Babaji

5698 Posts

Kogi: Kwamishina Kankarofi ya karrama jami’ai 42 bayan samun ƙarin girma

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kogi, CP Naziru Kankarofi ya jagoranci ƙarin matsayi na wasu jami'ai su guda 42 a jihar inda ya jaddada ƙoƙarinsu na ƙwarewa akan lamuran tsaro. A ranar Talata, rundunar ƴan sandan jihar ta yi bikin ƙarin matsayin jami'an a muƙamai daban-daban, waɗanda daga cikinsu akwai jami'in hulɗa da jama'a, SP William Aya a hedikwatar rundunar da ke Lokoja. Da yake jawabi, CP Kankarofi ya taya jami'an murna bisa samun ƙarin girman, sannan ya yi kira a gare su da su yi amfani da hakan wajen inganta ayyukansu a ko'ina…
Read More

Boma-bomai da alburusai ba su san addini ba, inji Shettima

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya ce ƙalubalen tsaro a Nijeriya na buƙatar aiki kafaɗa-da-kafaɗa, inda ya bayyana hare-haren ta'addanci a matsayin abinda ke shafar kowane addini, ƙabila ko yanki. Ya ce, yayin da aka yi amfani da makami wajen haddasa tsaiko ga zaman lafiya daga ƴan ta'adda, hakan ba ya bambancewa tsakanin mutane da manoma da sauran al'umma. Ya bayyana cewa, gwamnatin yanzu ta riski matsalolin tsaro da dama a lokacin da hau karagar mulki, lamarin da ya sa ta ɗauki matakan daƙile ayyukan ta'addanci da ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa…
Read More

Gwamnatin Kaduna ta bada damar samun ilimi da lafiya ga yankunan ƴan bindiga jihar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaƙi ya bayyana cewa a yanzu gwamnatin jihar ta ba wa ƴan bindiga damar samun ilimi, lafiya da damarmakin harkokin rayuwa a matsayin ɓangare na kawo ƙarshen ayyukan kashe-kashe da garkuwa da mutane na tsawon shekaru a jihar. Ya bayyana haka ne a lokacin taron kara wa juna sani kan aikin jarida na zaman lafiya da tawagar maruwaita na Ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa (NUJ) suka gabatar a Kaduna da haɗin-gwiwar Gidauniyar Zaman Lafiya ta ƙasa da Ma'aikatar Yaɗa Labarai ta jihar. A cewar Maiyaƙi, an…
Read More

Majalisa ta tabbatar da ƙudirin ɗaurin shekaru 14 ga lakcarori masu cin zarafin mata

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dokoki ta ɗauki mataki mai ƙarfi wajen inganta yaƙi da cin zarafin ɗalibai mata a manyan makarantu, yayin da ƴaƴanta suka amince da yin shekaru biyar mafi ƙaranci da 14 mafi yawa a kurkuku ga lakcarori da ma'aikatan da aka samu da hannu a lamarin. A ranar Laraba Majalisar Dattawa ta tabbatar da ƙudirin dokar wanda ya shallake karatu na ƙarshe a wajenta bayan kamala aiki akansa daga Majalisar Wakilai. Daga nan sai suka yi aiken sa ga Shugaba Bola Tinubu domin amincewa da sanyawa a kundin doka don fara aiki a nan…
Read More

Shekarau ya yi tsokaci kan makomar siyasarsa, Tinubu, Atiku da Trump yayin cikarsa shekaru 70

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ci alwashin cigaba da kasancewa ɗan siyasa har zuwa ƙarshen rayuwarsa, yana mai ikirarin shiga siyasa aiki ne da ya jiɓinci lamuran al'umma bisa jagorancin na gari a ƙasa. Shekarau ya bayyana haka ne a ranar Laraba, yayin tattaunawa da manema labarai a gidansa da ke unguwar Munduɓawa a jihar Kano, yayin bikin cikarsa shekaru 70 a duniya inda ya yi tsokaci akan zangon siyasarsa, ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta da goben siyasar adawa yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027 a Nijeriya. Tsohon Ministan na…
Read More

