Babaji

5684 Posts

Marasa lafiya biyu sun rasu a Babban Asibitin Ƙasa bayan karɓar allurar Ceftazidime

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Asibitin Ƙasa a Abuja, ya tabbatar da mutuwar wasu marasa lafiya guda biyu bayan shiga halin tsanani sakamakon zargin tasirin wata allura ta Fortcef, daga dangin sinadarin Ceftazidime. Asibitin ya sanar da haka ne a wata takarda da ya fitar mai ɗauke da 10 ga Satumba, 2026 daga Daraktan Harkokin Lafiya kuma Shugaban Kwamitin Shawarwarin Lafiya, Dakta O. Lawal. Wannan al'amari ya sanya asibitin ya ƙarfafa matakan sanya ido kan magungunan Ceftazidime da ake shigowa da su daga wajen asibitin musamman allurar Forcef mai nauyin gram 1. A cewar sanarwar, kwamitinta tantance magani…
Read More

UNGA 2026: Jamruman Hollywood da wasu sun yi zanga-zangar adawa da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jaruman Masana'antar Hollywood ta ƙasar Amurka, Susan Sarandon da Hannah Einbinder suna cikin masu zanga-zangar da 'yan sanda suka tsare a ranar Alhamis, yayin nuna adawarsu ga Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu gabanin jawabinsa a taron Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD). Ƙungiyar Jewish Voice for Peace ce ta shirya gangamin, inda aka samu halartar ɗaruruwan mutane a wajen hedikwatar MƊD. An ga yadda jama'a suka riƙa nuna adawarsu da zuwan Netanyahu taron da kuma nuna rashin goyon bayansu ga ayyukan sojojin Isra'ila a Gaza. Haka kuma, an hangi Sarandon, wadda ta taɓa lashe kyautar Oscar kan…
Read More

2027: Shugaban matasan ADC ya yi murabus sa’o’i bayan Atiku ya fitar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban matasan jam'iyyar ADC, Sultan Bello, ya yi murabus daga jam'iyyar. Bello ya sanar da wannan mataki ne a wata takarda mai ɗauke da 24 ga Satumba, 2026, wadda ya aike wa Shugaban jam'iyyar na Gundumar Gyaɗi-Gyaɗi da ke Ƙaramar Hukumar Tarauni, inda ya ce ya ɗauki matakin ne bayan shawarwari da dogon nazari da kuma raɗin kai. Ya kuma ce, wannan mataki ya fara aiki ne a nan take yayin da yake shirin sauya akalar siyasarsa, yana mai godiya ga jam'iyyar bisa damar da ta ba shi na yi mata hidima sakamakon amincewa…
Read More

Gurbin AFCON: Super Eagles ta doke Madagascar bayan farfaɗowa a wasan farko

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta fara wasanninta na neman gurbi a gasar Kofin ƙasashen nahiyar Afirka (AFCON) na 2027 da ƙafar dama bayan doke Madagascar da ci 2 da 1 a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo a Jihar Akwa-Ibom. Super Eagles tana cikin rukunin L ne, wanda ƙasa ɗaya ce take da damar shiga gasar saboda bai wa Tanzaniya gurbi kai-tsaye a matsayinta na mai masaukin baƙi. A wasan na daren Asabar, Madagascar ce ta fara zura ƙwallo a minti 16 a lokacin ɗan wasa Charly Couturier ya samu damar…
Read More

Ko ka na APC ko ba ka ciki kwata-kwata – Gwamna Dauda ga Wike kan tafiyar Rainbow Coalition

