domin gudanar da bincike akansu. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa, atisayen ya samo asali ne daga sahihan bayanan sirri,…
Read More

Ƙungiyoyin agaji sun yaba wa Gwamnatin Kaduna kan gyaran cibiyoyin lafiya a jihar

Haɗakar ƙungiyoyin agaji da ƙungiyoyin fararen hula tare da shugabannin addini, sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin kafafen yaɗa labarai sun yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna bisa nasarar gyaran daukacin cibiyoyin Lafiya na Matakin Farko (PHC) a faɗin jihar. Haɗakar ta kai ziyarar tantancewa zuwa wasu zaɓaɓɓun cibiyoyin Kula da lafiya domin nuna godiya ga Gwamnatin Jihar Kaduna da Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar bisa gyaran cibiyoyin Kula da lafiya guda 255 a cikin ƙananan hukumomi 23 na jihar. Manufar ziyarar ita ce tantance tasirin sauye-sauyen da ake aiwatarwa a ɓangaren lafiya a matakin ƙasa-ƙasa da kuma yadda hakan…
Read More

Ofishin jakadancin Amurka zai daina ba ƴan Nijeriya biza daga 1 ga Junairun 2026

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Amurka ta ce za ta dakatar da bada wasu nau'ukan bizozin shiga ƙasar ga ƴan Nijeriya daga ranar 1 ga watan Junairu, 2026 biyo bayan sabon matakin da fadar shugaban ƙasar ta ɗauka akan tsaron iyakoki da ƙasa. A ranar Litinin ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya sanar da cewa matakin zai fara aiki ne daga ƙarfe 12:01 na dare, kamar yadda fadar White House ta bayyana. Sanarwar ta ce, Nijeriya tana ɗaya daga cikin ƙasashe guda 19 da sabon tsarin ya shafa. Sauran sun haɗa da Angola, Antigua da Barbuda, Benin, Burundi,…
Read More

Ɗangote ya yi barazanar shigar da ƙarar biliyan N100 akan ɗan kasuwar Kaduna kan zargin ƙazafi

Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya yi barazanar shigar da ƙarar cin mutunci ta kuɗi har biliyan N100 akan wani ɗan kasuwa da ke Jihar Kaduna mai suna Injiniya Kailani Mohammed, bisa zargin sa da ɓata masa suna da yin kalaman batanci a bainar jama’a. Ɗangote ya bada wa’adin kwanaki bakwai ga Injiniyan da ya janye kalaman nasa tare da bayar da cikakken bayani da kuma neman afuwa a fili, ko kuma ya fuskanci matakin shari’a. Hakan na kunshe ne a wata takarda da lauyan Ɗangoten, Dakta Ogwu James Onoja, SAN, na kamfanin Onoja Law Firm da ke…
Read More

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya 28 ciki har da yara a Filato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'umma a garin Zak da ke Gundumar Bashar ta Ƙaramar Hukumar Wasen Jihar Filato sun shiga damuwa da tashin hankali a sakamakon garkuwa da kimanin matafiya 28 da wasu ƴan bindiga suka yi a daren ranar Lahadi wayewar Litinin. Waɗanda aka sacen sun haɗa da maza, mata da kuma yara, inda al'amarin ya rutsa da su a lokacin da suka taho daga Ƙauyen Zak zuwa Sabon Layi domin halartar taron Maulidi. Da yake tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho ga manema labarai, wani shugaban matasa a Wase mai suna Shafi'i Sambo, ya ce…
Read More