Babaji

5698 Posts

Abinda ya sa hedikwatar tsaro ta ƙi ayyana yunƙurin juyin mulki – Rahoto

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sababbin bayanai sun bayyana game da dabarun gwamnati wajen salon isar wa al'umma saƙo bayan bayyanar zargin kitsa juyin mulki a Nijeriya. Wani rahoto da jaridar PRNigeria ta fitar ya bayyana cewa an samu shawarar shari'a ne jim-kaɗan bayan jami’an leƙen asiri na cikin gida da ke aiki a Hedikwatar Tsaro (DHQ) sun gano cewa hakan wani shiri ne na wasu jami'an sojoji da wasu fararen hula da suka ɗauki nauyinsu da nufin haddasa wa gwamnatin fitina. Wani ƙwararre akan harkar shari'a da ke ba gwamnati shawara akan doka da lamuran tsaro ya yi…
Read More

Tinubu zai gana da Trump bisa zargin kisan Kiristoci a Nijeriya

Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Manufofin gwamnati, Daniel Bwala ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu da Shugaban Amurka, Donald Trump, na shirin ganawa a kwanaki masu zuwa. Za a yi ganawar ne a kodai a Fadar Shugaban Ƙasa ta Aso Rock ko kuma Fadar White House ta Amurka. An shirya haɗuwar ne domin tattauna muhimman batutuwan da tasowa bayan da Trump ya saka Nijeriya a jerin kasashen da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ke lura da su saboda zargin take haƙƙin ‘yancin addini da bada umarni ga Pentagon da ta duba yiwuwar kai hari kan ƙungiyoyin ‘yan ta'adda a ƙasar.…
Read More

Zargin kisan Kiristoci: Tinubu a ankare yake da barazanar Amurka, inji Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fadar Shugaban ƙasa ta ce Shugaba Bola Tinubu yana ankare da barazanar Shugaba Donald Trump na ɗaukar matakin soja a Nijeriya bisa zargin yi wa al'ummar Kiristoci kisan kiyashi. A ƴan kwanakin nan ne Trump ya yi kalamai da dama bayan ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa akanta, inda ya yi barazanar turo sojojin ƙasarsa matuƙar gwamnatin Nijeriya ta gaza dakatar da kisan gilla akan Kiristocin ƙasar. Ya umarci sashen yaƙi da ya kasance cikin kimtsi domin yiwuwar fara atisaye a Nijeriya. Da yake jawabi, Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga, ya…
Read More

Zargin juyin mulki: Yadda aka samu Naira biliyan 11 a asusun bankin ɗaya daga cikin sojojin da aka tsare

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wani rahoto da jaridar PUNCH ta fitar ya bayyana yadda jami'an sojojin leƙen asiri suka bankaɗo kimanin Naira biliyan 11 a asusun wani kanal na soja da aka tsare bisa zargin juyin mulki da aka alaƙanta da wasu manyan sojoji a Nijeriya. A cewar jaridar, majiyoyi na manyan jami'ai sun ce gano maƙudan kuɗaɗen na da alaƙa da tsararren jami'in, lamarin da ya ƙarfafa zargi akansa, wanda a baya aka tura shi aiki a yankin Neja-Delta. Da ake bincike akansa game da kuɗaɗen, Kanal ɗin ya yi ikirarin cewa asalinsu na wani tsohon gwamna…
Read More

Gwamnan Kaduna ya gabatar da ƙudirorin raya jiharsa a taron ƙoli na biranen Asiya

Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, ya wakilci Nijeriya a taron ƙoli na biranen Nahiyar Asia da aka yi a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gabatar da ƙudirorin sauyi na ci-gaban jihar. Taron, wanda ya samu halarcin manyan baƙi daga ƙasashe sama da 150 ciki har da gwamnoni, shugabannin birane, da jagororin kasuwanci daga nahiyoyin Asiya, Fasifik da Turai, da kuma Afirka. Taron, wanda taken wannan shekarar mai taken: “Haɗin Gwiwa. Ƙarfafawa. Sauyi.”, ya kasance wani dandalin musayar ra’ayoyi da dabarun ci gaba tsakanin shugabannin birane domin samar da ci gaban birane mai ɗorewa tare da haɗin kai.…
Read More

