Babaji

5684 Posts

An ceto mutane biyu bayan wata mota ta kutsa cikin ma’ajiyar tukwanan gas a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A safiyar ranar Lahadi wata mota ta afka cikin ma'ajiyar tukwanan iskar gas a yankin Arab Road da ke Kubwa a babban birnin tarayya Abuja, lamarin da ya haifar da tarwatsewar wasu daga cikinsu da jefa jama'ar wajen cikin firgici. Al'amarin ya auku ne da misalin ƙarfe 6:15 na safe, wanda shaidu suka ce an ji ƙarar fashewar tukwanan daga nisan kilomita masu yawa daga wajen da abin ya faru. Mazauna yankin Rukunin Gidajen Ɗantata a Kubwa, wato nisan kilomita biyu daga gurin, sun bayyana cewa hatta gine-ginensu sai da suka amsa bayan fashewar…
Read More

Gwamnatin Kano ta dakatar da hawan dawakai kan matsalolin tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta dakatar da baki ɗaya harkokin da suka shafi hawan dawakai acikin ƙwaryar birnin Kano, tana mai cewa ta yi hakan saboda waɗansu dalilai na tsaro da kuma buƙatar kariya ga yiwuwar fito-na-fito tsakanin jama'a. An sanar da wannan takunkumi ne a ranar Lahadi bayan wani zaman gaggawa da majalisar tsaron jihar (SSC) ta gudanar a gidan Gwamnatin Kano, inda aka yi nazari akan halin tsaron a game da harkokin da aka shirya. A cewar sanarwar da Kakakin gwamnatin jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, matakin majalisar na…
Read More

An sake ɗage dawowar Tinubu Nijeriya zuwa Talata

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya ɗage dawowarsa zuwa Nijeriya bayan wani sauyi da aka samu acikin jaddawalin tsare-tsaren tafiyarsa. Da fari dai an yi tsammanin shugaban ya dawo Nijeriya a yau Lahadi, amma a yanzu a samu sauyi inda ake sa ran ya dawo a Talata. Saidai ba a bayyana dalilinsa ba na ɗaukar wannan mataki har zuwa safiyar Lahadi. Majiyoyi daga fadar Shugaban Ƙasa sun shaida wa manema labarai cewa shugaban da zai dawo Nijeriya ne a yau Lahadi, kamar yadda aka tsara bayan shafe makonni yana hutu a Nahiyar Turai. A yanzu dai…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta kwaso ‘yan Nijeriya 105 daga Afirka ta Kudu yayin sabbin hare-haren ƙyamar baƙi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ce ta sake ɗebo wasu 'yan Nijeriya guda 105 daga ƙasar Afirka ta Kudu bayan aukuwar wasu sababbin hare-haren ƙyamar baƙi akan 'yan Nijeriya da 'yan wasu ƙasashen Afirka. Wannan tattara ta sa jimillar waɗanda Nijeriya ta kwaso daga ƙasar ta kai 1,821 tun bayan fara aikin a watan Yuni. Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen da aka dawo da su gida Nijeriya sun haɗa da manya 82 da yara 23, waɗanda suka sauka a filin jiragen sama na Legas ta jirgin South African Airways Flight SA060 da misalin ƙarfe 8:30 na…
Read More

Ɓarkewar kwalara ta yi ajalin fursunoni a kurkukun Kano

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu fursunoni guda biyu sun rasu bayan ɓarkewar cutar kwalara a gidan gyaran hali na Kurmawa da ke Jihar Kano. Hukumar kula da Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa (NCoS) ce ta tabbatar da ɓarkewar cutar a wata takarda da ta fitar a ranar Asabar, inda ta ce tuni aka ɗauki matakin kula da halin kuma a yanzu babu wani rahoton mutuwa bayan na mutane biyu. A cewar sanarwar da Kakakin hukumar, CSC JN Osuji ya fitar, wani binciken lafiya da aka gudanar a ranar 23 ga Satumba ne ya tabbatar da ɓarkewar cutar. Ya…
Read More

NLC ta ayyana shiga yajin aiki bayan zargin Kwamishinan Delta da umarnin lakaɗa wa mataimakin darakta duka har lahira

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja An samu wasu bayanai masu alaƙa da mutuwar Mista Unity Ekpevbughe Adeda, Mataimakin Darakta a Ma'aikatar Ilimin Sakandare ta Jihar Delta, wanda aka yi zargin ya rasu bayan lakaɗa masa duka bisa umarnin Kwamishinan, Dakta Kingsley Ashibogwu. Bayan haka ne Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), reshen Jihar Delta ta ayyana tsunduma a yajin aiki. Shugaban NLC a jihar, Goodluck Oforbruku ne ya sanar da haka a ranar Juma'a yayin jawabi ga ma'aikata masu zanga-zanga a Sakatariyar Chike Edozien da ke Asaba. Oforbruku ya ce matakin nasu amsa ne ga abin da ya bayyana a…
Read More

An halaka masu haƙo ma’adinai biyar da raunata wasu a sabon harin Filato

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kimanin mutane biyar ne aka halaka da raunata wasu a lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai farmaki a wani wajen aikin haƙar ma'adinai da ke ƙauyen Marit a Ƙaramar Hukumar Barikin Ladi ta Jihar Sakkwato a ranar Asabar. Al'amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1 na rana yayin da jama'a ke gudanar da harkokinsu, wanda ya haddasa firgici kan halin tsaron mazauna da masu aikin haƙar ma'adinai a sassan jihar, wadda take fama da matsalolin hare-hare da kashe-kashe a wasu ƙananan hukumominta. Wannan na zuwa ne ƙasa da kwana biyar da wasu…
Read More

EFCC ta kama dakatacciyar shugabar matan tafiyar City Boy Movement kan zargin badaƙala

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati EFCC, ta ce ta kama Halimat Adenike Tejuosho, wato kodinetar Kudu maso Yamma ta tafiyar City Boy Movement bisa zargin ta da hannu a wani al'amari da ya shafi mallakar wasu kuɗaɗe ta hanyar bayar da bayanan ƙarya. Rahotanni sun bayyana cewa, kamen na zuwa ne watanni bayan hukumar ta ayyana Tejuosho a matsayin wadda ake nema ruwa-a-jallo kan zargin ta da hannu a wani bincike da ya shafi zargin badaƙalar kuɗaɗe. A watan Afrilu ne EFCC ta ayyana matar mai shekaru 41 a sahun waɗanda…
Read More

Gwamnatin Sakkwato ta ware biliyan 1.59 don siyan Hilux 30 bayan amince wa dokar yaƙi da ‘yan bindiga

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ƙoƙarinta na tallafa wa ayyukan hukumomin tsaro wajen yaƙi da ayyukan 'yan bindiga da wasu miyagun laifuka, Gwamnatin Jihar Sakkwato ta amince da ƙudirin neman kafa Dokar Haramta Ayyukan 'Yan bindiga a Jihar Sakkwato ta 2026. Haka kuma, gwamnatin jihar ta bayar da kwangilolin siyo ƙarin wasu motoci guda 30 ƙirar Toyota Hilux akan jimillar kuɗi Naira 1,592,250,000. An ɗauki wannan mataki ne a zaman majalisar zartarwar jihar karo na 8 da ta saba, wanda Gwamna Ahmed Aliyu ya jagoranta, a cewar wata sanarwa da Daraktan yaɗa labaran gwamnan, Abubakar Bawa ya fitar…
Read More