Babaji

5684 Posts

Sanata Barau ya sallami tsohuwar jarumar Kannywood, Rashida Maisa’a kan zargin yi wa APC zagon-ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya sallami Rashida Adamu, wadda aka fi sani da Rashida Mai Sa'a daga muƙaminta na mai taimakawa ta musamman a ofishinsa. Hakan na ƙunshe ne a wata takarda da mai taimaka wa sanatan akan hulɗa da jama'a, Shitu Madaki Ƙunchi ya fitar a ranar Litinin, 28 ga Satumba. A kwanan baya ne dai Sanata Barau ya sallami ɗaya daga cikin masu mataimaka masa, Umar Alhassan, wanda aka fi sani da King Indara bayan wata wallafa da ya yi a Soshiyal Mediya da ke sukar Gwamna Abba…
Read More

SSS ta janye shirin dakatar da cigaba da shari’ar Sowore ta ɓatanci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Lauyan da ya gabatar da tuhuma kan Ɗan gwagwarmaya kuma mawallafin ShaharaReporters ta bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin "babban ɓarawo", ya musanta samun bayanin wani shirin Hukumar Tsaro ta Farin (SSS) na dakatar da shari'ar har sai bayan zaɓen 2027. Lauyan, Akinlolu Kehinde (SAN), ya musanta haka ne a ranar Litinin bayan lauya mai kare Sowore, Adeyinka Olumide Fusika (SAN) ya ankarar da Mai Shari'a Muhammad Umar kan wasu rahotanni masu cewa SSS na shirin neman a ɗage sauraron shari’ar na dogon zango domin bai wa Sowore cikakkiyar damar shiga babban zaɓen na…
Read More

Kotu ta ayyana dakatar da babban lauya, Gadzama a matsayin saɓa doka

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta ayyana matakin LPDC na dakatarwar shiga aikin shari'ar na tsawon shekara uku akan Mista Gadzama, a cewar wata sanarwa da aka aike wa jaridar PREMIUM TIMES a ranar Litinin. Sanarwar da lauyoyin Gadzama suka fitar ta ce kotun da ayyana aiwatarwa ko tilasta hukuncin akan babban lauyan a matsayin abin da ya saɓa wa dokokin Sashe na 36(1), 36(2) da 6(6)(b) na Kundin Dokokin Nijeriya. Sannan, sanarwar ta ce kotun ta ayyana cewa LPDC ba shi da hurumi akan al'amarin, don haka Mai Shari'a Obiora Egwatu ya haramta…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu na hanyar dawowa daga Paris – Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya kammala hutunsa na shekara yayin da ya bar Paris, ƙasar Faransa inda ya ƙudiri aniyar dawo wa gida Nijeriya. Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ne ya sanar da haka a wata sanarwa a ranar Talata. Ya bayyana cewa, ana tsammanin jirgin Shugaban ƙasar ya iso filin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke jihar Legas a wannan yammacin. Ya ce, Shugaban ya zaɓi ya fara sauka a Legas karrama tunawa da Cif MKO Abiola, wanda ya rasu yayin fafutukar dimukraɗiyyar Nijeriya. Ya ƙara da cewa a zaman nasa na Legas,…
Read More

Atiku da ADC na shirin gyara ƙarar ƙalubalantar shigar Tinubu zaɓen 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ɗage sauraron ƙorafin da ke neman a yi kwaskwarima ga ƙarar da su tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar da jam'iyyar ADC suka shigar akan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, jam'iyyar APC da Hukumar Zaɓe Ƙasa (INEC). A zamanta na ranar Litinin ƙarƙashin Mai Sha'ir Inyang Ekwo, kotun ta ce ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 13 ga Oktoba, 2026. An gabatar da ƙorafin mai lamba FHC/ABJ/CS/1888/2026 ne ga Mai Shari'a Ekwo. A yayin jawabinsa, lauyan da ke kare ɓangaren masu ƙara, Joseph Silas ya shaida wa kotun cewa…
Read More

INEC ta sanar da fara bada katin zaɓen 2027

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta sanar da ranar 9 ga Oktoba, 2026 a matsayin kwanan watan fara bayarwa da karɓar katin zaɓe (PVC) yayin cigaba da tunkarar babban zaɓen 2027. Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ne ya sanar da haka a ranar Litinin a Kaduna yayin ganawa da jami'an hukumar na shiyyar Arewa maso Yamma da jaddada shirinta na gudanar da zaɓen na 2027. Amupitan ya ce, aikin karɓar katin shi ne mataki na uku daga cikin matakan rajistar masu zaɓe, wanda ya samar da sababbin masu rajista guda 10,772,421, waɗanda suke dakon…
Read More

UNGA 81: Shettima ya dawo Nijeriya bayan jagorantar tawagar Nijeriya a New York

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo gida Nijeriya bayan wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jagorantar tawagar ƙasar a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) karo na 81 a Amurka. A ranar 20 ga Satumba ne Shettima ya bar Nijeriya bisa umarnin Shugaba Tinubu domin wakiltar Nijeriya a taron wanda ya haɗa jagororin ƙasashe da kuma gabatar da matsayar Nijeriya akan muhimman batutuwan da suka shafi ƙasar, shiyya da kuma muhimmancinsu a matakin duniya. An gudanar da taron ne na wannan shekara mai taken, "Restoring trust, managing transformation: A United…
Read More

An yanke wa fitaccen mai garkuwa, Ɗan Iyali hukuncin kisa a Sakkwato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta yi sanadin yanke wa sanannen jagoran 'yan bindiga Ibrahim Usman da aka sani da Ɗan Iyali, hukuncin kisa bisa samun sa da hannu a ayyukan garkuwa da halaka wasu mutum uku a Jihar Sakkwato a watan Satumban 2023. Rahotanni sun ce, Usman ya fuskanci tuhume-tuhume guda uku ne a Babbar Kotun Adalci ta Jihar Sakkwato da ke sashen shari'a na Sakkwato, tare da wasu da ake nema ruwa-a-jallo. Ababe da aka tuhumce shi da su sun haɗa da makircin aikata miyagun laifuka, garkuwa, kisa da kuma haddasa…
Read More

Daga wajen ma Tinubu yana aiki cikin ƙoshin lafiya – Fadar Shugaban Ƙasa ga Obi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da yadda ake nuna damuwa kan inda Shugaba Bola Tinubu yake da rashin halartarsa a taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81 a New York, tana mai cewa Shugaban yana nan "cikin ƙoshin lafiya" kuma yana bakin aiki. Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya wallafa a Facebook a yammacin ranar Lahadi, inda yake bayar da amsa akan tambayoyin da tsohon gwamnan Jihar Anambara kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi da wasu suke yi kan daɗewar shugaban a…
Read More

NDLEA ta kama ango ɗauke da ƙullin hodar ibilis 72 a filin jirgi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi NDLEA, ta ce ta kama wani sabon ango ɗan shekara 25 kuma ɗan kasuwa a Filin jiragen sama na Akanu Ibiam da ke Enugu bisa zargin sa da yunƙurin safarar ƙulli 72 na hodar ibilis zuwa ƙasar Portugal. An kama wanda ake zagin ne a babban ɗakin tantance matafiya a ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026, yayin da yake ƙoƙarin neman gurbi a jirgin Ethiopian Airlines zuwa Portugal ta birnin Addis Ababa. A cewar NDLEA a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, wanda ake zargin…
Read More