Tsohon Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Janar Abdullahi Muhammed ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon shugaban ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa na gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, Manjo Janar Abdullahi Muhammed ya rasu. An ruwaito cewa jami'in sojan mai ritaya ya rasu ne bayan shafe shekaru 86 a duniya a gidansa da ke Kaduna a safiyar ranar Laraba. Marigayin, wanda aka fi sani da Adangba, ya taɓa zama gwamnan tsohuwar jihar Benuwai-Filato a zamanin soja daga 1975 zuwa Fabarairun 1976 lokacin mulkin Janar Murtala Muhammed. Haka kuma a matsyinsa na haifaffen Ilorin a jihar Kwara, marigayin shi ne wanda ya samar da tsohuwar Ƙungiyar Tsaro ta ƙasa (NSO)…
Read More

Zargin kisan kiyashi: Gwamnatin Tarayya ta jero yaƙin haɗaka na Musulumi da Kirista a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A wani karo, Gwamnatin Tarayya ta ta yi watsi da ikirarin Gwamnatin Amurka na ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa a kanta (CPC) bisa zargin tauye ƴancin addinin wani ɓangare na al'ummar ƙasa, tana mai bayyana hakan a matsayin kuskuren fahimta game da halin tsaro a ƙasar. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Mohammed Idris, FNIPR, yayin jawabi ga manema labarai a Cibiyar Yaɗa Labarai ta ƙasa da ke Abuja, ya ce matsayar Amurka akan al'amarin abu ne da ke ƙoƙarin raina ɗimbin nasarorin da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu…
Read More

Har yanzu mu na neman Sowore ruwa a jallo, inji ƴan sanda

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kwamishinan ƴan sanda a Jihar Legas, Olohundare Jimoh, ya jaddada aniyarsu ta cigaba da ayyana ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo, yana mai alwashin cewa za su bi dukkan hanyoyin da doka ta tanada wajen ganin sun kama shi. A ranar Litinin ne kwamishinan ya sanar da ayyana Sowore a matsayin wanda suke nema bisa zargin sa da ta da zaune-tsaye acikin jama'a sakamakon jagorantar wani gangami da ya haddasa cinkoson ababen hawa a yankin Third Mainland Bridge da ke jihar. Da yake magana a wata hira da…
Read More

NIS ta musanta ƙwace wa Sanata Natasha fasfo

Hukumar Shige da Fice ta ƙasa (NIS) ta ƙaryata rahotannin da ke cewa ta ƙwace fasfon Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, inda ta ce abin da ya faru wani ɓangare ne na aikinsu na yau da kullum ba wani kamawa ko tsangwama ba. Kakakin hukumar, Akinsola Akinlabi ya bayyana cewa an duba fasfon nata ne bisa bin tsarin tsaro da ake aiwatarwa ga dukkan matafiya, musamman manyan jami’an gwamnati da ƴan majalisa. A cewarsa, “Ba a kama ko ƙwace fasfon Sanata Natasha ba. An yi bincike ne kamar yadda ake yi wa kowa, kuma an mayar mata da takardunta nan take.” Saidai…
Read More

DSS ta sallami jami’ai 115 don inganta aiki

Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), ta ce ta kori wasu jami'anta su guda 115 daga aiki, saboda abinda ta kira da 'wasu sauye-sauye da take yi'. A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Talata, DSS ta shawarci al'umma da su kauce wa mu'amala da jami'an a matsayin wakilan hukumar. Bayanan mutanen da hukumar ta fitar sun nuna cewa an kori mutanen ne tsakanin shekarar 2024 zuwa 2025. Hakan na zuwa ne bayan da a watan Oktoban da ya gabata hukumar ta kama wasu tsofaffin jami'anta biyu bisa zargin su da amfani da sunan hukumar suna…
Read More