09
Nov
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Makiyayan Miyetti Allah ta ƙasa (MACBAN), ta yi tir da matakin ƴan majalisar Amurka na a hukunta ta bisa zargin ta da tauye ƴancin addini a Nijeriya. Hakan na zuwa ne bayan da Majalisar Wakilan Amurka ta yi kira ga ma'aikatun tsaro da asusun ƙasar ta hukunta wasu ƙungiyoyin Nijeriya ciki har da Miyetti Allah na Makiyaya da Miyetti Allah Kautal Hore. Da fari Shugaba Donald Trump na Amurka ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa akanta bisa zargin musguna wa Kiristoci. A wata hira da jaridar Daily Post, jagoran…
