04
Nov
Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritayal), wato tsohon Shugaban ƙasa na mulkin soja a Nijeriya, ya buƙaci shugaban Amurka Donald Trump da ya goyi bayan yaƙin da Nijeriya ke yi da ta'addanci da rashin tsaro ba wai yi mata barazana ba. Abdulsalami, wanda a yanzu yake Landon, ya yi magana a wata hira ta wayar tarho, inda ya ce ya lura cewa kalaman shugaban na Amurka ka iya kawo cikas ga haɗin kan ƴan Nijeriya. Ya kuma bukaci ƴan Nijeriya da su yi watsi da bambance-bambancen da ke tsakanin su, su haɗa kai don kare ƴancin ƙasar ta hanyar fuskantar barazana…
