Babaji

5684 Posts

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Alhamis a matsayin hutun zagayowar Ranar ‘Yancin Kai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba, 2026 a matsayin ranar hutu domin karrama cikar Nijeriya shekeru 66 da samun 'yancin kai. Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida, Dakta Magdalene Ajani ta fitar a ranar Laraba, 30 ga Satumba. A cewar sanarwar, Ministan Cikin Gida, Tunji-Ojo, wanda ya ayyana haka a madadin gwamnatin tarayyar, ya taya 'yan Nijeriya da ke gida da waje murnar Ranar 'Yancin Kai ta cikar Nijeriya shekeru 66 da samu daga hannun Turawa. Ministan ya kirayi 'yan ƙasa da…
Read More

Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan Kannywood don tabbatar da nasarar Tinubu a 2027

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya buƙaci ƙwararrun ’yan mawaƙa da 'yan fim na Arewa da su mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2027, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da haɗin kan ƙasa da ci gabanta. Shettima ya bayyana hakan ne ranar Laraba, lokacin da ya karɓi tawagar Shugabanni da mambobin ƙungiyar Triple-R For Renewed Hope a ofishin yaƙin neman zaɓen APC da ke Abuja. Mataimakin shugaban ƙasar ya ce gwamnatin Tinubu tana aiwatar da manufofin da za su bunƙasa masana’antar Kannywood da suka haɗa da tallafa wa masu shirya fina-finai, mawaƙa da…
Read More

Mutum uku sun rasu yayin rige-rige a gidan gwamnatin Neja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Aƙalla mutane uku ne suka rasu yayin da wasu da dama suka jikkata a lokacin da suke rige-rige shiga gidan Gwamnatin Jihar Neja da ke Minna. Waɗanda suka jikkatan a halin yanzu suna karɓar magani a Babban Asibitin Minna. Rahotanni sun bayyana cewa al'amarin ya faru ne a daren Talata wayewar Laraba a lokacin da aka gayyaci wasu dandazon matasa zuwa gidan gwamnatin domin lallashin su akan janye batun zanga-zangar da aka alaƙanta da mutuwara masu haƙar ma'adinai 37 a jihar. Daga cikin waɗanda suka rasu akwai wata mata 'yar gudun hijira mai suna…
Read More

Zamfara: Filin jiragen saman Gusau ya tsallake tantancewar ICAO gabanin fara aiki – Rahoto

Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Gusau (GIA) da ke Jihar Zamfara ya samu nasarar kammala dukkan gwaje-gwaje da binciken tabbatar da inganci da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasa-da-ƙasa (ICAO) ta gudanar, kwanaki kaɗan gabanin fara zirga-zirgar jiragen kasuwanci a watan gobe. Wannan ci-gaba ya zo ne yayin da ake kammala shirye-shiryen fara jigilar fasinjoji ta kasuwanci a filin jirgin, inda ake shirin samun jiragen da za su yi zirga-zirga sau biyu a mako daga Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja zuwa Gusau, a ranakun Litinin da Juma’a.…
Read More

Ɗan Ministan Abuja ya miƙa fasfonsa ga kotu kan zargin damfarar filin Dala 2.1m

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba Jordan Wike, wanda ɗan Ministan Abuja, Nyesom Wike ne ya gabatar wa Babbar Kotun Abuja fasfo ɗinsa na Amurka yayin da yake cigaba da kariyarsa a shari'ar da ta ƙunshi zargin damfarar Dala miliyan 2.1 na samar da wani fili a Abuja. Manhaja ta ruwaito cewa, a ranar Litinin ne Alƙali Sylvanus Oriji na kotun ya umarci Jordan da ya gabatar da fasfo ɗinsa na Amurka bayan wani rikici kan inda yake a ranar 25 ga Oktoba, 2025, ranar da masu iƙirarin suka yi zargin ɗan ministan ya karɓi miliyan $2.1…
Read More

