Babaji

5691 Posts

An yi wa fiye da mutane 100 aikin ƙaba da ƙari kyauta a Kano

Sama da yara 100 ne suka rabauta da aikin ƙaba da ƙari kyauta a Karamar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano. A sanarwar da Jami'ar Yada Labaran ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, Kansilan Lafiya na yankin, Malam Bashir Shu'aibu, ya ce, sama da mutum dari ne suka amfana da aikin kaba da kari kyauta, a cigaban ayyukan inganta lafiyar al’uma, wanda Gwamnatin Jihar Kano da Karamar Hukumar Bichi ke daukar nauyi. Malam Bashir Shu’aibu ya bayyana cewa aikin yana gudana ne a asibitin Kula da Lafiya a Matakin Farko dake Mazabar Saye, inda ya yi fatan alheri…
Read More

An sake saya wa unguwannin ƙaramar hukumar Bichi bututun ruwan famfo

An yi kira ga al'umar Bichi su rika bijiro da bukatun ayyuka da suke da bukata ga Majalisar karamar hukumar, domin inganta al'amuran rayuwarsu. A wata sanarwa da Jami'ar Yada Labarai ta karamar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa Manema Labarai, Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya yi wannan kiran ne a yayin kaddamar da bututun ruwa ga wasu unguwannin karamar hukumar a ofishinsa dake sakatariyar Bichi, inda ya bayana farin cikinsa na aiwatar da wannan aiki da ya yi a karamar hukumar. "Kamar yadda kansilan harkar ruwa ya fada, wannan kusan shi ne kashi…
Read More

Kano: Ƙaramar Hukumar Bichi ta yi namijin ƙoƙari a allurar rigakafi, inji Mahmud Garba

Sama da yara 92,760 ‘yan kasa da shekaru biyar ne aka yi nasarar yi wa allurar rigakafin cutar shan-inna a Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano. Jami'in gudanar da allurar rigakafi na yankin, Malam Mahmud Garba ne ya bayyana haka, yayin tattaunawarsu da Jami'ar Yada Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo. Malam Mahmud Garba da ya gamsu da haka, ya tabbatar da taimakon Allah tare da kokarin Gwamnatin jiha da na Majalisar karamar hukumar suka samu nasarar aiwatar da aikin rigakafin. Ya ce, yara kimanin dubu daya da dari takwas da saba'in da daya 1871, aka yi nasarar…
Read More

Gwamnatin Kano ta raba wa mata fom don bunƙasa sana’o’insu

Gwamnatin Jihar Kano ta sake raba fom ga mata domin cigaba da tallafa musu wajen bunƙasa harkokinsu na kasuwanci a faɗin jihar. A sanarwar da Jami'ar Yada Labarai ta Karamar Hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa Manema Labarai, Shugaban Karamar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ne ya bayyana haka, a yayin da Kungiyar Mata masu Sana'ar Man Kuli suka kai masa ziyara a ofishinsa dake sakatariyar karamar hukumar. Shugaban Majalisar yankin, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ya bayyana jin dadinsa bisa amanar jagororin kungiyar matan masu sana'ar, bisa isar da sakon tallafin da ya yi…
Read More

Zangon ƙarshe na rayuwar Buhari ya kasance cike da jimamin rashe-rashe – Aisha Buhari

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Dakta Aisha Buhari ta bayyana shekarar ƙarshe ta rayuwar Buhari a matsayin abin da ya fuskanci yawan jana'iza da tafiye-tafiye akai-akai bayan saukarsa a karagar mulki da tsananin rashin lafiya da ya fuskanta. Aisha ta bayyana haka ne a littafin "From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari", wanda Dakta Charles Omole ya wallafa, inda ta bada ba'asin kwanakin ƙarshe na tsohon shugaban ƙasar da halin ƙunci da iyalansa suka shiga. A cewarta, rashin lafiyar Buhari ya tsananta ne a lokacin da ya kammala wa'adinsa biyu na shugabancin Nijeriya,…
Read More

‘Rayuwarmu tana cikin haɗari’: Akpabio ya roƙi Tinubu ya sake duba dokar janye wa manyan mutane ƴan sanda