Gwamna Uba Sani ya kashe biliyan N8.2 a gina titin Kabala zuwa Costain, inji Daraktan KADRA

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya kashe jimillar Naira biliyan 8.2 wajen biyan bashin da aka gada da kuma sake farfaɗo da aikin hanyar Kabala zuwa Costain na cikin karamar hukumar Kaduna ta Arewa wanda aka yi watsi da shi a baya. Shugaban Hukumar kula da Hanyoyi ta Jihar Kaduna (KADRA), Dakta Abdullahi Baba Ahmed ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyara domin duba halin da aikin yake ciki. Ya ce, gwamnatin da ta gabata ta bar aikin ne saboda matsalolin tsari da kuma rashin isasshen kuɗin gudanarwa, wanda a yanzu gwamnatin Uba Sani take cigaba da…
Read More

‘Yan bindiga sun halaka mutane uku da ƙone gidaje a ƙauyukan iyakar Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Al'umma a ƙauyuka da dama sun shiga firgici a Ƙananan Hukumomin Shanono da Tsayawa da ke Jihar Kano biyo bayan wani harin ƴan bindiga da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku da yin garkuwa da mutane. Al'amarin ya uku ne a daren ranar Juma'a wayewar Asabar, wanda ya jefa al'umma cikin fargaba game da ayyukan ƴan bindiga a ƙauyukan da ke iyakokin jihohin Katsina da Kano. Wani shaida ya bayyana wa manema labarai cewa kimanin ƴan bindiga guda 20 ɗauke muggan makamai ne suka shiga Ƙauyen Yanganau da ke Tsanyawa, kana daga bisani suka…
Read More

Rikicin PDP ya caɓe yayin da tsagi ya dakatar da Damagum da naɗa sabon shugaban jam’iyya

Rikicin babbar jam’iyyar adawa (PDP) ya ƙara ƙamari yayin da wani sabon ɓangare daga cikin Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ya sanar da dakatar da Shugaban jam’iyyar, Umar Damagum da wasu manyan jami’an jam’iyyar guda biyar. Wanna tsagin ya yi sanarwar ne a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ƙarƙashin jagorancin Sanata Samuel Anyanwu, wanda shi ne sakataren jam’iyyar na ƙasa. A cewar Anyanwu, an naɗa Mohammed Abdulrahman, mataimakin shugaban jam’iyya na yankin Arewa ta Tsakiya, a matsayin sabon muƙaddashin shugaban PDP. Ya ce, Damagum da wasu jami’an jam’iyyar sun yi sakacin aiki, cin hanci da saba wa hukuncin…
Read More

Likitoci na shirin tafiya yajin aikin gama-gari

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fannin lafiya a Nijeriya ya sake shiga halin rashin tabbas yayin da sama da likitoci 11,000 da ke ƙarƙashin ƙungiyar likitocin Nijeriya ta (NARD) suka shirya shiga yajin aiki a daren yau Asabar wayewar Lahadi. Rahotanni sun bayyana cewa hakan zai shafi manyan cibiyoyin lafiya aƙalla guda 91 a Nijeriya ciki har da asibitocin koyarwa, manyan asibitoci da wasu asibitocin kuɗi, lamarin da ka iya shafar kula da marasa lafiya a faɗin ƙasar. A watan hira ta wayar salula da manema labarai, Shugaban NARD, Dakta Muhammad Suleiman ya ce ƙungiyar ta yanke shawarar tsayar…
Read More

PDP ta dakatar da sakatare, mai bada shawara kan harkar shari’a da wasu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar jam'iyyar adawa, PDP, ta dakatar da Sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, wanda na hannun dama ne ga Ministan Abuja, Nyesom Wike. Haka kuma, ta dakatar da wasu shugabanninta da ake ganin suna da alaƙa da tsohon gwamnan na Jihar Ribas. Sakataren yaɗa labaranta, Debo Ologunagba ya ce jam'iyyar ta ɗauki matakin ne wanda za a yi tsawon wata guda aciki, jim-kaɗan bayan gudanar da taron gaggawa na kwamatin gudanarwa a yau Asabar. Sauran waɗanda aka dakatar sun haɗa da mai ba jam'iyyar shawarar kan harkar shari'a, wato Kamaldeen Ajibade (SAN) da sakataren…
Read More