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙalubalanci Ministan Abuja Nyesom Wike da ya bayyana ainihin alƙiblarsa ta siyasa kan shigarsa cikin tafiyar Rainbow Coalition gabanin zaɓen 2027. Wike, wanda ɗan jam'iyyar PDP ne, ya kasance yana danganta kansa da Rainbow Coalition, tafiyar siyasar da ke ƙoƙarin tara wa Shugaba Bola Tinubu mutane domin sake zaɓar sa a 2027. Saidai wannana ci-gaba ya janyo adawa daga ɓangaren gwamnonin APC, waɗanda suka ce suna da manufar goya wa Tinubu da sauran 'yan takarar APC baya yayin zaɓen a yayin da Wiken ya taƙaitu akan mara Shugaba…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: PDP ta tantance Pantami da wasu biyu yayin da ta shirya sabon zaɓen fidda gwani a Gombe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Jam'iyyar PDP a Jihar Gombe, ta sanar da tantance Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, Khamisu Ahmed Mailantarki da Usman Aliyu Garry domin shiga sabon zaɓen fidda gwanin ɗan takarar gwamnan jihar da ta sake shiryawa. A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa labaran jam'iyyar, Abdulƙadir Ahmed Dukku ya fitar a ranar Juma'a, ya ce an tantance 'yan takara ukun ne domin gwabzawa a zaɓen fidda gwanin da aka sake shiryawa a karo na biyu. Ya ce, hakan ya biyo bayan hukuncin wata kotu ne na soke takarar Pantami a jiya Alhamis. Akan hakane jam'iyyar ta…
Read More

Ƙungiyar NAWOJ ta taya Kwamishinan labaran Kano, Abdullahi Waiya murnar kammala digiri na uku

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sakatariyar Ƙungiyar 'Yan Jarida Mata ta Ƙasa (NAWOJ), na taya Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, Kwamishinan Yaɗa Labara da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, murnar kammala digirinsa na digirgir (PhD). NAWOJ a wata takarda da ta fitar ta hannun Shugabanta Aishatu Ibrahim da Sakatariyarta Wasilah Ibrahim, ta ce wannan ba iya nasarar ilimi ba ce, saidai shaida ce ta ƙoƙarinsa wajen neman ilimi, jajircewa, horo da cigaba da gina kai daga ɓangarensa. A cewarta, akwai buƙatar a yaba wa nasarorinsa musamman ganin yadda yake hidimta wa al'umma ta ilimi da jagorancinsa, tana mai cewa…
Read More

Nijeriya da Amurka sun ƙulla yarjejeniyar bunƙasa haƙo ma’adinai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya da ƙasar Amurka sun rattaɓa hannu akan yarjejeniyar ƙarfafa matakin zuba jarin Amurka a fannin haƙar ma'adinan Nijeriya da tafiyar da ci-gaban albarkatun ƙasa a Nijeriya. Ministan Ci-gaban Albarkatun Ƙasa, Dele Alake ne ya sanya hannu a yarjejeniyar a madadin gwamnatin tarayya yayin da Mataimakin Sakataren Gwamnatin Amurka, Christopher Landau ya wakilci Amurka a ɗaya gefen, a Nigeria House da ke New York a wani ɓangare na babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81. Alake ne ya sanar da wannan ci-gaba ne ta kafar X a ranar Alhamis, inda ya ce tsarin…
Read More

Taron UNGA 81: Shettima ya nema wa shirin Sabuwar Nijeriya goyon bayan ‘yan ƙasa mazauna waje

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya kirayi 'yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje musamman masu zama a Amurka da su bai wa Shirin Ajandar Sabunta Fata ta gwamnatin Shugaba Bola Tinubu goyon baya wajen bunƙasa nasarorin tattalin arziƙin ƙasar. Shettima ya yi wannan magiya ne a wata ganawa da su yayin wani taro da Shugaban NIDCOM, Hon. Abide Dabiri Erewa ya shirya, wanda aka gudanar a Nigeria House da ke Birnin New York. Mataimakin Shugaban ƙasar ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu tana iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta daidaita lamuran tattali musamman kan fannonin ilimi,…
Read More

2027: Atiku ya naɗa El-Rufa’i cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC duk da yana tsare

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ya sanya tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai acikin tawagar kwamitin yaƙin neman zaɓensa na shugaban ƙasa a 2027. Rahotanni sun bayyana cewa, ɗan takara shugaban ƙasar a jam'iyyar ADC, ya sanar da naɗin El-Rufa'i ne a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis. Wannan naɗi ɓangare ne na bayyana tsarin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar. A halin yanzu dai El-Rufa'i yana tsare a hannun Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), inda yake fuskantar tuhume-tuhume masu alaƙa da rashawa. Yana fuskantar tuhume-tuhume ne da…
Read More