Babaji

5698 Posts

Borno: Sojoji sun ceto mutane 86 da kama masu kai wa ƴan ta’adda kayan aiki 29

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakarun tsaro ƙarƙashin rundunar atisayen Haɗin Kai (OPHK) da na haɗaka a shiyyar Arewa ta Gabas sun yi gagarumar nasara a aikinsu na yaƙi da ta'addanci a jihar Borno. A wata takarda da jami'in yaɗa labaran OPHK, Laftanal Kanal Sani Uba ya fitar, ya ce jami'ai na musamman na Bataliya ta 135 a jiya Lahadi, sun yi artabu da mayaƙan Boko Haram/ISWAP a yankin Dutsen Kura a lokacin da suka gano cewa sun yi garkuwa da mutane a hanyar Buratai zuwa Kamuya. A yayin farmakin ne sojojin suka yi nasarar kora mayaƙan zuwa yankin…
Read More

Yanzu-yanzu: Na hannun daman Kwankwaso, Hon. Abdulmumin Kofa ya koma APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Darakta Janar na ƙungiyoyin goyon bayan Tinubu, wato 'Tinubu Support Groups' kuma ɗan Majalisar Wakilai, Hon Abdulmumin Jibrin Kofa ya fice daga Jam'iyyar NNPP inda ya koma mai mulki APC, yana mai bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Tinubu a zaɓen 2027. Komawar ɗan majalisa APC ta nuna cewa jam'iyyar mai mulki ta samu gagarumar ci-gaba musamman a harkar siyasar jiharsa ta Kano. Hon. Kofa ya sanar da haka ne a mahaifarsa ta Kofa da ke Ƙaramar Hukumar Bebeji a jihar Kano, inda ya samu tarba daga dubunnan magoya baya da jagororin addini.…
Read More

Mahaifiyar Ministan Muhalli Abbas ta rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mahaifiyar Ministan Muhalli da Albarkatun Ƙasa, Mallam Balarabe Lawal Abbas, Hajiya Ɗayyabatu Lawal Aliyu ta rasu. A yammacin jiya Lahadi ta rasu a gidanta da ke Zariya City a Jihar Kaduna. Wata majiya mai kusanci da iyalanta ta shaida wa wakilinmu cewa ta rasu ne bayan fama da wani rashin lafiya. Marigayar ta shafe shekaru 93 a duniya. Wakilin namu ya ruwaito cewa za a yi jana'izarta a yau Litinin da misalin ƙarfe 11 na safe acikin garin Zariya.
Read More

Ƙungiyar SWAN ta bada babbar lambar yabo ga wakilin Manhaja, Abdullah Tanko

Daga UMAR GARBA a Katsina Ƙungiyar marubuta labaran wassanni ta ƙasa (SWAN) ta bayar da mafi girman lambar yabo ga tsohon shugaban ƙungiyar reshen jihar Katsina kuma Wakilin Blueprint Manhaja, Kwamred Abdullah Mohammed Tanko. Sakatariyar ƙungiyar ta ƙasa ce ta shirya bikin bayar da lambobin yabon a Abuja don girmama 'yan jarida na ɓangaren wasanni waɗanda suka ba da gudummawa a lokuta daban-daban ga ci-gaban ƙungiyar. Shugaban SWAN na Jihar Katsina, Kwamared Nasir Gide, wanda ya wakilci Abdullahi Tanko a bikin, ya miƙa masa lambar yabon ne a wani biki da ya gudana a Katsina. Ya bayyana gudunmawar Kwamred Abdullahi…
Read More

Ɓata-gari suna yi wa aikin titin Abuja zuwa Kano zagon-ƙasa, inji Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙaramin Ministan Ayyuka, Bello Goronyo ya bayyana kaɗuwarsa akan ayyukan zagon-ƙasa da ake yi wa aikin babban titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano. Goronyo ya faɗi haka ne a yayin sanya ido a wani sashi na aikin a jiya Asabar, inda ya kirayi jagororin al'umma da su yi jan hankali ga waɗanda suke jagoranta akan munanan ayyukan. Ya ce, waɗanda aka bai wa kwangilar aikin suna iya bakin ƙoƙarinsu ba dare ba rana wajen ganin sun yi aiki mai kyau don haka ba daidai ba ne ace wasu na ɓatawa. Ministan ya bayyana cewa…
Read More

