04
Nov
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore ya yi watsi da barazanar Amurka ƙarƙashin jagorancin Shugaba Donald Trump akan ɗaukar matakin soja a Nijeriya, sakamakon zargin yi wa Kiristoci kisan gilla, yana mai bayyana hakan a matsayin abinda zai haddasa tashin-tashina acikin al'umma. A wani rubutu ta Soshiyal Mediya, Sowore ya ƙalubalanci masu murna da matakin, yana mai cewa hakan illa ne da ka iya shafar kowane addini ƙabila a ƙasar. Ɗan siyasar ya kuma ce samar da mafita game da matsalolin Nijeriya ba abu ne ba za a magance ta…