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, ya yi magiya ga Shugaba Bola Tinubu da ya sake duba umarninsa na janye jami'an ƴan sanda daga gadin manyan mutane, yana mai bayyana dalilai na tsaro ga ƴaƴan Majalisar Dokoki. A ranar 23 ga watan Nuwamba Shugaba Tinubu ya umarci a gaggauta janye jami'an ƴan sandan da aka tura gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya da nufin warware matsalolin tsaro da ke cigaba da taɓarɓarewa a ƙasar. Shugaban Majalisar Dattawan ya yi roƙon ne a madadin ƴan majalisu akan umarnin da Tinubu ya bayar na janye jami'an daga…
Read More

Borno: Dakarun tsaro sun daƙile harin ƴan ta’adda a tsaunikan Mandara zuwa Bitta

Dakarun rundunar atisayen Haɗin Kai (OPHK) sun yi nasarar daƙile wani yunƙurin kutsawar ƴan ta’adda zuwa garin Bitta da ke Jihar Borno, inda suka kashe da dama daga cikinsu a yayin da suka arrangama. A wata sanarwa da Kakakin dakarun OPHK, Sani Uba ya fitar a ranar 18 ga watan Disamba, ya ce al'amarin ya faru da misalin ƙarfe 12:30 na dare a ranar a lokacin da dakarun suka gano motsin ƴan ta’addan daga tsaunin Mandara ta hanyar na’urorin sa ido na zamani. Bayan barin ƴan ta’addan su kusanto har zuwa inda ya dace, dakarun suka buɗe wuta tare da…
Read More

Shugaban INEC ya gayyaci tsagin Turaki da Anyanwu kan rikicin PDP

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ƙarƙashin jagorancin Farfesa Joash Amupitan, ta shiga tsakani akan rikicin shugabancin babbar jam’iyyar adawa, PDP, inda ta gayyaci ɓangarorin jam’iyyar biyu zuwa hedikwatarta da ke Abuja a ranar Juma’a. Zaman ya haɗa ɓangaren da Tanimu Turaki ke jagoranta da kuma na Abdulrahman Mohammed da ke samun goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike. Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa kiran ɓangarorin biyu ya zama wajibi saboda ta’azzarar rikicin cikin gida acikin jam’iyyar. Bayan gabatar da jawabi, an shiga taron sirri domin samun sasanci tsakanin ɓangarorin da ke rikici,…
Read More

Yanzu-yanzu: Tinubu ya gabatar da Kasafin tiriliyan 58.47 na 2026 ga Majalisar Dokoki

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da Kasafin kuɗin shekarar 2026 na jimillar Naira tiriliyan 58.18. An gabatar da kasafin ne zaman haɗaka na majalisun Dattawa da Wakilai tun a ranar Alhamis, 12 ga watan Disamba, 2025 wanda jagororin majalisun kamar Shugaban na dattawa Godswill Akpabio da Kakakin na wakilai, Tajudeen Abbas da kuma shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa suka halarta. Da yake gabatar da jawabi yayin gabatar da kasafin, Shugaba Tinubu ya bayyana hakan a matsayin 'lokaci na bayyana nasarar zangon gyare-gyaren Nijeriya'. Ya kuma yi tsokaci akan raɗaɗin da ƴan Nijeriya suek fuskanta…
Read More

Majalisar Dattawa ta tabbatar da Mohammed da Eyesan a matsayin jagororin NMDPRA da NUPRC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Oritsemeyiwa Eyesan a matsayin sabon shugaban Hukumar Gudanarwar Man Fetur na Nijeriya (NUPRC). Haka kuma, ta tabbatar da Sa'idu Mohammed a matsayin shugaban Hukumar Kula Lamuran Man Fetur na Ƙasa (NMDPRA). Hakan na zuwa ne bayan da kwamitin haɗaka ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdulrahman Kawu ya gabatar na rahotonsa na nazari akan mutane biyun. A ranar Laraba, Farouk Ahmed ya yi murabus a muƙamin shugaban NMDPRA yayin Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya ɗora zargin rashawa akansa. Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya sanar da cewa Gbenga…
Read More