Babaji

5691 Posts

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya 28 ciki har da yara a Filato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'umma a garin Zak da ke Gundumar Bashar ta Ƙaramar Hukumar Wasen Jihar Filato sun shiga damuwa da tashin hankali a sakamakon garkuwa da kimanin matafiya 28 da wasu ƴan bindiga suka yi a daren ranar Lahadi wayewar Litinin. Waɗanda aka sacen sun haɗa da maza, mata da kuma yara, inda al'amarin ya rutsa da su a lokacin da suka taho daga Ƙauyen Zak zuwa Sabon Layi domin halartar taron Maulidi. Da yake tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho ga manema labarai, wani shugaban matasa a Wase mai suna Shafi'i Sambo, ya ce…
Read More

Gwamnatin Tarayya za ta fara gwajin ƙwaya ga masu neman aikin gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta ce ta amince da shirin gwajin ƙwaya ga masu neman aikin gwamnati a faɗin Nijeriya, inda ta ce daga yanzu za a saka gwajin ta'ammali da ƙwaya a cikin abubuwan da suka zama wajibai kafin a ɗauki mutum aiki a ƙasar. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya, Segun Imohiosen ya fitar a madadin gwamnatin. Ya ce, "don haka ana umartar dukkan manyan sakatarori da shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya a ƙasar da su saka gwajin ƙwaya a cikin abubuwan da ake buƙata kafin samun aikin gwamnati." Sanarwar…
Read More

Trump ya yi wa jakadan Amurka a Nijeriya da wasu ƙasashe 29 kiranye

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta Amurka ta sauke Jakadan ƙasar a Nijeriya, wato Richard Mills, tare da wasu jakadun ƙasashe guda 29 a duniya, a wani ɓangare na sabon tsarin sake fasalin ofisoshin jakadancin ƙasar. Blueprint ta ruwaito cewa, ƙasashe 13 na Nahiyar Afirka na daga cikin waɗanda hukuncin ya shafa yayin da Amurka da ɗauki ɗamarar sauya tsarin difulomasiyyarta a ƙasashen waje. Wannan mataki na cikin shirin Shugaba Trump na tabbatar da manufarsa ta bai wa Amurka fifiko a harkokin difulomasiyya da ƙasashen waje. Bisa bayanan jami’an Ma’aikatar Harkokin Waje, waɗanda suka nemi…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Tarayya ta bada hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun 25 da 26 ga watan Disambar 2025 da kuma 1 ga watan Junairun 2026 a matsayin lokacin hutun bikin Kirsimeti, ranar boksin da kuma murnar shiga sabuwar shekara. Babbar Sakatariyar Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, Dakta Magdalene Ajani ta bayyana haka a wata takarda, yau Litinin. Ta ce, Ministan ma'aikatar, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya sanar da haka a madadin Gwamnatin Tarayyar. Ya yi kira ga al'umma da su yi amfani da lokacin wajen ƙarfafa soyayya, zaman lafiya, tausayi da sadaukarwa a tsakaninsu yayin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa…
Read More

Sauran ɗaliban makarantar Neja da aka sace sun shaƙi iskar ƴanci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Alamu sun bayyana cewa sauran ɗaliban makarantar St. Mary's Catholic School, Papiri da ke Ƙaramar Hukumar Rafi ta Jihar Neja sun shaƙi iskar ƴanci bayan shafe tsawon makonni a komar ƴan bindigar da suka yi awon-gaba da su. Hakan na zuwa ne bayan da iyayen yaran suka koka wa gwamnatocin tarayya da ta jihar akan a yi ƙoƙarin ceto yaran gabanin bikin Kirsimeti. Zuwa yanzu dai sauran ɗalibai guda 130 na makarantar da ke hannun ƴan bindiga sun kuɓuta, inda jimillar adadinsu ya kai 230. Yanzu dai za a iya cewa babu sauran ɗaliban…
Read More

