Babaji

5698 Posts

Ku yi amfani da alƙalumanku wajen gina ƙasa ba rusawa ba – Tinubu ga editoci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yau Laraba Shugaba Bola Tinubu ya kirayi editocin Nijeriya da su cigaba da tsare gaskiya da adalci yayin fitar da rahotanni, yana mai roƙon su da su riƙa amfani da ofisoshinsu wajen ƙoƙarin inganta harkar dimukraɗiyya da haɗin kan ƴan ƙasa. Da yake jawabi yayin buɗe babban taron Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE) na shekara-shekara a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, Tinubu ya ce fannin jarida sh ine ƙashin bayan ci-gaban ƙasa da ƙarfafa shugabancin dimukraɗiyya a sassan ƙasar. Taron ya haɗa jagororin jaridu, manyan ƴan jarida, masu samar tsare-tsare da malaman harkar…
Read More

Ku dawo da tiriliyan N210 da ba a san yadda aka yi da su ba – Majalisar Dattawa ga NNPC

Majalisar Dattawa ta ce wajibi ne Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya mayar da kuɗaɗen da ba a bayyana yadda aka yi da su ba, waɗanda suka kai jimillar Naira tiriliyan 210 zuwa asusun tarayya. Kwamitin Majalisar Dattawa akan ƙididdige adadin kuɗaɗen gwamnati ƙarƙashin jagorancin Sanata Aliyu Wadada ne ya yanke wannan hukunci, bayan shugaban kamfanin, Bayo Ojulari, ya gaza bayyana a zaman kwamitin domin ya fayyace amsoshin tambayoyi da aka aika masa. A binciken da aka gudanar kan ayyukan NNPCL daga shekara ta 2017 zuwa 2023, kwamitin ya gano cewa kuɗaɗe da ba a iya bayyana yadda aka…
Read More

Chadi ta nemi haɗa hannu da Nijeriya kan inganta tsaron iyakoki da tattali

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban hafsan tsaron dakarun Chadi a Maiduguri, Mista Bisso Youssouf Mbodou Mbami ya yi kira da a ƙarfafa haɗakar tsaro tsakanin Nijeriya da Chadi domin kawo ƙarshen ayyukan ta'addanci a yankin Tafkin Chadi. Mista Bisso ya yi wannan kira ne yayin da ya jagoranci wata tawagar ofishin tsaron ƙasarsu a wata ziyara a hedikwatar jami'an haɗaka (JTF) na yankin Arewa ta Gabas da na atisayen Haɗin Kai (OPHK) a Maiduguri. Ya ce, bunƙasa haɗaka tsakanin ɓangarorin ƙasashen biyu abu ne mai muhimmanci wajen cin galaba akan mayaƙan Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ta'addanci da…
Read More

Yadda aka tada jijiyar wuya tsakanin Wike da sojoji kan fili a Abuja

Wani jami’in soja a Abuja ya yi gaba da gaba da Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, inda ya hana shi shiga wani fili da aka ajiye sojoji domin tsaron sa. Al'amarin ya faru ne a lokacin da Wike ya nace akan cewa sai ya shiga filin inda ya fuskanci jami’in sojan da ya ce umurni aka ba shi da kada ya bari kowa ya shiga wannan wurin. Jami’in ya ƙara da cewa yana aiki ne da umarni, don haka babu yadda zai yi ya ba shi damar shiga filin. An jiyo Minista Wike yana bai wa jami’in umarni da…
Read More

Asibitin Best Choice zai riƙa duba wasu cututtuka kyauta don tallafa wa ƙoƙarin gwamnatin Kano

Ganin yadda Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ke ƙoƙarin haɓaka fannin lafiya, Asibitin Best Choice ya shirya duba nasu wasu nau'ukan cututtuka kyauta, inda ya yi rangwamen kaso 50 ga aikin tiyata. Asibitin ya sake bijiro da wasu ayyukan jin ƙai a yunƙurinsa na cigaba da faranta wa al’umma kamar yadda ya saba lokaci bayan zuwa lokaci duba da yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf yake jajircewa wajen tallafa wa bangaren lafiya faɗin a jihar. Rahotanni sun bayyana cewa jagororin Best Choice za su duba masu waɗannan larurar kyauta, idan kuma abin ya kama za a yi aiki, za'a biya kaso…
Read More

