03
Oct
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa shirin ceto Zamfara da gwamnatin sa ta ƙaddamar yana kawo sauyi a fannoni daban-daban masu muhimmanci a jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da aka fara jerin bukukuwa da ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan raya ƙasa domin bikin cikar Jihar Zamfara shekaru 30 da kafuwa. An gudanar da bikin ne tare da ƙaddamar da ayyukan raya ƙasa, inda suka samu halartar tsohon Shugaban Mulkin Soja na farko na Jihar Zamfara, Kanar Jibril Bala Yakubu (mai ritaya), da tsoffin gwamnonin jihar, Ahmed Sani Yarima da Mahmud Aliyu Shinkafi, da sauran manyan…
