Babaji

5698 Posts

Kotu ta sake hana PDP yin babban taronta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sake dakatar da jam'iyyar PDP daga gudanar da babban taronta da take shirin yi a garin Ibadan na jiyar Oyo a watan nan na Nuwamba. Wannan shi ne karo na biyu da kotu ta hana gudanar da taron, wanda babbar jam'iyyar hamayyar ke shirin yi a ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamban da ake ciki. Haka kuma kotun ta hana INEC sa ido akan babban taron ko kuma amincewa da sakamakon taron wanda ake sa ran fitar da sababbin shugabannin jam'iyyar. Saidai kafin wannan hukuncin na biyu, wata kotun a Jihar Oyo…
Read More

Gwamnatin Tarayya da Amurka na tattaunawa kan barazanar Trump

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya tana ganawa da hukumomin Amurka bisa barazanar ɗaukar matakin soja akan Nijeriya da Shugaba Donald Trump na ƙasar ya yi a kwanan nan bayan zargin yi Kiristoci kisan ƙare dangi a ƙasar. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Al'umma, Mohammed Idris ya sanar da haka yayin hira da gidan Sky News, ranar Litinin. Ya bayyana cewa, hanyoyin difulomasiyya ne suka dace wajen shawo kan al'amuran da ke tsakanin Amurka da Nijeriya. Ya ce, da dama daga cikin labaran da suka haddasa matsalar zarge-zargen tauye ƴancin wani ɓangare sun faru ne sakamakon…
Read More

Likitoci na kula da halin Dharmendra, ku sanya shi a addu’a, inji matarsa Hema

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A halin yanzu daɗaɗɗen jarumi kuma tsohon ɗan siyasar ƙasar Indiya, Dharmendra yana kwance a gadon asibiti a birnin Mumbai inda likitoci ke cigaba da kula da shi Matarsa Hema Malini, wadda ita ma sananniyar jaruma ce tun tsawo shekaru 50 da suka gabata a masana'antar Bollywood, ta sanar da haka a jiya Litinin. Ta yi godiya ga ɗaukacin jama'a da suke cigaba da nuna damuwa akan halin da yake ciki inda ta yi magiyar da a sanya shi acikin addu'o'in fatan samun waraka, kamar yadda ta wallafa ta kafar X. Jarumi Dharmendra mai…
Read More

Matar Marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Shehu Shagari ta rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Iyalan tsohon Shugaban Ƙasa, Marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari sun sanar da rasuwar matarsa da ta rage, wato Hajiya Saratu Shagari bayan shafe shekaru 89 a duniya. A wata takarda da babban ɗan tsohon shugaban ƙasar kuma Sarkin Mafaran Shagari, Kyaftin Bala Shagari ya fitar, iyalan sun ce Hajiya Saratu ta rasu ne a jiya Litinin da misalin ƙarfe 3 na yamma bayan fama da wani dogon rashin lafiya. Ya ce, ta rayu cikin mutunci, haƙuri da sadaukarwa acikin iyalanta, wanda hakan ya sa za a yi kewar ta. Ya kuma ce, za…
Read More

Tinubu ya taya Shekarau murnar cika shekaru 70

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya taya tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau murnar cikarsa shekaru 70 a duniya. Tinubu, a wata takarda daga Kakakinsa Bayo Onanuga, ya jinjina wa Shekarau bisa gudumawarsa acikin al'umma musamman a fage siyasa, wanda ya faro tun daga malamin makaranta har zuwa babban sakatare a ma'aikatar ma'aikata ta jiharsa, gabanin shiga harkokin siyasa a shekarun farko na 2000s. Shugaban ƙasar ya tuno lokacin da Shekarau ya lashe zaɓen gwamna a shekarar 2003, inda ya doke gwamna mai ci na a wancan lokaci, lamarin da ya taimaka masa riƙe muƙamin…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗin hajjin 2026 zuwa miliyan N7.6

Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta sanar da rage kuɗin aikin Hajji na shekarar 2026 ga maniyyata daga sassa daban-daban na ƙasar, inda aka samu sauƙin kuɗi idan aka kwatanta da na bara. A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce maniyyata daga yankin Borno da Adamawa za su biya N7,579,020.96, maimakon N8,327,125.59 da suka biya a 2025, wanda hakan ke nuna an samu ragin kusan N748,104.63. Haka kuma, masu niyyar tafiya daga yankin Arewa za su biya N7,696,769.76, wanda ke nuna ragin N760,915.83 daga kuɗin bara da ya kai N8,457,685.59. A ɓangaren masu tafiya daga Kudancin ƙasar kuwa, farashin…
Read More

Gwamnan Katsina ya taya Soludo na Anambara murnar lashe zaɓe karo na biyu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na Jihar Katsina, ya bayyana nasarar da Farfesa Chukwuma Soludo ya samu a matsayin wata gagarumar nasara da ta samo asali daga jajircewa, hangen nesa a jagoranci, da kuma amincewar da ƴan Jihar Anambra suka gina a gare shi tsawon shekaru. A sanarwar da Babban Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Muhammad Kaula ya fitar, gwamnan ya ce sakamakon zaɓen, wanda aka kammala da tazara mai yawa, ya nuna irin gamsuwa da goyon bayan da jama’a ke da shi ga irin salon jagoranci na Gwamna Soludo da tsarin gwamnatin sa mai cike da…
Read More

Sulhu: ‘Yan bindiga sun sako mutane biyar a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sakamakon sasanci da wasu ƙananan hukumomi na Kudancin jihar, ƴan bindiga a Ƙaramar Hukumar Sabuwa sun saki mutane biyar waɗanda dukkan su ƴan asalin yankin garin Maska ne. 'Yan bindigan sun miƙa mutanen ne a garin Sabuwar da ke karamar hukumar Sabuwa inda suka miƙa su ga Magajin Garin Maska Alhaji Abdullahi Umar. Shugaban karamar hukumar Funtua Hon Abdulmutallaf Suleiman Goya wanda shine yayi ta kaiwa da komowa wajan ganin an sako mutanen ya ce mutanen da aka sako Yan asalin garin Maska a karamar hukumar Funtua. Ya bayyana cewa, duk da suna cikin koshin…
Read More

Boko Haram da ISWAP sun yi ba-takashi kan jagorancin Tafkin Chadi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yankin Tafkin Chadi na fuskantar sbaon rikici yayin da ƙungiyoyin ikirarin jihadi na Boko Haram da ISWAP suka yi artabu a tsakaninsu da nufin samun wajen zama a tsibirin ƙananan hukumomin Abadam da Kukawa da ke jihar Borno a yankin. Wani rahoto da Zagazola Makama, mai sharhi akan lamuran tsaro ya fitar a jiya Lahadi, ya ce al'amarin ya faru ne a ranakun 5 zuwa 8 ga watan Nuwamba, 2025 a yankunan Sahel na 1, Dogon Chuku, Mangari da yankunan ruwa na Tumbun Gini, Tumbun Shanu, Mangari da Dumba. Rahoton ya bayyana cewa mayaƙan…
Read More

Nijeriya da Saudiyya sun ƙulla yarjejeniyar hajjin 2026

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta ƙulla yarjejeniyar gudanar da aikin Hajji ta shekarar 2026 da ƙasar Saudiyya yayin da ake gab da fara shirye-shiryensa. An cimma haka ne a yayin wani biki a da aka gudanar a birnin Jeddah na Saudiyya. Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya sanya hannu a madadin Nijeriya, yayin da Mataimakin Ministan Hajji na Saudiyya, Abdulfatah Mashat ya wakilci ƙasa mai tsarki. NAHCON ta bayyana cewa yarjejeniyar hujja ce akan cewa Nijeriya ta shiga jerin ƙasashen da za su gudanar da aikin ibadar a 2026. Kawo yanzu…
Read More