19
Dec
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Alhamis Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci zaman gaggawa na Majalisar Zartarwa (FEC) a Fadar Shugaban Ƙasa yayin da yake gab da gabatar da Kasafin Kuɗin shekerar 2026 ga Majalisar Dokoki. Rahotanni sun bayyana cewa an gudanar da zaman ne sa'o'i kaɗan da shugaban ƙasar ya sanar da majalisa ƙudirinsa na gabatar da kasafin a yau Juma'a da misalin ƙarfe 2 na rana kamar yadda dokar ƙasa ta bada dama. Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya ce an shirya zaman ne domin bada damar gabatarwa ta ƙarshe bayan kammala aikin tantance kasafin gabanin…