Gwamnatin Zamfara ta yi alwashin tallafa wa sabuwar Jami’ar Kimiyya ta Tsafe

Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi alƙawarin tallafa wa sabuwar Jami’ar Tarayya ta Kimiyyar Likitanci da Fasahar Lafiya da ke Tsafe jihar. Hakan na ƙunse a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Gwamna Dauda Lawal kan harkokin yaɗa labarai, Sulaiman Idris, ya fitar a yau Talata a Gusau. Idris ya ce, Gwamna Lawal ne ya bayyana wannan alkawari lokacin da ya karɓi shugaban jami’ar, Farfesa Ibrahim Yakasai, tare da tawagar sa a ranar Litinin. Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta ayyana dokar ta-baci a fannoni biyu — ilimi da lafiya domin nuna cikakken ƙudirinta na farfado da waɗannan ɓangarori a jihar.…
Read More

‘Yan fansho na shirin yin zanga-zanga tsirara kan rashin biyan haƙƙoƙinsu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Haɗakar ƙungiyar ƴan fansho ta tarayya a Nijeriya, ta yi barazanar yin zanga-zangar gama-gari a yanayin tsirara, wanda zai gudana a ranar 24 ga watan Nuwamba matuƙar gwamnati ta gaza biyansu bashinsu da ƙarin kuɗaɗe da alawus na tallafi da aka yi musu alƙawari. Shugaban ƙungiyar, Mukaila Ogunbote ya sanar da haka yayin taron manema labarai jiya Talata a Legas. Ya bayyana cewa, za su gangamin idan gwamnati ta ƙi biyan su fansho da ƙarin N32,000 da alawus na N25,000 na tallafi da aka amince da shi tun 2023. Ya ce, ƴan fansho da…
Read More

Kano: An sace mota a gidan gwamnati

Dafa BELLO A. BABAJI a Abuja Wani ɓarawon mota ya yi nasarar kutsawa cikin Gidan Gwamnatin jihar Kano da asubahin ranar Litinin, inda ya yi awon-gaba da wata mota ƙirar Toyota Hilux. Rahotanni sun bayyana cewa, ɓarawon ya samu shiga gidan ne ta ƙofa ta 4 inda ya fice da motar da misalin ƙarfe 5 na asubahin. Majiyoyi sun ce, kyamarorin CCTV sun nuna cewa ɓarawon ya fita da motar ne ta babbar ƙofar gidan. Haka kuma sun ce motar tana ɗaya daga cikin motocin tawagar mataimakin gwamnan jihar. Wata majiya ta shaida wa DAILY NIGERIAN cewa ana sanya ido…
Read More

An yi garkuwa da daraktocin Ma’aikatar Tsaro shida a hanyar Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An shiga firgici a yayin da ƴan bindiga suka yi awon-gaba da daraktocin Ma'aikatar Tsaro su guda shida akan hanyarsu ta zuwa Abuja daga Legas. Rahotanni sun bayyana cewa al'amarin ya faru ne a ranar Litinin, 10 ga watan Nuwamba, 2025 akan babbar hanyar Kaba zuwa Lokoja. An gano cewa matafiyan sun ɗauko hanya ne daga Legas zuwa Abuja domin yin jarrabawar ƙarin girma, inda suka yi ciɓis da ƴan bindigan. Al'amarin ya girgiza Ma'aikatar Tsaro da Ƙungiyar manyan ma'aikatan gwamnati na ƙasa (ASCSN), inda suka koka game da tsaro acikin ma'aikatan gwamnati da…
Read More

Yanzu ƴan bindiga ke jagoranci da ƙaƙaba wa al’umma haraji a Arewa, inji Dambazau

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida kuma Shugaban Sojoji (mai ritaya), Laftanal Janar Abdulrahman Bello Dambazau, ya koka game da yadda al'amarin taɓarɓarewar tsaro ke cigaba da ta'azzara a yankin arewacin Nijeriya, yana mai gargaɗin cewa ƴan bindiga da mayaƙa sun koma karɓe iko da wasu garuruwa. Da yake jawabi a babban taron harkokin jarida da tsaro da aka yi a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi a ranar Litinin, Dambazau ya ce shiyyar tana fama a matsanancin barazanar tsaro na tsawon sama da shekaru 20, inda a yanzu al'amarin ya yi ƙamari. A cewarsa, yanzu ƴan…
Read More