Gwamnatin Kaduna za ta ɗauki jami’an lafiya 9,000 aiki cikin shekara biyar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce za ta ɗauki ƙarin wasu jami'an lafiya guda 9,000 a jihar daga yanzu zuwa nan da shekara biyar masu zuwa. Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ahmed Maiyaƙi ya bayyana haka a yau Lahadi a Kaduna, yayin wani zama na kwana ɗaya da ya ƙunshi harkar labarai, wanda Hukumar Ci-gaban Insorar Lafiya ta jihar (KADCHMA) da haɗin-gwiwar ƙungiyar lafiya mai zaman kanta, wato Lafiya: UK-Nijeriya Partnership for a Healthier Future' suka jagoranta. Ya ce, a kwanan nan ne Gwamna Uba Sani na jihar ya amince da ɗaukar ma'aikatan lafiya su guda…
Read More

Hon. Mai-Palace ya ɗauki nauyin koyar da mata sana’o’i a mazaɓarsa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Gusau/Tsafe ta Jihar Zamfara, Hon. Kabiru Amadu Mai Palace, ya ɗauki nauyin koyar da mata sana’o’i, wanda gidauniyar Sidiya Charity Foundation za ta jagoranta. Yayin da suka kammala karɓar horon sana'o'in, Hon. Kabiru zai ba su jari domin fara kasuwanci domin zama masu dogaro da kansu. Kimanin mata 50 ne za su amfana da shirin koyar da sana'o'in, wanda ya dace da manufar Hon. Kabiru na tallafa wa mata da matasa, da kawo sauyi da sauƙin rayuwa ga al’ummarsa. Wannan ba shi bane karo na farko da yake…
Read More

Ali Modu Sherrif ya musanta zargin Shettima da kafa Boko Haram

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sheriff ya ƙaryata rahoton da ke cewa ya zargi Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima da kafa ƙungiyar Boko Haram. An ga yadda wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa Ali Modu Sheriff ya fito ya ce, "Ba ni ba ne, Shettima ne ya ƙirƙiri Boko Haram." Jaridar The Cable ta bayyana cewa a karon farko da aka wallafa wannan rahoto shi ne a watan Agustan shekarar 2016, kamar yadda wani bincikenta ya nuna. Ali Modu Sherrif ya bayyana wannan labari da ake…
Read More

Majalisar Ƙolin Shari’a ta nemi Tinubu ya tsige Amupitan a shugabancin INEC kan zargin iƙirarin kisan Kiristoci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A jiya Asabar Majalisar Ƙolin Shari'a a Nijeriya (SCSN) ta kirayi Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta soke naɗin da ya yi wa sabon Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan. Hakan na zuwa ne bayan da jaridar ShaharaReporters ta fitar da wani rahoto da ke bayyana yadda Farfesa Amupitan ya taɓa yin wani rubutun shari'a da ke zargin yadda ake yi wa al'ummar Kiristoci da wasu ƙabilu kisan mummuƙe sakamakon yawan kai musu hare-hare a sassan Nijeriya. A kwanan nan ne Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin jagoran INEC, wanda…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Soludo na APGA ya lashe zaɓen Anambara karo na biyu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamna Chukwuma Soludo na Jam'iyyar APGA ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Anambara a karo na biyu biyo bayan sanar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 21 na jihar da Hukumar Zaɓe (INEC) ta yi a yau Lahadi. INEC ta sanar da cewa jimillar masu zaɓe 584,054 ne suka kaɗa ƙuri'a a jihar, inda gwamnan ya samu ƙuri'u 422,664, lamarin da ya ba shi damar doke Nicholas Ukachukwu na jam'iyyar APC da ya samu guda 99,445 a matsayi na biyu. Sauran ƴan takarar sun haɗa da na ADC mai guda 8,208, sai na PDP da ya…
Read More