Yanzu-yanzu: Kotu ta tasa ƙeyar Adeyemin hukumar bogi zuwa kurkuku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci a tura Darakta-Janar na Hukumar da aka ayyana a matsayin "ta bogi", wato Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC), Frins Adeniyi Matthew mai shekaru 38 zuwa kurkukun Kuje da ke birnin tarayyar. Mai Shari'a Mohammed Umar yayin hukuncinsa a ranar Laraba, ya umarci a ajiye Adeniyi a gidan yarin har zuwa lokacin da za a gabatar musu da buƙatar bayar da belinsa. Umarnin alƙalin ya biyo bayan da Adeniyi ya musanta baki ɗaya tuhume-tuhume guda takwas da ake masa na makirci da amfani da bayanan bogi…
Read More

‘Na more ƙwarai kuma na kimtsa tsaf’, inji Tinubu bayan dawowa daga hutun Turai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya ce ya ji daɗin hutunsa na makonni huɗu da ya yi a nahiyar Turai kuma ya dawo Nijeriya cikin "ƙoshin lafiya da shiryawa tsaf domin cigaba da gudanar da harkokin mulki". Tinubu ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata yayin da ya dawo Legas daga Paris ta ƙasar Faransa, ind ya shafe ɓangare na ƙarshe na hutun nasa a Turai. Shugaban ya kuma bayar da amsa game tambayoyi akan damuwa da wasu 'yan Nijeriya suka nuna ciki har da masu masa fatan alheri musamman kan halin lafiyarsa. "Na shirya…
Read More

‘Yan bindiga sun buƙaci fansar miliyan N2 ga kowanne bayan sace manoma 47 a Neja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja 'Yan bindiga a Jihar Neja, sun sace manoma a wasu hare-hare da suka ƙaddamar a Ƙaramar Hukumar Mariga, inda shugaban ƙaramar hukumar ya ce jimillar mutanen da aka yi awon-gaba da su sun kai 47. Ya kuma ya ce masu garkuwar sun buƙaci ba su Naira miliyan biyu ga kowane ɗaya daga cikinsu a matsayin kuɗin fansa. Rahotanni sun bayyana cewa, al'amarin ya auku ne a lokacin da mutanen suke tsaka da aikin nome gyaɗa a gonakinsu da ke Tungan Rimi a Gundumar Ma'undu-Beri ta ƙaramar hukumar. An ruwaito cewa, a ranar Asabar ne…
Read More

Gombe: Mailantarki ya ƙi amince wa sakamako bayan Pantami ya sake lashe zaɓen fidda gwanin PDP

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya sake zama ɗan takarar gwamnan jihar Gombe a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP a zaɓen 2027 bayan da ya lashe sabon zaɓen fidda gwanin da jam'iyyar ta gudanar a gundumomi 114 na faɗin ƙananan hukumomin jihar. An gudanar da zaɓen fidda gwanin ne a ranar Talata a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar, bayan hukuncin Babbar Kotun Gombe na ranar Alhamis da ya soke fitar da Pantami a matsayin ɗan takara a karon farko da PDP ta yi da kuma umartar ta sake gudanar da sabon zaɓe. Kotun ta…
Read More

Tinubu ya dawo Nijeriya bayan shafe makonni huɗu a Turai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya dawo gida Nijeriya bayan tsawaita zamansa a nahiyar Turai. Manhaja ta ruwaito cewa, Shugaban ya isa birnin Legas ne daga Paris ta jirgin ƙasa a ƙarƙashin ikon Sojojin Sama na Nijeriya, wanda ya sauka a filin jiragen sama na Murtala Muhammed da misalin ƙarfe 6:32 na yammacin ranar Talata. An ga yadda aka hana 'yan jarida ɗaukar hoto ko bidiyon isowar Shugaban Nijeriyar, yayin da aka taƙaice adadin 'yan jarida a lokacin da jirgin yake ƙoƙarin ƙarasawa zuwa wajen ajiyarsa. A ranar 30 ga Agusta ne Shugaba Tinubu ya bar…
Read More