ICPC ta gayyaci Ɗangote kan zargin tsohon shugaban NMDPRA da hannu a rashawa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Yaƙi da Cin hanci da Rashawa (ICPC), ta gayyaci Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote domin fara bincike akan zargin da ya yi wa tsohon shugaban hukumar kula da harkokin man fetur ta ƙasa (NMDPRA), Farouk Ahmed. Majiyoyi na kusa da al'amarin sun tabbatar da cewa an gayyaci Ɗangote zuwa ofishin hukumar ne inda aka nemi ya je a gobe Litinin ko kuma ya wakilta Lauyansa, wato Ogwu Onoja (SAN) yayin da hukumar ta fara gudanar da cikakken bincike akan ƙorafin nasa. Ɗangote ya zargi Farouk Ahmed ne da aikata cin hanci…
Read More

Tinubu ba shi da tsara a zaɓen 2027, inji Shettima

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Juma'a Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya ce, babu wanda zai yi yunƙurin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 sai 'ɗan ta-kife ko ɗan basaja' da an san ba zai kai labari ba. Shettima ya bayyana haka ne a taron Kwamitin Zartarwar Jam'iyyar APC karo na 15 a babban ɗakin taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. A cewarsa, ba a cin zaɓe ta kafar Soshiyal Mediya ko kuma kafafe irin su Twitter wanda a yanzu ya zama X, inda za a yi ta kumfar baki wajen kururuta abin da…
Read More

Tinubu ya sauya sunan Jami’ar Kimiyya ta Azare zuwa Sheikh Ɗahiru Bauchi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya amince da sauya sunan Jami'ar Kimiyyar Lafiya ta Tarayya da ke Azare a Jihar Bauchi zuwa Jami'ar Sheikh Usman Ɗahiru Bauchi. Tinubu ya sanar da hakan ne a yau Asabar, a lokacin da ya isar da ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin a garin Bauchi. A cewar Shugaban Ƙasar, matakin ya sami ne domin karrama kyawawan ayyukan da marigayin shehin malamin ya bari na karantarwa a tsawon rayuwarsa da ya shafe kusan ƙarni guda. Lamarin da ya taimaka wa ci-gaban al'umma a Nijeriya da ma ƙasashen waje. Haka kuma, Tinubu ya bayyana…
Read More

MOPPAN ta aike da saƙon ƙarshen shekarar 2025

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Ƙasa MOPPAN, ta miƙa saƙonta na jinjina ga masana'antar Kannywood bisa hoɓɓasa da ta yi wajen fitar da muhimman ayyukan da suka ƙara ɗaukaka darajarta a fannin fasahar wasam kwaikwayo. A wata takarda da Sakataren MOPPAN ma ƙasa, Dakta Mohammed Ibrahim Gumel ya fitar, ƙungiyar ta ce furodusoshi sun yi ƙoƙari wajen ganin sun samar wa masu kallo na kowane mataki fina-finai masu ilimantarwa, nishaɗantarwa, faɗakarwa da ƙayatarwa, lamarin da ya taimaka wajen dawo da hankulan masu kallo kan ayyukan masana'antar. A saƙonta na ƙarshen shekarar 2025, ƙungiyar ta…
Read More

Tinubu ya ƙaddamar da muhimman ayyukan Gwamna Zulum a Maiduguri

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Bola Tinubu ya ƙaddamar da manyan ayyuka da Gwamna Babagana Umara Zulum na Borno ya samar a Maiduguri, Babban Birnin jihar. Shugaban ƙasar ya buɗe manyan makarantu uku, wato 'mega schools' da kuma motocin lantarki da babura masu ƙafa uku, wato adaidaita guda 620, waɗanda gwamnan ya samar. An yi taron ƙaddamarwar ne a wurare mabambanta, inda Shugaba Tinubu ya yaba wa Gwamna Zulum bisa jagoranci na gari da yake ƙoƙarin aiwatar wa al'ummar jiharsa. Tinubu ya ce: "Ina taya Gwamna da al’ummar Jihar Borno murna bisa wannan gagarumin sauyi. Gwamnati dai game…
Read More