04
Oct
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da aikin gina sabuwar hanya mai tsawon kilomita 95 a Ƙaramar Hukumar Tsafe, yana mai cewa aikin zai inganta zirga-zirgar kayayyaki da ayyuka tare da ƙarfafa ayyukan jami’an tsaro a yankin. Gwamna Lawal ya ƙaddamar da aikin ne a ranar Lahadi, inda aka fara gina hanyoyin ’Yandoton Daji, Cediya, Doka, ’Yan Waren Daji, Hayin Alhaji Bedi, Unguwar Joji da ’Yankuzo zuwa Tsafe, tare da gina gadoji guda biyar a Ƙaramar Hukumar Tsafe. An raba aikin zuwa matakai biyu, inda kamfanin SKY Construction Company ya samu kwangilar matakin farko mai tsawon kilomita 47, yayin…
